Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,312 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

salatin me hade da kiran Daddy,a lokaci daya suka zabura Akeela da wannan hajiyar dake kanta cikin gigita,a kuma dai-dai lokacin ne kuma su Daddy suka fado parlour,inda Ammi tazube sumammiya. Tashin hankali su Daddy suka shiga ganin su Akeela a wannan mummunan yanayin,inda yanufi Ammi yadagata, Baba Hashim kuwa cikin sauri yafita daga palourn yana rintse idanuwa,wannan wane irin masifa ne? Ranga² Daddy yadauki Ammi yanufi gida da ita,nanfa Mom tashiga tambyar abinda ke faruwa,sai dai babu amsa, fifita aka shiga yiwa Ammi don Zuhra ta farfado banda kuka babu abinda takeyi,ta isa wajen Ammi tana mata fifita haka Mom ma"Wai Baban Aseef meke faruwa ne?na tambaye Zuhra tunda ta farfado batace min komai ba kuma bata bar kuka,kuku ma kunshigo da Ammi ranga²"batare da Baba Hasheem ya tanka mata ba yakara waya a kunne,babu jimawa akayi picking"Assalamu alaikum, Dr barka da warhaka,daga can 6angaren aka amsa,magana ya cigaba"don Allah Dr munason ganinka ne yanzu anan gida"amsa masa akayi tacan bangaren"To shikenan sai ka iso,yafada yana aje wayar ya cigaba da cewa"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakeel. ***** Babu jimawa Dr Ahmad ya iso,yanayin da yaga jikin Ammin ne yasa yace gaskiya sai fa anje asibiti,aiko haka suka dunguma asibitin, Zuhra akace taje ta sanar da Bodejo. Taimakon gaggawa aka shiga bawa Ammi don ceto numfashin ta,kusan awa biyar kenan ana kanta,ana cikin hakan ne kuma Galadima da Bodejo da zuhra suka shigo. "Ikon Allah Aisha kuma lokaci daya ace ciwo ya sauka?lallai Allah me iko"Mom tace"wallahi kuwa bodejo barka da zuwa,bodejo tace"yawwa Rabi,nan suka cigaba da tsayuwa, Dr Ahmad ne ya fito yadubi su Daddy yace"Alhaji muje office"da okay Daddy ya amsa sannan shida Baba Hasheem suka nufi office din harda Galadima,waje suka zauna nan Dr Ahmad yafara bayani"babu komai kawai firgice tayi da alama taga wani abu daya firgita,but Insha Allah everything will be okay,yanzu haka ma ta farfado zaku iya dubata"godiya sosai sukayi masa suna fiata daga office din,duk cikansu suka rankaya dakin, Ammi na zaune banda hawaye babu abinda yake mata,duk sannu suka shiga yimata, amsawa tayi tana me duban Daddy dakyar ta bude baki tace"Daddyn yara ALLAH yasa mafarki nake ba gaske ba,ina jin tsoron abinda na gani ya zama gaskiya,gyaran murya Daddy yace"Uhmm please Aisha calm down cuz likita yace baki bukatar hayaniya....carab bodejo ta ca6e"ku mana bayani mana Taleeb wai meke faruwa ne? Mom tace"gaskiya kam saboda kinga Zuhra tafara ganin abinda ke faruwa sannan a sashin Sauban, Galadima yace"ya isa haka kubarta ta samu natsuwa idan anje gida duk a tattauna. A ranar Dr Ahmad yabama Ammi sallama. ****** Akeela kuwa ganin abinda yafaru ba karamin rudewa da tashin hankali ta shiga ba,kuka takeyi tana fadar ta shiga uku shikenan tasan ita auren ta yanzu ya gama yawo,itakuwa hajiyar ganin abinda yafaru yasa ta tattara yanata yanata tabar gidan gudun wani mummunan abu ya auko,aiko Akeela cikin tsananin rudu da damuwa tanufi gidansu tana kuka kaitsaye sasan Guggo Laure ta nufa,da tashin hankali Guggo Laure ta tareta tana kamata suka shiga daki,ananfa Akeela ta shirga ma Guggo Laure karya da gaskiya ita kuma tahau ta zauna, bala'i tafara zazzagawa,nan kuwa ta shirya ta nufi gidan Galadima,a dai-dai lokacin su kuma suka dawo daga hospital,da kuka Guggo Laure da taresu don su sam basu lura da ita bama,duk cikansu mamaki sukeyi,musamman Daddy da Baba Hasheem,kaitsaye Ammi ta tunkara tana nuna ta da yatsa tare da kumfar baki"Aisha baki isa ki yanke abinda Allah shi da kansa ya kulla ba,dama tunda akafara maganar auren Akeela da Sauban na lura da take²n ki bakiso,taya za'ace