Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,315 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bugewar su ta bayyana,da sauri zuhra tadan dafe goshinta tare da cewa"ouch! Matsawa gefe tayi da sauri saboda kallon da taga Sauban na mata sosai tasha jinin jikinta,sake hade rai yayi dama da ragowar 6acin ran da Akeela ta hada masa yake,cikin tsukakkiyar fuska yace"Ina zaki da wannan dressing din haka?in ina Zuhra tafara"dama..d...dama leqawa zanyi nadubo abu shine,cikin muryan tsawa yace"Dallah go back my friend,wallahi akan ire-iren wadannan banzayen dressing din da kike a gidan nan sai na baki mamaki,yayi maganar yana ra6ata ya wuce, Bodejo da fitowan ta kenan daga palour Galadima tace"To sarkin kwarwa kadawo kenan,yanzu kuma ba zata samu wani sakewa ba,haba jama'a wai meyasa duk idan kashigo da masifar fadan ka baka saukewa kan matarka sai ita? Sauban fuska a daure yace"to ai itama matar tawa ce Bodejo,idan ki kaga na mata fada itama lefi tayi, Bodejo tace"to sannu me mata ai saika cigaba. Mikewa yayi yanufi parlourn Galadima batare da yasake bin ta Bodejo ba. Bayan kwana biyu,gabadaya Zuhra time din kanta ma wahala yake mata cuz exam da suke ta shirye-shiryen farawa sam lokacin ta na karatu ne,sai dai kullum tana shiga kowane apartment da safe gaishesu,a bangaren Ammi kuwa sosai take samun kalawa,don sam Ammi bata dauke ta wata surika ba,sunyi kusan kwana biyu basu hadu dashi ba hakan ba karamin faranta mata rai yayi ba saboda ta fahimci a duk sa'in da zasu hadu sai ya nemi lefi ya liqamata ya hauta da fada,Yau ma kamar kullum da wuri suka gama Exam dalilin hakan yasa kawai ta nufi gidan muneefa,sosai Muneefa tayi murnan ganinta ta dade sosai a gidan sai bayan isha'i sannan Mus'ab yadauko ta yadawo da ita,bude motan tafito tana dan rissinawa tace"to Yaya Mus'ab nagode sosai Allah yabar zumunci, murmushi yayi yace"Ameen kanwar mu kicema rigimammiyar tsohuwan nan bazan samu leqowa ba amma ga wannan ki bata"yayi maganar yana miko mata wani leader bag me kyau sannan sukayi sallama yazuge tinted window dinshi yaja motar,cikin natsuwar ta tashiga gidan,harta gota first gate sai taji kamar ana binta a baya ko kafin tayi yunkurin juyowa taji anfisgota,a gigice ta bude baki da niyyar ihu sai dai jitayi andane bakin da yatsu,sosai taji wani azababben zafi, face dinsa ta kalla sosai ya canza jikinta ne yadauki wani irin rawa da tsuma,bakinsa har rawa yake tsaban masifar dake cinsa fuskar nan tayi jajawur,hadata da jikin gate din yayi,da karfi Zuhra ta rintse ido domin kuwa ta sadakar yau me kwatar ta sai Allah,muryan shi tajiyo cikin amo yana magana"Wancan wane dan iska ne ya ajeki a mota?Fateema da aure na a kanki kike kula wasu mazan?da aurena akanki kike cin amanata?wai halan kina mance ke din matar aure CE koh?yayi maganar cikin muryan tsawa yana me matse mata hannu gam kamar zai balla,wani irin kuka Zuhra ta saki jikinta kuwa banda tsuma babu abinda yakeyi"Am talking to you teemah!!!yayi maganar yana daka wani tsawa wanda yasa Ammi fitowa ita da Daddy don apartment dinsu tadan fi farko duk da kuwa tazarar su,cikin muryan kuka Zuhra tace"wallahi ba wani na kula ba kuma ba wani ne yakawo ni....bata karisa ba yace"To uban waye ya sauke ki a mota?karya zanmiki? "Kai Sauban lafiyan ka kalau kuwa?Wai menene kakeyi haka ne?sakin mata hannu kafin ranka yayi mummunar 6aci wallahi a gidannan"Ammi tayi maganar cikin 6acin rai,yakasa sakin ta saboda bala'in kishin da ke cinsa a ransa, Daddy yace"Wai bada kai ake magana ba?sakinta yayi Yana me kafa mata idanuwan sa da sukayi jawur,itakuwa kanta na kasa banda kuka babu abinda take rusawa. "Meke faruwa ne Sauban? Daddy yayi maganar yana karisowa cikin kamewa,itako zuhra kamata Ammi