Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,272 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba to tabbas da akwai gagarumar matsala kuwa. Murmushi ne ko wanne akan fuskansa, Galadima cike da jin dadi yace"Allah yayi miki albarka fadimatu. Da Ameen su Daddy duk suka amsa. Bodejo ta qanqantar da idanuwa tace"wallahi an shiga hakkina ba kadan ba saboda ni tuni Sauban na zaba masa matar aure,amma babu komai in matan shi ne nan gaba Allah yabashi. Su Daddy suka sake amsawa da Ameen,duk da kuwa kowa yaso jin Karin bayani a wajen bodejo Amma gudun maido da hannun agogo baya yasa sai suka haqura. Anan aka tsaida magana inda Galadima yayanke shawarar da kanshi zaije yawa kanwar sa wannan albishir din. Tabe baki bodejo tayi tare da mikewa ta gyara zaninta tawuce ko sallama batayi musu ba. Abba ne yasauke ajiyar zuciya yace"Yaya taya zamu sanar da Sauban wannan batun?kaga yaron nan yanuna bayason wannan abin tunfarko. Daddy yace"yakuwa zaiyi auren biyayya shine abinda zaiyi ko kuwa Sadeeq? Abbie Wanda koda yaushe fuskansa baya rabo da murmushi yace"Allah yasa hakan shine abinda yafi alkhairi. Sunji dadin addu'ansa. Nan suka kammala tattaunawan su sannan suka miqe. Zuhra ce kwance akan kujeran Ammi ta lumshe idanuwanta saboda tsananin ciwon da kanta ke mata,sosai jikinta yadauki zafi alamar zazzabi nason saukar mata. Yaran gidan gabadaya suna wajen Ummie don Ummie macece meson yara sai dai tsakaninta da zuhra sai a hankali. Ammi ce tafito daga kitchen hannunta rike da wani plate tayo inda zuhra ke kwance,zama tayi a gefenta sannan tadauki kanta tadora akan cinyar zuhra. "Subhanallah zuhra ai ba ciwon kai kadaine ke damunki ba ga zazzabi nan a jikinki, tashi kisha wannan fruit salad din. Batare da tayi musu ba tamike,wani irin Sara mata kan yayi da qarfi,hannu takai tare da kama kan,jijiyoyin kan sun firfito. Sake rikicewa Ammi tayi domin sosai Allah yadora mata son zuhra tun sanda Ummie ta haifeta tare da wani burinta akan zuhran. Sanyayyan muryanta tabude a hankali,muryan inbanda rawa babu abinda yakeyi tace"Ammi ki Kama mun kaina inajin kamar zai fashe. Kama mata kan Ammi tayi tafara yimata addu'o'i a hankali wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyan zuciya Ammi ta sauke tare dajin wani tausayin zuhran a ranta. Samun gefen ta tayi ta zauna tana duban kofar parlo tare da amsa sallamar da akayi. Kareem ne yashigo fuskar sa dauke da murmushi dama shi mutum ne wanda baya rabo da murmushi. "Barka da gida Ammi,yafada tare da rissiniwa. Cike da fari'ah Ammi tace"A'ah Kareem har kadawo daga airport din? Kareem yace"Ea Ammi nadawo don sai da natsaya ma har jirginsu yatashi sannan nataho. "Allah sarki Allah YAKARA muku dankon zumuncin nan naku da kaunar juna Kareem anfa gode,angode sosai. Dariya Kareem yayi yace"Haba Ammi tsakani na da Sadauki ai babu haka, bari naje gida hajiya tanata kirana. Ammi tace"tohm Allah yayi albarka ka gaisheta,kace inanan zuwa,anfa gode. Fita yayi tare da satan kallon inda zuhra ke kwance,duk da yaso yaga fuskanta Amma Allah baibashi sa'a ba. Da daddare yaran gidan duk suna sashin bodejo harda zuhra. Bodejo tadubi zuhra tare da kyabe baki tace"waike yarinyar nan lafiyanki?tundazu kiketa yatsina ko bakijij dadi ne? Shiru zuhra tayi tare da sake lumshe idanuwanta. "Yarinyar nan haryanzu wannan shegen miskilancin naki yananan,nidai keda saudan bansan wanda yafi wani wajen miskilanci ba. Gabadaya yaran parlon suka sanya dariya,maimoon tace. "Bodejo bafa saudan ba, Yaya Sauban. Bodejo tace"Toh uwar feleke,ni ina ruwa na,haka na iya haka kuma zan fada. Murmushi Galadima yayi yace"zuhra zo nan kinji. Mikewa zuhra tayi a hankali kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki ta nufi inda Galadima yake ta zauna a gefensa tace"granny mezaka bani na dadi. Duban Laila Galadima