Chapter 34
Chapter 34
sosai taji dadi a ranta,sai lokacin ta tuna bata gaishe da Aunty Maryam ba,cikin kissa tashiga gaisheta, Aunty Maryam itama ta amsa cike da kulawar don batasan itace Akeelan ba itadai taji ana cewa jikar Guggo Laure ce. A kwana atashi babu wuya yau biki yarage saura sati guda kuma ayau Sauban zai diro don taufeeq yatafi daukosa tare da wasu abokansa su hudu,don kayan kwana biyu kenan da isowar su yana hannun wata kawar Ammi an aje a gidan.Itama Aunty labeeba anjima zasu kariso,gida fa yacika yayi tam,a gefe daya kuma Guggo Laure ranta a jagule yake saboda rashin ganin ba'a kawo lefe ba don kuka Akeela ta tasata tafara mata,aiko ana cikin hakane baba sani yayi sallama yashigo farlon. Gaida Guggo yayi cikin kulawa face dinsa dauke da raha yafara magana"Guggo dama maganar kayan lefen Akeela ne ankawo sunzo bayan la'asar don yanzu suka taf......ai be karasa magana ba Guggo Laure tamike tare da sakin wani guda. "Ayyyiirirrrriiiii!Allah nagode ma,sani ina suke masu kawo kayan?. "Sun tafi tun dazu Guggo. Shigowa Alhaji mansir yayi, ya gaida Guggo,nanfa ta amsa baki a yage tsananin murna. "Sani to ina kayan suke yanzu? Baba sani yace"Suna farlona. Hade rai tayi tace"a sashen ka Wai kake nufi? Sake tsuke fuska tayi tare da dubansa tace"A'ah magana ta Allah niban yarda ba akan wane dalili za'a ajiye kaya a sashenka ga sashin uban 'ya?gaskiya ayi maza-maza adawo dashi sashin mansir,daga baba sani har baba mansir,mujaheed sakin baki sukayi suna duban Guggo laure,cikin bacin rai Baba mansir yadago zaiyi magana,katsesa Baba Sanj yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yadubi mujaheed wanda ranshi yakai kololuwar baci yace"Mujaheed maza kaje parlo na ga key din ka kwaso kayan lefen kanwar ka kakawo dakin Guggo,cikin ladabi Mujaheed yasa hannu ya amsa key din tare da juyawa yatafi,da harara Guggo laure tabishi tana Jan tsaki kasa². Baijima ba yafara zhigowa da akwatunan,aifa nan Guggo laure tashiga guda daga Mom din Akeela har hajiya zainab murna sukeyi baki har kunne,kafin kace me gida yafara cika da makota zuwa ganin kayan lefe,sosai kayan sukayi kyau Masha Allah don Sauban yakashe kudi musamman hand bag da shoes nd Dubai gowns,kaya dai sunyi kyau sai dai makiyi akwatuna takwas yayi. Nanfa kafin kace me kawayen Akeela sunfara watsawa a duniya. Washegari ya Sauban yaturo mata da message kan yananan shigowa,murna Akeela tayi saboda aganinta yafara son tane da kula da ita a fili ta furta"Lallai bokan Guggo yasan aikin shi, hehehehe ya Sauban kenan ai kashigo hannu na kagama,takare maganar tana mikewa tare da fadawa toilet,sabulan ta na dilka dana bleaching da ake hada mata tafara muttsike jikinta dshi before tashiga wanka. Aiko washegari su Suby da Zuleey suka zo gidan inda suka je wani restaurant suka siyo musu snack's lafiyayyu,tare da shiryawa ala dole zakace su ne suka hada. Sai wajen 5:30 su ya Sauban suka iso dashi da Taufeeq da Kareem duk cikan su sunyi kyau musamman Sauban da Taufeeq duk da cewa manyan kaya suka sanya,shadda ya Sauban yasanya me ruwan kanwa inda aka mata dinki half jamfa sai hannun ma gajere hulan kanshi ya murzata brown sai cover shoe da ya Sanya brown,agogon hannun shi kirar Gucci me ruwan kanwa,inda farin fatan shi yafito yayi masifan kyau,face dinshi sanye da shade fuskar nan babu annuri ko kadan,shima ya Taufeeq shaddar ya sanya dark blue shima half jamfa amma shi besa hula ba takalmin shi da agogon sa bakake shima yayi kyau duk da daka gansu shida Sauban zaka san jini daya ne, malam Kareem kuwa kananun kaya