Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,313 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a turo ba, account din daya daga cikin mu zaki bayar mukuma muyi yanda mukeso da kudin"Zuleey tayi maganar tana tamke fuska"kwarai kuwa zuleey amma kinji abinda yarinyar nan ke cewa, Akeela wai me kika maida mu wawaye ko menene? Sauke ajiyan zuciya Akeela tayi tana kokarin danne bacin ranta"A tunanina million 3 bazai hadani da ku ba amma tunda kun matasa zanbaku 200,000 naira shikenan? "A'ah wallahi bazamu amsa ba ya mana kadan,inama lefin kibamu 1 million mu biyu? "Wallahi bazan iyaba,inama lefin 500,000?da wanne zqnji ga Kama hall da sauran su, Zuleey tana kokarin magana Suby ta hanata ta hanyar yi mata magana da ido,badon ranta yaso ba haka tadannne. "Okey to kuzo muje mufara tsare-tsaren yanda komai zai wakana,don inaso muje gidan mommy ne ko kuwa?dukka amsa mata sukayi da hakane. ******** Tarasa dalilin da yasa take tsintar kanta cikin bacin rai a duk sa'ilin da taji anyi maganar auren Sauban din,hakanan takejin wani kunci na ziyartarta tare da tsanar Akeela matuka a ranta,shikuwa mugun haushinsa takeji,a kullum cewa take bacin hadene dana su Aunty Mashahuda da wallahi bazata zauna ayi bikin ba,kai ita duk wanda taga yana rawar kafa akan lamarin na Sauban shima haushinsa takeji. Shigowa Laila tayi don bata jitaba,zama tayi tare da makama cinyar ta duka,da firgici tadago tana dubanta, ajiyar zuciya ta sauke"zuwa nayi nace miki kitashi muje mu amso dinkin mu,gasu ya Taufeeq zasu sauke mu a shagon"bata fuska tayi"Gaskiya nibazan bisu ba idan ku zaku bisu ku bisu amma ni adaidaita zan samu,takarisa maganar tana mikewa don shiga bathroom"Ummie tace nazo na fada miki idan kuma naje nabata amsar hakan to,tayi maganar tana mikewa tsaye.Cikin sauri Zuhra ta dawo tana shan gaban Laila tare da tsuke fuska"ni ban aikeki ba kice mata ganinan nashiga wanka ne,tayi maganar tana juyawa cikin sanyin jiki, dariya Laila ta kunshe tana me fita. Bata wani jima a toilet dinba ta fito ta shirya a gurguje don tasan basu fiye son delayed ba yayyen nasu,ba wani kwalliya tayi ba a fuskar ta,Dubai gown Army Green ta sanya sai sneaker black tayi Rolling kanta,dan karamin hand bag dinta baki tadauka tafita da sauri,ilai kuwa tana fita ta hango Laila da nihal a parking space jikin motar ya Sauban,wani kululin bakin ciki da bacin rai taji ya taso mata lokaci daya,harara Laila ta aikamata tace"Zaki gamu dasu Yaya wallahi babu ruwan mu kin bata musu lokaci,bata kulata ba suka bude motar suka shiga, Taufeeq ne ke driving,shikuwa Sauban laptop ne akan cinyar sa yaketa sarrafata,gaishesu sukayi duk suka amsa,cikin barkwancin sa yadube su"Allah yasa telan be mata muku dinki ba,don nasan teloli sai addu'ah,cikin raha Laila tace"Ai Yaya Ameer ya iya dinki sosai,tun daga Zaria yazo yima su Aunty Mashahuda dinkin biki,namune be gama ba yace sai munzo da kanmu,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Ah gaskiya ne tunda aka dauko tun daga Zaria to lallai nima na sheda,don nasan gimbiyar tawa bata za6en tumin dare ko gimbiya?yayi maganar yana duban Zuhra ta jikin mirror motan,dariya Zuhra tayi wanda sai da point nata ya loma,sannan Gap teeth dinta suma suka samu damar bayyana,lankwasar dakai tayi cikin shagwaba tace"To yaya maganar saloon din bamuje bafa, gashi gobe mother's day,kuma mu a goben ne zamu henna ko?tayi maganar tana duban su nihal,daga mata kai sukayi gabadayansu,nihal tace"Kuma ranar Friday kamu ba! Zuhra tasake shagwabe muryan"Yes yaya and kamu. Tun sanda ta fara magana tatafi da duk wani kuzarinsa lokaci daya yaji wani kasala ta kamashi,banda bugawa babu abinda zuciyar sa