Chapter 17
Chapter 17
Muneefa tace"Sis muje kada kuyi magrib, Ammi tasaki murmushi tare da duban Akeela"Akeela ya hajiya maimunan take? Cike dajin dadi tace"wallahi tananan lafiya mommah. Murmushi Ammi tasake saki akaro na biyu tace"to don Allah kigaisheta mungude sosai. "Ai babu damuwa mommah nima fa 'yar gida ce. Ammi murmushi kawai tayi bata sake magana ba,muneefa tace"yee gaskiya ne Auntymmu, Allah dai yabar kauna keda ya SAUBAN! A gigice zuhra tadago tana duban muneefa sai dai kowa hankalinsa baya kanta,wani mummunan faduwar gaba ta tsinci kanta a cikin jin an ambaci sunan Wanda batayi zato ba,a kaikai ce tasake duban Akeela da wasu second's zuwa can ta sauke ajiyar zuciya,aranta tace toni meye damuwa na? Nanfa muneefa tafara magana"Ai wallahi bikin nan haba za'ayi abinda ba'a taba yiba sai ansan anyi biki na jinin Galadima auren ya Sauban ai dole muci uwar sabada. Akeela tace"ai gaskiya za'ayi biki nagani nafada hmmm kudai Allah yakaimu lokacin, mommah muntafi tayi maganar tana ma Ammi bye bye. Daga Zuhra har Mashahuda kallon mamaki sukabi Akeela dashi, Mashahuda tadubi Ammi tace. "Cabdi wallahi Ammi kinsan da matsala Yaya Maison mace mai kunya amma jibi wacce aka bashi matsayin mata?hmm wallahi nidai bana son Yaya ya aureta sam,tayi maganar tana daga hannu tare da nuna iyakacin gaskiyar ta, sauke ajiyan zuciya Ammi tayi tace"please Mashahuda ni bana son kananun zantuka haba abar maganar. "Hmm Ammi kema fa kinsan Yaya be dace da wannan yarinyar b.... "Allah Mashahuda zan saba miki,tayi maganar cikin muryan bacin rai. Itadai Zuhra ko tankawa batayi ba tanata yanka cabej dinta,sai dai hakanan tatsinci zuciyar ta cikin bacin rai lokaci guda. Hakanan taji tayi mugun tsanar Sauban din dashi da Akeela. *******^^^****** Sosai yaqara gogewa da kyau yazama wani classic guy wanda ko a malysia ma 'yan mata rububinsa sukeyi. Yarasa dalilin da yasa yake sake tsanar auren da ake nema a qaqaba mishi itakanta yarinyar bayajin zai iya aurenta duk da kuwa besanta ba. Messenger sane yashigo office din yace"Sir kayi baki. Duban CCTV camera dinda ke office din yayi yana duban mutanen dake Zaune a wajan office din nasa,maido da duban sa yayi ga massenger yace"Miracle who re those people? "I don't know Sir,yayi maganar cike da girmamawa. Dan girgiza kai Sauban yayi tare da cewa"Ok jeka shigo dasu. "Ok Sir,yayi maganar yana fita babu jimawa yashigo da baqin. ******** "Boka so nake a sauko da auren lokacin da aka sanya na bikin nan wallahi yayi tsayi ita kanta yarinyar takosa ace tayi aure tahuta,bari kaji nifa so nake a mallake mana yaron ya zama na bayajin maganar kowa sai nawa,kai yazama mai taurin kan tsiya. "Hahahaha,aka kyalkyale da dariya,wani dan wadan aljani ne wanda sam bayada kyan gani ko kadan kuma daga ganinsa baya da imani yace" _BANADA LAFIYA FANS DON ALLAH INA BARAR ADDU'AN KU👏🏽_ Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 15/16 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ PLS KUTAYANI DA ADDU'AH MASOYA ALLAH YAKARAMIN LAFIYA DON CIWO YASANI GABA SHIYASA KUKA JINI SHIRU KWANA BIYU BANJIN DADI, NAGODE SOSAI DA SAKONNIN GAISUWAR KU MUSSAMMAN MA KE *MAMAN HEELAL* KEDIN TA DABANCE. _____Zuhra ce zaune a parlon Bodejo tana yimata massage,sallamar Baba mudi gateman sukaji a bakin kofan parlon,amsawa sukayi inda Bodejo tabashi izinin shigowa. Cike da girmamawa ya rissina yace"Barka da warhaka Bodejo,inayini ina gajiya? fuskar ta kadaran kadahan tace"yauwa mudi lafiya Alhamdulillah ya kuma aiki? Baba mudi yace. "Alhamdulillah! Dama wani yaro ne a waje yazo yake cemin don Allah nakira masa Fateema. Cikin natsuwa Zuhra tadago tadubi Bodejo itama ita take kallo,maida dubansa tayi ga Baba mudi tace"Fateema