yasanya jeans da t shirt sai dai yayi kyau don duk cikansu badai iya wanka ba,gabadaya sun rude da ganin zaratan mazan,sosai Zuleey da Suby suka hadiye miyau don gabadaya sunyi mutuwan tsaye da ganinsu musamman Sauban. "Hello sannun ku da zuwa,please have a sit, zuleey tayi karfin fada tana nunawa Sauban inda zai zauna,cike da karairaya ita da Suby suka samu 2 seater suka zauna,inda su Sauban ke zaune a 3 seater,cikin kissa Suby tasa wayar s kunne tare da fara magana"hello kawata wai mekikeyi ne?kifito mana haka gasu angon namu fa yazo,takarisa maganar tana lankwasa muryan ka,ta wutsiyar ido Zuleey ta gallamata harara tana me mikewa. Yake tasaki tana saka idonta kan na Taufeeq don sam kwarjinin da Sauban ya mata yasa takasa hada Ido dashi tace"excuse me!tayi maganar tana watsa yatsu wadanda suka sha kunbunan kanti,sanye take da wani riga da skirt na atamfa sunyi bala'in matseta duk da ba bayan ne da itaba amma karfi da yaji ake jujjuya su. Ko kallonta Sauban beyi ba don shi hankalin sa Yana ma kan wayan dayake daddanawa ne, Taufeeq ne da Kareem sukayi karfin halin amsa mata, Suby tace"ya shirye-shirye guy's?munji ku shiru Ashe yau dinma kuna tafe?shiru kowannen su ya mata yana danna wayansa,da mamaki Suby ta dubesu amma sai wata zuciyar ta bata amsa da kila basu jita bane. "Oyoyo sweetheart"Akeela tashigo farlon da gudu tare da nufar Sauban sai dai ganin face dinsa da rayi yasa dole ta ajiye duk wani kissa da bariki da taso aiwatar wa,cikin rawar jiki tashiga gaishesu,cike da kulawa Taufeeq da Kareem suka amsata amma gogan ko dagowa beyi ba balle tasa ran ze amsata,"amarya kina lafiya?karem yayi maganar yana dan murmushi, Akeela ma murmushin tayi tace"lafiya lou munjiku shiru ga events da zamu fara gudanar wa tun jiya amma baku iso ba sai yau. "Aikam kinsan ogan be gama wattaakewa da tafiya ba so munjira ya huta sai mu shigo agaisa, Akeela tace"eyya babu komai,duban Sauban tayi tare da langabar dakai tace"Baby inata magana amma kayi shiru, dagowa Sauban yayi tare da Kura mata ido duk da bata ganin eye ball nashi amma sai da kallon yasata taji babu dadi,agogon hannun sa ya kalla tare da duban su yace"please Taufeeq kuyi abinda yakawo mu cuz time yana tafiya, Taufeeq yace"Ok. Dagowa yayi cike da basarwa yadubi Akeela yace"amarya nawa kuke da bukata ne?na hidima nd everything? "10 millions naira! Sukaji ambasu amsa,duk cikansu suka dubi inda maganar yafito har shi gogan sai da yadago. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [5/28, 11:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 39/40 ______Sosai maganganun hajiya Aliya suka tsaya ma Adda zainab a ranta domin tashiga fargaba tare da tsananin tashin hankali,lallai tasan wacece hajiya Aliya duk abinda ta sama gaba to tabbas sai ta cimma nasara,hankalinta a tashe yake sosai take safa da marwa a cikin dakin nata,a gefe guda kuma damuwar ta daya shine haryanzu bataji sakamako akan bilkisou ba,a koda yaushe cikin jiran tsammanin kira take amma shiru ga biki ya gabato saura kwana biyar kuma can maidugrin zasu nufa don acan ne ake taron biki,sosai hankalinta yakasu gida biyu,wani tunani ne yafado mata cikin rai don haka da sauri tadauki wayarta tafara laluban layin hajiya Aliya,sai dai kash!sanar da ita ake wayan fa haryanzu a kashe take alamu ya nuna tabbas bata dawo daga kasar nijar dinba. ****** Sanye takeda doguwar riga mai hannun armless,roba ce tasamu waje ta lafe a jikinta wanda har tayi sanadin bayyanan duk wani halittun ta saboda shape
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87