tayi tare da maidata gefenta,yanaso yayi magana yakasa saboda ruwan kwallan da ya taru masa a idanuwa,juyawa kawai yayi yanajin kansa na sara masa yafita daga gate din, Daddy bece masa komai ba don yaga yanayin mode dinsa,"kamata muje ciki muji meyafaru"kamata Ammi sukayi har parlour ta ajeta kan carpet duk suka zauna,nan Daddy yake tambayanta abinda ke faruwa"Wai saboda yaga an sauke ni a mota shine yashigo yafara fada"tayi maganar cikin sanyin murya, Daddy yace"wanene ya ajeki a motar? Zuhra tace"Yaya Mus'ab din Aunty Muneefa ne"Daddy yace"A'ina kuka hadu dashi har ya dauko ki?nan Zuhra tafara in ina alamun rashin gaskiya"da...dag...daga gidan su naje wajen Aunty Muneefa daga school na wuce"Daddy yace"okay to karfe nawa ya saukeki?zuhra tace"wajen 8:17 kayahakuri Daddy"Daddy yace"wakika tambaya? Zuhra cikin tsananin tashin hankali tace"Bodejo kawai tasani. Girgiza kai kawai Daddy yayi yace"tashi kije da safe zan nemeku kedashi"cikin muryan kuka Zuhra ta mike tafita,da kallon tausayi Ammi tabita tana takaicin abinda Sauban kema Zuhra,duban Daddy Ammi tayi zatayi magana,hannu yadaga mata tare da cewa"Hmmmmm!"dole Ammi taja bakinta ta tsuke. Duk da ya fita apartment din da 6acin rai amma hakan be hanashi soyewa da matarsa ba,duk da bawai wani dadi da gamsuwa yake ba amma haka yake hakuri don gudun fadawa halaka. ********** "A gaskiya Alhaji nagaji da rashin adalcin da ake gwadamin a gidannan kada fa kamanta nima fa matarka ce,akan me tunda kazo duk inda zaka sai da hajiya Aliya kake zuwa?dame tafini?kyau ko kuwa ilimin addini dana boko?dan murmushi Alhaji iliyasu yayi yana girgiza kafa tare da sipping coffee"Alhaji magana fa nake maka"Adda Zainab tayi maganar damuwa tattare da a face dinta,ajiye cup din Alhaji iliyasu yayi yana duban Adda Zainab"Bata fiki da komai hasalima ke kika fita dashi,amma fa kuma ada,domin kuwa a yanzu tafimin ke sau dubun dubata,kin manta ada lokacin da kika fifita ta akan kowa naki,hatta ni mijina?sai nace miki kizo muyi tafiya kiki,amma ita da zarar tamiki kike binta ki tafi?to bari kiji a yanzu Hajiya Aliya tafimin ke nesa ma ba kusa ba. Wani kuka Adda Zainab tasa tace"wallahi baka isa ba Alhaji,wallahi sai na illata hajiya Aliya sai na maidata abar kwatance"tana karisa fadar hakan tafita tana share hawaye tare da jin matsananaciyar Hajiya Aliya da Alhaji iliyasu a ranta,zuciyar ta sai ingizata takeyi akan wani kuduri nata. Shikuwa Alhaji iliyasu sam baiji dar ba hasalima waya yadauka yakira hajiya Aliya akan tagama shirinta su wuce. Sosai komai ya dagulewa Adda Zainab,gashi boka hatsabibi yadena sauraranta kwata-kwata hakan yasa tafara bin malamai akan dai sabauta Ummie don tadau alwashin sai ta sabauta ta tana ganin duk abinda yake faruwa a gidan ta ba komai bane kamar matsalar ta da Ummie ( _Kai jama'a hassada mugun ciwo,mu guji kanmu da hassada domin kuwa masifa ne,gadai Adda Zainab nan haka kawai babu abinda Ummie ta mata amma ta tsaneta sam bata son ko bude ido tayi taganta a doron kasa, Allah yasa mudace ya rabamu da ciwon hassada Ameen 🤲🏽 domin maganinsa nada matukar wahala_. ) Tarasa me zatayi burinta ya cika ganin da tayi dukiyoyin ta zai tafi a banza a wofi yasa tadawo bangaren kuma Hajiya Aliya,itadai islaha sosai yakema mahaifiyar tata nasiha sai dai da alamun kamar tayi nisa batajin kira domin a duk sa'ad da tamata fada ranar kwana take zaginta har ta waya take kiranta ta cimata mutumci,hakan be hana islaha yima mahaifiyar tata nasiha. Satin su Alhaji iliyasu uku suka dawo gida daga honeymoon din tare da murnar samun cikin Hajiya Aliya,bakaramin razana da gigita Adda Zainab tashiga ba domin har Suma tayi ta tayi tare da sumbatu,wanda

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});