kuma mudi?wa Fateema tasani a garin nan har zai aiko akira masa ita? Tayi tambayar cike da mamaki. "Wallahi kuwa Bodejo bansan shi ba nidai yanata roqona kan nakira masa ita. "Ikon Allah ko wanene haka oho?tashi kije kiji ko wanene. Dan tsamm Zuhra tayi tare da dan bata face tace"nikam bazani ba Bodejo wallahi bansan shiba kawai ina zaman zamana ya wani kirani? Takarisa maganar tana kokarin shiga hanyan corridor din Bodejo,sakin baki Bodejo tayi tana duban Zuhra,kallon Baba mudi tayi tace"shikenan mudi kace tana zuwa. Mikewa yayi tare da fita,murmushi kawai Bodejo tayi tana kokarin mikewa ne sai ga Mashahuda tashigo,dan gaida Bodejo tayi sannan tace. "Bodejo ina Zuhra ne tundazu Shuraim yazo nemanta Baba mudi yace yazo ya kirata amma taqi fitowa. Dan tabe mouth Bodejo tayi"Toh ni ina nasanin mata,bansan me take nufi ba,wanine shuraish?dan gwalo idanuwa Mashahuda tayi"kaji Bodejo kuma da bata suna bafa shuraish ba Shuraim ake cewa. "Uhum kudai kuka sani da wani iyayi da sanabe abinda dai nafada shikika maimaita. Rausayar dakai tayi kaitsaye ta nufi bedroom din Bodejo. Koda tashiga kwance taga Zuhra sai daddanna phone nata take hankali kwance,ganin Mashahuda yasa tamike cike da fara'a a fuskarta tace"Aunty Mashahuda kece? Hararar wasa ta zabga mata tace"kyace mana nice tun dazu mutumi yazo nemanki kina wulaqanta sa haba Zuhra menene haka? "Aunty nifa bansan shiba bansan koshi wanene ba akan me zan fitan masa?shiyasa ma ban fitaba,takarisa maganar tana dan babbata fuska. Itama Mashahudan bata fuska tayi tace"Lallai ma yarinyar nan kinci uwar rainin wayo to Shuraim ne yazo kitashi kuje ku gaisa mana. "Shuraim! Zuhra ta maimaita sunan alamun bata ganesa ba tace"Aunty ni bansanshi ba. Mikewa Mashahuda tayi tare da fita tace"idan kinje wajen ai zaki gane wanda nake nufi,takarisa mgnr tana barin dakin. Tsuru tayi tana bin kofan da kallo tadau kusan 6 minute's a zaune kamar wacce aka dasa,zuwa can tasauke ajiyar zuciya tare da mikewa,closet din ta tabude taciro wata Dubai gown mai taushi wanda yaji wasu irin flower's maroon colour,sannan tasaka viel din tayane kanta dashi,flat shoe baqi tasaka batare da tamurza ma kyakkyawan face dinta komai ba tafito parlon, Bodejo ta taras a zaune tana kallon Africa TV 3 dan sunkuyar dakai tayi like munafuka sum sum tafice. Cikin sanyin jiki take tafiya kamar mejin tausayin kasa acan gefen apartment din Ammi ta hango Mashahuda da wani don bata ganesa ba saboda ya juya mata baya,a hankali take tafiyar har ta isa inda suke zaune,sallama tayi cikin zazzaqar muryanta mai sanyi da dadi,da sauri yadago don jin muryanta. Da mamaki Zuhra take dubansa a hankali tace"Yaya dama kaine? murmushi kwance akan fuskar Shuraim yace"Ea nine Zuhra. Dan tsamm tayi tare da duban Mashahuda,mikewa Mashahuda tayi tare da duban Shuraim tace"bari nashiga na fito kafin ku gama gaisawa,sake fadada fara'a Shuraim yayi tare da cewa"Allah yafito dake lafiya Auntymmu,zuhr kuwa sakato tayi tana duban Mashahuda har tashiga parlon su,ajiyan zuciya ta sauke saboda muryan Shuraim da taji yana cemata ta zauna. Karasawa tayi kujeran da Mashahuda ta tashi ta zauna,dukar da kanta tayi kasa tafara wasa da yatsun hannunta. "Babu gaisawa ne Zuhra?Shuraim yace. Cike dajin nauyi da kunya cikin sanyin muryanta tace"eyya ba haka bane wallahi yaya don Allah kayahakuri, inayini? "Sai dana roka?yayi maganar still murmushi kwance saman fuskansa. "Kayahakuri,tasake maimaitawa cikin sanyin muryanta. "Lafiya lau Alhamdulillah ya kwana biyu? "Lafiya lau wallahi. "Ashe anata shirye-shiryen school ne?to Allah yabada sa'a Aunty Mashahuda take fadamun. Zuhra tace"Ea anata shiri munkusa fara zuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87