Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,263 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 14/4/23. [5/4, 14:37] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 29/30 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *BARKAN KU DA SALLA MASOYA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA,WADANDA SUKA RIGAYEMU GIDAN GAAKIYA ALLAH YAJIKANSU.....YAWWA NACE BA GORON SALLAH KADA A MANTA DUK WANDA ZAI BADA YAZO A BASHI ACCOUNT NUMBER😁HAR NAMAN SALLAH DA CIN-CIN ZA'A IYA TUROWA TA ACCOUNT.* *DUBUN GAISUWA A GAREKU MAMAN ASLAM,MMN TAUFEEQ,UMMU MEE'AD,GODIYA DA TARIN KULAWA.* ________Gabadaya dakin daga masu tayasu kuka sai masu juriya haka suka kasance, Zuhra kuwa wani irin nishadi takeji wanda tunda take bata tabajin irin sa ba. Nan Galadima yake sanar dasu abinda yafaru,babu wanda baishiga shocked ba, Ummie haka ta taso ta rungume Sauban tana me sake zubda hawaye cikin muryan kuka tace. "Nagode son Allah ya saka maka da mafificin alherinsa bazan taba manta kaba a rayuwa ta, Allah ya dafa maka a lamuran ka. Amma tace"ubangii Allah ya baka mata tagari me kula dakai Allah ya daukaka duniya da lahira. Gabadaya dakin sai amsawa akeyi da amin,ita kuwa Mom takaicin irin addu'o'in da ake kwaranyo ma Sauban takeji,domin ji take kamar ta shake shi ya mutu kowa ma ya huta,banda yaqe babu abinda takeyi. Anan suka sake godiya ga Allah akayi addu'o'i suka dunguma kuma jabi road don Ummie sarai ta warke, Zuhra na maqale a gefenta. Ko kafin su iso Abba yasa anyimusu oder lafiyayyun kalolin abinci,tuwon shinkafa miyan egusi,jollop din shinkafa,sakwara da miyan alayyahu sai snack's da drink's. A babban sashen Galadima suka zauna wanda idan yashigo da kaduna yake zama,matan kuma suka nufi sashen Ummie. Amma tace"Niko lafiya hajiya Zainab gabadaya number ta baishiga?nakirata ban sameta ba nakira number farida tace batanan tayi tafiya. Ummie tace"toh ina Adda Zainab taje ne?tayi tafiya kuma takasa sanar dake Amma? gaskiya da mamaki. "To nima dai shi nagani,ita takanta taci burin zuwan wannan ranar shiyasa nake nemanta fa, Allah ya kyauta bari zuwa anjima nasake gwada kiranta. ****** Hajiya Aliya da hajiya Zainab kuwa basu da wani choice da yawuce amsan bukatan boka,haka hajiya Zainab tanaji tana gani wadannan kattin matan sukayi amfani da ita sannan a gaban boka hatsabibi yana watsa musu wani irin ruwa yana cigaba da surkullen sa. Sai da suka shafe awa daya suna abu guda zuwa can suka kyale ta,boka yace suje zuwa anjima tazo ta amsa saqon magungunanta,su kuma matan suka zauna anan. Banda dariyar keta babu abinda hajiya Aliya keyi ganin yanda aminiyar ta ke tafiya a tattale,sosai hajiya Zainab ta kulu ta dubeta da niyyar tayi magana amma sai ta rigata. "Kada kice komai don tun kafin ayi hakan dake akayi dani fin sau goma,ke nifa idan har akan biyan bukata ne zan iya komai,ke ko boka hatsabibi ne yace yana son kaina zanbashi,ke ko dan mutum yace nakawo zankawo. Takarisa maganar tana taunar chwengum"kas kas kas". Sai yau hajiya Zainab tasake yarda lallai aminiyata hatsabibancin ta ko shedan tsoron ta yakeyi. "Nikam mu amsa maganin nan mutafi don wallahi Alhaji baisan da fitana ba kuma kowane lokaci zai iya dawowa,gashi layina ba za'a iya samu ba. Hajiya Aliya tace"toh mukoma mu gaya masa mukam tafiya zamuyi yanzu. Haka suka sake komawa inda babu abinda ke tashi a dakin sai hayaqi da wani irin wari,sun dauki minti biyar a tsaye kafin boka hatsabibi cikin muryan tsawa yace. "Tsayuwar me kuke musu a hanya alhalin zasu wuce,wallahi duk Wacce aka gurgunta babu ruwa na,duk cikansu jikinsu