keyi,shekara da shekaru kenan yake karya ta abinda zuciyar sa ke raya masa,sam takasa tunkarar wani da maganar balle yasamu sassauci,lumshe idanuwa yayi cikin natsuwa wanda mutum bai isa yagane ya yanayin sa ba. Cikin taushe tare da basarwa yafara ma Taufeeq magana batare da ya dubesa ba"inada baki da zasuzo,wasu daga maleysia wasu kuma daga Canada so ina bukatan hotel me kyau sosa and sai dai niban san kan hotel's din garin nan ba,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Gaskiya nima bansan kan hotel's din garin ba sai dai mukira Kareem kan ya bincika mana,let me call him"yayi maganar yana jawo wayar sa daga aljihu,jinjina kai Sauban yayi batare da yayi magana ba. Zuhra kuwa ajiyar zuciya take ta sauke wa a boye batare da kowa ya fahimta ba,dai-dai lokacin da suka iso shagon dinki me tsananin kyau don dama yasan shagon shida kanshi yake dauko Mashahuda ya kawo ta. Bude kofan sukayi suka fito tare da rufo musu kofan,tsayawa Zuhra tayi gefen Taufeeq duban ta yayi yace"to yanzu maganar saloon din zaku wuce ne, idan mundawo zamu biyu ta shagon mu dauke ku,jijjaga masa kai Zuhra tayi,kudi yaciro a aljihu wanda shi kansa besan ko nawa bane yamika mata,godiya suka masa gabadaya suka shiga shagon. Ta wutsiyar ido yake hankalce da duk wani motsinta da wani babbasar wan da takeyi. Kai tsaye shagon suka shiga,basu jima ba suka fito dauke da kayan su Ghana most go guda medium,an dinka a goge duk da sunso dudduba kayan amma ganin mutanen dake cikin shagon yasa suka hakura,don Zuhra a takure take abinda ta tsana kenan a rayuwar ta,har bakin titi Ameer ya rakosu suka samu napep sannan yajuya,kaitsaye shagon saloon din suka isa me suna saleema hair beauty saloon matar tana da matukar kirki,gashi tana tsananin son Zuhra,basu jima ba bayan magrib suka gama ana Shirin Kiran isha'i,turama da Taufeeq address din Zuhra tayi,babu kuwa bata lokaci yadawo,wannan karan shi kadai kuma ta map ya dinga bin address din. Kudin saloon din yabiya sannan tadauki kayansu yasanya musu a cikin boot,kaitsaye suka isa gida. _________ Washe gari Biki yayi biki inda labarin event din su Akeela kawai akeyi,maisuna suger mommy's day,sosai suka kashe kudi a event din wanda akayi a gidan hajiya daharatu,wato mommy, sosai ranar 'yan less sukayi iskancin da suke so, Akeela kuwa a daren mutane uku sukayi masha'arsu da ita,sun cancare matuka gaya,sai karfe ukun dare suka watse. A dai-dai kuma wannan lokacin aka tura ma da Sauban video. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 7/6/23. [6/8, 21:41] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 43/44 _______Ganin bakuwar number ce yasa yadanja siririn tsaki tare da kin bude message din a fili yafurta"Trash! Yana takaicin 'yan matan dake bibiyan sa wadanda sam basu da aji balle ayi maganar kamun kai,wayar ya ajiye a side yana mikewa tare da shiga toilet don dauro alwala,saboda Sauban mutum ne mai rukon addini tsantsa shiyasa lokuta da dama yake jin dan sanyi a zuciyar sa. Washegari da safe GALADIMA family suka tashi da shirye-shiryen mother's day,Ammi,Ummie,Mom,Mommy sunyi kyau sosai don babu wacce bakinta basu zoba musamman Ummie don da kawayen ta na kaduna da Zaria,haka ma Ammi kowa dai yatara mutanen sa,kanofi uku aka kakkafa,duk wannan shagalin su ZUHRA basa gidan suna can wajen henna,sun hada mother's day dinsu yayi masifar kyau,duk da iya kacinsu ne don ko maza basu shigo gidan ba, security ma suna can gate 1,haka zalika sunsa police mata kan su kula duk wacce tayi video Koda waya ne to aka mata,duk da cewa ba badala sukayi ba,sunyi wanka mahaukatan lace hadaddu,da Ammi da Ummie

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});