Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 48

Chapter 48

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,314 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zoba?maida duban sa yayi ga zuhra yace"kin kyauta tunda kece keda iko da kanki? yanzu har kinyi girman da zaki kira saurayi yazo zance gidan ku batare da kingama makaranta ba?batare da annemi izinin iyayen ki ba?shiru zuhra tayi jikinta babu inda baya rawa. Cikin daka tsawa dayasa Ammi dasu Laila fitowa yace"Ba magana nake miki ba kike girgiza min kai kamar kadangaruwa? Cikin muryan kuka zuhra tace"don Allah Baba kuyahakuri"girgiza kai kawai Daddy yayi sannan yayi gaba, Baba Hasheem yace"kin kyauta domin duk abinda yafaru kece sila,kenan a school dinma samari kike kulawa ba karatu kikeyi ba kenan?da sauri zuhra tadago tana girgiza kanta hawaye na mata zarya. Batare da yasake magana ba ya wuce, Sauban ma bin bayansa yayi,zuhra kuwa atake anan ta duke tana me salkin wani irin kuka me ban tausayi domin bata kawo zuwan ranar nan kusa,shikan shi Shuraim hankalinsa ba karamin tashi yayi ba,duban ta yayi cike da tausayawa, Ammi ce takaraso wajen tana me kama zuhra suka nufi cikin apartment dinta,jikinsa yayi bala'in sanyi,a gefe daya kuma ga tausayin kawunan su,dama a waje yake parking motar shi,direct gate ya nufa ya fice daga gidan gabadaya. Haka dai takara sa yinin ranar tayi shi sukuku babu walwala ga tarin fargaba da ya hadu ya mata yawa don kuwa tabbas tanaji a jikinta shirun Daddy ba alheri bane. Bayan sallan isha'i zsune take a dinning sam abincin takasa ci tsakura wa kawai takeyi,sam bakinta babu apatite hakanan tarasa abinda ke mata dadi,Laila ce tashigo cikin sanyin jiki ta dubeta"Sis kitashi kije Daddy nakira wai suna parlour Galadima"jitayi kirjinta ya tsananta bugawa fargaban ta yakaru,ko kaffara bazatayi ba tabbas akanta ne za'ayi wannan zaman,mikewa tayi cikin sanyin jiki tana duban Laila idon ta na cikowa da ruwan hawaye,dafa kafadanta kawai Laila tayi tana mejin tausayin 'yar uwan tata. Cikin sanyin jiki ta yafa gyalin Egyptian gown din dake jikinta tanufi apartment din Bodejo,da sallama tashiga parlour,zaune suke Galadima, Bodejo, Daddy, Baba Hasheem, Ammi, Ummie, Mom sai kuma Sauban dake zaune gefen kafar Galadima ahankali takarisu parlour cikin sanyin jiki,wani irin kallo Ummie ke aika mata dashi don ita batasan meyafaru ba sai a bakin Mom takeji. Zama tayi akan hadadden carpet din wanda ya qawata parlour sosai,gaishesu tashiga yi cikin jam'i,cike da tsokana Galadima yace"feel free mana amaryas,sai kame² kikeyi ba?ai asirin ki ya tonu wato nema kike kimin Kishiya saboda kinga natsufa ko?to komin abinki ba'a canzawa tuwo suna"yakarasa maganar yana gyara zaman shade din fuskan sa, Bodejo tace"Hmmm ai kayi kagama ni me kishi dani sai ya shirya"duk dariya aka Sanya banda Sauban daketa daddana wayar,shiru ne ya gifta zuwa can Daddy yayi gyaran murya yana duban zuhra"mamana! Muryan zuhra na rawa tace"na'am Daddy, Daddy yace"kinsan zaman nan akan wa mukayi shi ba sai anyi dogon jawabi ba ko?daga kai zuhra tayi alamun Ea. Daddy yace"Masha Allah,tunda muke a gidannan tun kama daga kan Addojinki su Maryam babu wacce tataba kula wani saurayi kafin aure hatta su Mashahuda batare da anzo annemi izinin mu ba,kece ta farko da kika fara karya dokar gidan nan harki dinga kula wani saurayi ku kulla soyayya batare da duk munsani ba,bazan boye miki ba raina yayi mummunan 6aci domin kuwa hakan babban zunubi ne agareki. Shiru parlour ya