tunda tazo gida kullum sai kinshiga gidan ta kin tayar mata da hankali?wai me ta tsare miki,kwanaki ma da tayi 6ari tace kece kika zuba mata abu a lemu tasha cikinta ya zub........bata karasa ba Baba Hashim ya katseta cikin 6acin rai,domin dai da alama yau Guggon nasu ta kure shi"Don Allah ya isa haka Guggo ya isa,ita shedaniyar jikan takice tafada miki wannan kanzon kuregen?wallahi da na kama yarinyar nan a gidan nan yau dukan mutuwa zan mata domin itadin annoba ce a cikin ahalinmu,ko makiyin mu bazamuyi fatan ya hada zuri'ah da me irin halayen yarinyar nan ba"cikin daga murya Galadima yace"Hasheem kana hauka ne? Guggon naka kake fadawa haka?gabadaya idon Baba Hashim ya juye da bala'i yace"Galadima kadena sauraren maganar Guggo,domin duk halin da Aisha tashiga Akeela ce sila,domin dai Akeela 'yar madigo CE!nan yashiga basu labarin abinda ke faruwa tundaga zuwan Zuhra da suman da tayi har zuwan su dasu Daddy da sumar da Ammi tayi,gabadaya Galadima, Bodejo, Guggo laure salati suka sanya Daddy na tayasu,cikin kuka Guggo Laure tace"Karya kukeyi hasheemu wallahi sharri kukeyi Allah ya isa tsakanina daku da yardan Allah sai Allah yasakama Akeela, Allah ya isa"tana fada tana kuka haka yafita tabar gidan. Taga² Galadima yayi zai fadi,cikin sauri suka taresa,fadi yake nine Laure yau takema 'yayana Allah ya isa? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,gabadaya gida ya hargitse kamasa sukayi suka kaishi bedrooms dinsa suna masa fifita, Galadima kuwa sai maimaita magana guda daya yakeyi abinka da tsufa yafara riska,shekaru 82 ba wasa ba ai"Nine Laure kema yarana Allah ya isa?a ranar dai sai da jinin Galadima yahau, Sauban ma ammishi waya kan gobe zai iso, Abba ma haka. Gabadaya ahalin kwanan rashin dadi da natsuwa sukayi domin tsiya sosai Guggo Laure takeyi Alhaji mansir na tayata, Baba sani kuwa cewa yayi abari ayi bincike,nanfa Guggo Laure da Alhaji mansir suka dirar masa wai shima ya yarda da sharrin da akama Akeela. Da daddare kuwa Akeela ba gida ta kwana ba,can tatafi suka sake cin Karen su babu babbaka,domin gani takeyi yanda tahada wannan maganar komai zaizo da sauki. Washegari kuwa da wajen 1:30 babu abinda kakeji na tashi sai hayaniya gidan Galadima family wanda har yaja koke koke domin kuwa Guggo Laure ta dage kan wallahi muddin aka raba auren Akeela da Sauban itama ta rabu da Galadima bata bashi babu zuri'ar sa rabuwa kuma ta har abada,a'inda Bodejo itama ta rantse kan wallahi sai Sauban ya saki Akeela don bazasu zauna da annoba,Sauban idanuwan nan sunyi jajawur nan yashiga recalling din abubuwa da dama,sannan tabbas shima yasha zargin sa da haka,nan yashiga bayanin komai shima,sannan Ammi tasamu shedar tunda akayi bikin Sauban bata shiga sashin ba sai jiya,sosai rayuka suka 6aci hankula suka tashi,ita kuwa shedaniyar batasan meke wakana tana can suna madigon su,duk da a gefe guda na zuciyan ta tanajin bazata iya rabuwa da Sauban ba.Gida kuwa sai kuka da kuka domin Guggo Laure tace"anuna musu sheda na kama Akeela da akayi tana madigo"Bodejo tace"sheda ai Allah ne shaida kuma insha Allah sai Allah yatoni asirinta mudaije zuwa. Wata kalma da ya girgiza su ne yasa mutane biyu zuciyoyin su rawa lokaci guda wato Galadima da Guggo Laure domin kuwa a take anan Sauban yace"ni Muhammad Taleeb Muhammad nasaki matata Akeela saki daya,biyu.....baikarisa na ukun ba yaji wani gigitaccen mari,da hanzari yadago lokaci daya, Daddy ne ya maresa"Sauban ka gwammace ka yanke zumuncin 'yan uwa biyu?Ashe baka da hankai? Sauban yace"Daddy ko na cigaba da zama da Akeela babu aure domin zargin ta zan fara,kuma aure da zargi babu aure. Ihu Guggo Laure tasa kamar mahaukaciya tana fadar"Allah ya isa tsakanina da ahalinki Yaya Muhammadu bani

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});