yayi. "Zonan Laila,jeki kitchen din bodejo saman fridge dinta zakiga bakar leda ki daukomin. Zuhra batasan sanda wani murmushi ya subuce mata ba jin amfani hakar leda. Daga murya Galadima yayi yace"ki kuma zo da plate guda biyu.Da toh Laila ta amsa. Tuni yaran parlon suka fara murna. Laila batajima ba tafito hannunta da wani dan leda baqa medan girma,tare da plates uku babba guda da madaidaita biyu,akan babban plates din tadora ledan. Galadima yace"hajiya bodejo azo akasa abawa kowa nashi. Bodejo takama baki tace"wa? Ai idan zuhra na waje bodejo bata tasiri ga tagaban goshi? Murmushi Galadima yayi yace"Toh ko nihal ta raba ne?nihal zoki raba mana. Tasowa nihal tayi aiko ta raba kashi uku kamar yanda Galadima yace tayi,shida bodejo kashi daya itada da Laila da zuhra Kashi daya sai su maimoon ma kashi daya. "Allah yasaka da alkhairi granny ubangiji yaqara budi, Allah yaqara daukaka GALADIMA FAMILY,zuhra tayi addu'an cikin muryanta mai sanyi. Da Ameen su Laila suka amsa. Sosai Galadima da bodejo sukaji dadin addu'an na zuhra,wanda a kullum suna yabawa da hankalinta. _SU WAYE GALADIMA FAMILY?_ Cikakken sunansa Muhammad Taleeb Muhammad haifaffen garin MAIDUGRI sai dai mahaifiyar sa ce 'yar nan wacce take shuwaarab,shi kuwa mahaifinsa buzaye ne irin masu tashin nan,adalilin haka Allah yakawo mahaifinsa da mahaifiyar sa garin MAIDUGRI inda wata rana suna kwance da daddare wata takama Wanda ba'asan daga inda wutar yafito ba. Mutane suka fara kawo dauki,a lokacin Muhammad nada shekara a duniya,atake anan Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa garin ganin ya cece matansa da dansa maisuna Muhammad,don sosai yayi wani irin mummunan kuna,mahaifiyar Muhammad kuwa itama kokari take takare Muhammad tare da abinda ke cikinta. Asibiti aka kai mahaifiyar Muhammad,inda likitoci suka dukufa akanta,koda suka duba sai sukaga cikinta yana watan haihuwa ne babu bata lokaci suka yanke hukuncin ciro abinda ke cikinta,suna shirye²n yimata aikin ne Allah yadau rayuwanta,ganin haka yasa suka hanzarta yimata aikin. Aiko suka Ciro yarinya kyakkyawa mace, Muhammad kuwa sai kuka yakeyi,nan suka tattara akayi abubuwan da za'ayi aka amsa gawar Muhammad. A lokacin hakimin garin shine kakan bodejo don haka shine yayi komai,suka koma suka sallaci gawa biyu,babu bata lokaci hakimi da sauran dattawan anguwa suka yanke hukuncin baiwa hakimi su Muhammad,inda shi kuma hakimi yadamqasu a hannun danshi tilo namiji Harun mahaifin bodejo. A lokacin bodejo nada shekara bakwai mahaifiyar ta daga kanta bata sake haihuwa ba Allah yamata rasuwa,a lokacin matan baban bodejo na aure da kanin bodejo yakub sai aka bata jaririyar ta hadasu tana shayar dasu. Kamar yanda al'ada yazo ranar suna aka radama yarinya suna Lauratu inda mutane ke kiranta da Laure,sosai mahaifin bodejo da kakanta suka bawa su Muhammad gata,hakimi yasa aka tattaro masa raquman su Muhammad guda goma Sha biyar yabawa wani abokinsa dake cikin gari ajiyansu ana cigaba da kula dasu. A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har akasa Muhammad a makaranta inda shakuwa mai karfi tashiga tsakaninshi da bodejo,a gefe guda kuma hakimi na cigaba da kula mishi da dukiyanshi shida mahaifin bodejo. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami🖊️yafi takobi🗡️ 16/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 07 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____A lokacin da Muhammad yagama secondry school lokacin Allah yadauki rayuwan hakimi,inda anan harun mahaifin bodejo yatura Muhammad cikin garin MAIDUGRI gidan aminin mahaifinsa inda gadon su Muhammad yake anan yaciga ba da karatunsa na gaba da sakandiri,a gefe guda kuma shakuwa sosai tasake dinkewa tsakanin bodejo da Muhammad lokacin tagama aji uku na

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});