Chapter 32
Chapter 32
ta mata akwati guda haka su Ummie suka bari Dubai cike dajin dadi,kwanan Ummie da Ammi biyu a kaduna suka wuceZaria kai tsaye dukkan su anguwan su Ammi suka nufa saboda ita iyayenta sun rasu sai 'yan uwa don haka zata ta kwana daya gobe da safe tazo gidan su Ummie don zasubi jirgin 4:30 ne sai su wuce gida. Sosai ko wacce 'yan uwa sunyi murna da ganinta, washegari kuwa suka nufi gida. ********** "Aminiyata nifa a tsorace nake haryanzu ba'a kirani ance gashi wani abu yasameta ba,ke in takaice miki ma har Zaria sunje itada matan Alhaji Taleeb sun kwana"Adda Zainab ne ke maganar nan. "Hmmm nifa lamarin matan nan hajiya Zainab yafara bani tsoro,kinsan Kuma aikin nan yanda aka umurce mu haka muka gudanar,to amma bari nakira boka hatsabibi"hajiya Aliya ta ida fada tana dauko wayarta dake aje kan center table,nan tashiga laluben number boka amma abin mamaki babu ita babu alamanta,sake dai bincika wa tayi amma still bata gani number,nandanan tamike tsaye cikin tashin hankali tare da dafe kirji tace"Nashiga uku ni Aliya,taya lefin wani zai shafe wani?da sauri Adda Zainab tamike tana dubanta. "Lafiya aminiya meke faruwa ne?naga hankalinki atashe kuma ga abinda kikace?duban hajiya Zainab hajiya Aliya tayi tace. "Narasa number boka hatsabibi kuma wallahi ko kaffara bazanyi ba munyi masa gagarumin aiki mun lalata masa aiki,nidai da nasan haka ne wallahi da nabarki ke kadai kinyi aikin ki da bansa hannu ba,nashiga uku gashi iya duba na naduba banga number ba,aikin banza kema ba number ne gareki ba. "Munshiga uku yanzu Yaya zamuyi. Yaya zamuyi kuwa tafiya ce ta ganmu don kuwa tunda kikaga babu number turo aljanu yayi suka goge don yasan dole mu nemesa kinsan abinda yace fa tun farko. "Nasani sai dai gaskiya nikam wannan karan da wuya nakoma don gudun zargi banso a zarge ni.Wani banzan kallo hajiya Aliya ta aikama Adda Zainab"mekike nufi kenan hajiya Zainab?kina nufin nikadai zanje?cabdijam!wallahi baki isa ba aikin kifa akeyi. Kasa da murya Adda Zainab tayi tare da marairaice fuska tace"A'ah ko daya ba haka nake nufi ba,banason abinda zaisa idon mutane sufara sauka kan mu kingane?ke widowed ce nikuma kinga matan aure CE so sai afi samin Ido ba'a samiki ba,sannan kinsan halin Alhaji na ciki da bai kinsan halinshi sarai,don Allah kiyahakuri kije mana duk abinda ke akwai inkin dawo sai muji kokuwa? Dan sakin fuska hajiya Aliya tayi tace"Ahto 😏 kada a maidani wata bican fa, saboda ni for sale CE. Dariya Adda Zainab tayi"A'ah ko daya wallahi matsayin ki ya wuce haka a wajena kedin ta daban ce so kisha kurumin ki nidake we're together"takarisa zancen suna tafawa da juna tare da kyalkyalewa da dariya. "Nima idan naje akwai aikin da nakeso yamin don inaso nayi wufff da wani Alhaji dana gani lokaci daya yashiga zuciya ta yayi kane-kane. "Au dagaske?Kai amma matan nan ke shedaniya ce shine bani da labari ko a sanarmin,?to a'ina aka samosa? "Hmmmm kedai bari nifa hajiya Zainab da kafar dama nashiga GALADIMA house don anan naga MIJIN Aure. 😳Diddilo idanuwa hajiya Zainab tayi gabanta na masifan faduwa cikin mamaki tace"kekuwa wanene wannan? Wani dariyan hajiya Aliya ta kyalkyale dashi tare da cewa kedai bari ayi sha'ani kawai,tana sake kyalkyala dariya. Itakuwa Adda Zainab gabanta ne yashiga dakan lugude a zuciyar ta tace _Da yarda bi'izinillah babu ke babu shiga gidan GALADIMA hajiya Aliya,shedaniya kawai niban shiga gidan bane kece zaki shiga?