na rawa suka fada dakin. Zama sukayi a kasa,wani bakin kwarya boka hatsabibi ya dauko tare da yin wasu yare sai ga kullin magani guda biyu sun bayyana,hannu yasa ya dauka inda yadaure face tare da duban hajiya Zainab yace"Kinga wannan hajiya,kije kisamu dai-dai kan inda 'yar uwanki ke kwanciya ki barbada wannan garin maganin,babu wanda zai gane kinsa wani abu,ni kuma ina tabbatar miki da muddin anyi aikin yanda ya kamata to fa 'yar uwanki zata kamu da mummunan ciwon barin jiki(paralysis)wanda har tabar gidan duniya babu maganin shi. Sai kuma wannan kisamu abincinda kikasan shine abincinda tafiso duk cikin abinci ki barbada mata hhhhhhhhhhh....daga zarar kika barbada mata taci kowa gudunta zai dingayi harta 'yan uwanta da uwanta ke da kowama nata,don zata dinga magana ne bakinta na wani irin aman wari tare da fitar da wasu tsutsotsi. Wani irin dariya hajiya Aliya da hajiya Zainab suka sanya najin dadi. "Idan wadannan basuyi ba to dole sai munyi mummunan aiki akansu. "Ayi boka hatsabibi ka kasheta inaso ta mutu natsani in daga ido naga bilkisou. "Hhhhhhhhh kisa a ranki aikinki ya kammala gashi kutafi yanzunnan. Da sauri suka mike ko gidan da suke sauka basu koma ba don dama bawai sunzo da kayan canji bane,hand bags ne shima suka tura driver hjy Aliya yaje ya dauki musu,nanfa suka fafaro hanyar dawowa lajeria🤪 ______ *NIGERIA*______ Haka wadannan ahalin suka kasance cikin farin ciki inda a washegari Sauban zai koma Malaysia,ummie ma tace zataje maidugri kusa da diyarta ta kwana biyu ta dawo. Tunda babu daman ita ta zauna kodan school dinta,inda Amma itama atake anan tace zata bisu taje sosai sukaji dadi babu bata lokaci Abba da Daddy suka fita nema musu jirgi Wanda zaije borno kona 5:00 pm ne. Cikin yardan Allah kuwa suka samu jirgin inda nan suka tafi suka bar su mommy da Abba da kewarsu,maimoon ma sai rigima suke kan sai sun bi Ummie. Washegari tun 7:00 am Kareem yadauki Sauban don kaishi airport,jirgin 7:30 zaibi hakan yasa basu wani jima da isaba aka fara neman matafiya aiko nan Sauban yatafi suna ma juna waving hannu shida Kareem. Anan ma wani sabon kwarkwaryan walima aka hada don su Mashahuda sunyi farin ciki haka su nihal saboda babu wanda besan 'yar tsaman dake tsakanin Ummie da Zuhra ba. Duk da tasan yatafi Amma sai ta nemi walwalarta tarasa tunda taji labarin shine mutumin da yayi aikin haqo asirin da aka mata itada Ummien ta sai taji wani kiman sa da darajar sa a zuciyar ta,musamman da taji irin kasada da hadarirrikan dake cikin aikin tare da wahalar da yasha sai mutumcin sa ya ninku a idon ta,duk da tasan bawai yinsa take ba hasalima ba birgeta yake yaba yasata jan tsaki akasar ranta ta furta " _to meye abin damuwa da tafiyar nasa?kekam wawuya ce._" Yinin ranar kwanan farin ciki wadannan ahalin keyi,don saura kiris Zuhra tayi lattin School ko wanka batayi ba ta sulale tatafi gashi suna da test. *MALAYSIA* Yauma kamar kullum sanye yake cikin suit gray sosai yayi kyau duk da fuskar sa babu alamun fari'a ko kadan amma hakan 'yan matan company din nan keta binshi da mayataccen kallo,dan tsaki yayi kasa² tare da sake tamke fuskar a hankali ya isa office dinsa. Nan aka fara shigowa yimasa barka da zuwa maza da mata. Aiki yakeda shi sosai akan wani designer shoe da yafito wanda sam bema bayyana ba shine take su hada don ko babu komai a fara gani a company nasu shysa take so busy yaudin kam,don duk wanda yazo nemanshi ma baya ma samunsa saboda ya gayama secretary dinsa cewa duk wanda yazo tace yana aiki. Bashi yabar office ba sai kusa

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});