_ a fili kuwa tasaki dariya tare da cewa"Ayyoririrrriiiiii amarya amarya amarya a gidan GALADIMA house,pls kifadamun wa idonki ya kyallo ne? Fari hajiya Aliya tashiga yi da idanuwa kamar wata budurwa. *GALADIMA FAMILY* Kafin kace me sha'anin biki yagama kankama yinshi kawai akeyi babu kama hannun yaro, Rammat tayi kuka sosai saboda tasan cewa bazata taba samun Sauban ba sosai tamika lamuran ta ga Allah ta fawwala masa komai,inda hajiya Biba ko takasa natsuwa shige shigen malamai ko takasa sai canye mata kudade sukeyi ko wanne da karyan dayake lafta mata,hakan ba karamin sosa zuciyar Rammatc set yakeyi ba A lokacin da biki yarage saura sati uku da kafini daya dangin ma'aruf gobe zasu kawo lefe,kafin kace me anfara tarbansu tun daren ranar,duk wani kalolin girki Ummie da Ammi ne sukayi tare da Mashahuda da zuhra harda ma muneefan. Washegari kuwa takama asabar su Mashahuda,muneefa,duk basunan sunje gidan da ake musu gyaran jiki su kuma su zuhra,Laila da nihal suna gida. Wajen karfe daya mommy da Abba suka diro mota biyu sukayo don babu wanda yasan da zuwan su,sai karar Horn dana motoci akafara ji,ko kafin kace me ma'aikatan gidan sun bude dayar motar Sharon sunfara fiddo da akwatuna suna nufar sashen Galadima,a lokacin mutanen gidan suka firfito ko wanne baki bude cike da mamaki akwatuna sha shidda cif. Ummie tadubi mommy tace"Kai mommyn yara wannan wane irin zuwa ne haka?nuna Abba tayi tace"surprise ne daga Abba babu ruwana, dai-dai nan Zuhra tazo da gudu ta cafeta tsananin murna,Suma su nihal karisowa sukayi suna ihun murna,kafin kace me gida yafara hautsinewa da hayaniya don maimoon da Ateek ganin Zuhra suma yasasu murna nan su Ummie suka koma ciki don shiryawa su kuma suka mika apartment din Galadima don mika gaisuwa, da sallama suka shiga sashen inda suka cidda Bodejo rike da haba tana karewa lefen kallo. "Hauwa wannan lefen na waye haka kuka taho dashi?ni fatsuma. "Ai dai kyabari su sasara ko?daga shigowa ko hutawa ba'a yiba bare maganar gaisawa sai ki fara da lefe? Murmushi Abba da mommy sukayi,nan suka fara gaggaisawa da juna, sun gaisa sosai sannan mommy tamike tace bari taje tayi sallah. Anan Abba ke sanar dashi kayan lefen Taufeeq ne daya hado masa shine nasa gudummawar don har ya sanar dashi yace kada yahada,dama shida Sauban yaso hada musu amma sai yace shi tuntun-tuni ya gama hada lefen shi idan zaidawo zai taho dasu,naso duk da haka na masa amma sai yanuna min kada ayi almubazzaranci. Galadima yace"gaskiya ne kaga da da hankali ko, shikenan Allah ya musu albarka yanzu yaushe yace ma zeshigo?gaskiya bamuyi maganar ba amma ai dole next week yashigo Galadima. "Masha Allah Haroun Allah ya muku albarka ubangiji ya kara hada mun kawunan ku. Ameen suka amsa shida Bodejo. Nan yasake gyaran murya sai Kuma su matan na biya musu kujeran umra,shima Sauban da wannan nake tunanin na biyama yarinyar da zai auran. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ya maka albarka harouna ka kyauta kaima Allah ya saka da alkhairi. Da ameen still ya amsa nan suka dasa hira Bodejo da Galadima zuciyoyin su wasai da jin dadi. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 10/3/23. [5/24, 17:48] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 37/38 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______Da la'asar family din ma'aruf suka iso,sosai suka samu tarba me girma da karamci a farlon Galadima don maza ne suka kawo lefen,su kansu sai da suka tabbatar da ba auren kwadayi dansu yayi ba tabbas ya aure 'yar gidan tarbiyya da mutumci saboda yanda Daddy, Abba Baba Hasheem suka tarbesu cike da mutumtawa,gefe daya ga tsoho me ran karfe yasha wata mahaukaciyar danyar shadda fara tasss sai maiko takeyi,shikanshi ya burgesu yanda sukaji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87