dauka zuwa can ya cigaba"nema kike ki maida mu mutanen banza?a'ina har kika samu karfin gwiwwan haka?waye shi a'ina kuka hadu?jikin zuhra yasake sanyi muryan ta na rawa ta shiga basu labarin haduwar ta dashi tundaga farko har karshe,cikin muryan kuka tace"wallahi Daddy ba karya nakeyi ba ka tambayi Aunty Mashahuda da Aunty Safeena,domin dan uwan Ouncle Asheer ne,sosai tabawa su Daddy tausayi amma sukaki nuna mata hakan,cigaba da magana tayi"sannan yaso ya sameku nice na hanasa nace sai na gama school amma don Allah kuyahakuri bazan kara ba. "Hmmm abinda yasa muke hanaku kula da wasu mazan ba komai bane face gudun matsala,domin ke akanki hakan ne ke shirin faruwa dake domin akwai aure akanki"ai a gigice Ummie, Mom,zuhra ke duban Daddy, Ammi kuwa mamaki ne ya kashe ta,jikin ta babu inda baya rawa tamike tanaso tayi magana takasa saboda tashin hankalin da tashiga, Daddy ya cigaba da magana"Marigayi Sadeeq yabar mana wasiyyar idan yarasu yanaso ranar addu'an ukun shi a hada da auren ku,domin yace tun sanda aka haifeki da wannan kudurin a ransa,ranar da Sadeeq ya cika kwana uku da rasuwa a ranar aka daura auren ki da yayan ki Sauban!zuhra jitayi kanta na juya mata lokaci daya taji wata jiri na dibanta,wannan karan Mom ce ta zabura ta mike tsaye tana kokarin magana sukaji karar fadin mutum timmm!!! Gabadaya juyawa sukayi wajen inda sukaji karar faduwan,zuhra ce ta yanke jiki ta fadi a take anan, da wani azababben gudu Sauban yanufe ta yana me jawo ta ya rungume,duk cikan 'yan parlour zagayeta sukayi banda Galadima da Ummie da suke zaune, Ummie wani hawayen farin ciki ne ya shiga sirnano mata,tabbas abinda tadinga addu'an samu kenan tundaga sanda tadawo hayyacinta take fatan Sauban da zuhra su fahimci juna,sai dai rashin jituwar su ba karamin daga mata hankali yakeyi ba. Da sauri Ammi tabude fridge din dake nan parlour,bottle water medan sanyi ta dauko,balle murfin tayi tashiga tsiyaya ma Sauban a hannu,shikuma yana shafa mata haka sukayi har kusan sau biyu ana ukun ne taja ajiyar zuciya tana me sakin wani irin kuka,duk ajiyan zuciya suka sauke sannan suma suka koma suka zazzauna"zaunar da ita Sauban"cewar Baba Hasheem,zaunar da ita yayi sannan yana dan matsawa gefe cikin kamewa,rarrafawa tayi tana dafe kafar Daddy cikin muryan kuka gwanin ban tausayi tace"please...please Daddy don Allah kuyahakuri kada kubarni dashi bazan iya rayuwar aure da.....maganar ce tatsaya cak a dalilin marin da Ummie ta sauke mata,tana huci takai hannu zata sake mata wani marin cikin sauri Ammi ta tare,6acin rai kwance a fuskar ta tanuna ta"zuhra!maganar mahaifin ki kike nema ki butulce?yabar wasiyya kice ba haka ba?mekika sani ke?harkin san wani so ne ke?wallahi nasake jin kalmar nan abakinki saina miki bugun tsiya,mtsewww useless"tana kare fadan hakan tafice daga parlour,bakajin komai sai shasshekan kukan ta,shikan shi Sauban din sai yaji wani tausayin ta ya kamashi gabadaya. Cikin fusata Mom tamike tana duban kowa tace"tsakani da Allah ana rashin adalci a cikin family dinnan,ni nazata Aseef ne za'a bawa zuhra? maganar gaskiya nida 'yayana ba'a Mana adalci,domin kuwa ai wannan tsantsar rashin adalci ne,sai kace duk family din Sauban ne kadai da'? Anbashi Akeela ga kuma zuhra gaskiya....cikin bacin rai baban Hasheem yace"Rabi!! Kishiga hankalinki dani,waye sa'anki anan?itama Mom cikin bacin rai tace"ni iya gaskiya ta nake fada wallahi"tana gama fadan hakan tafice daga parlour tana 'yan kananun surutai. Daddy yace"koma mene duk abinda zakuyi kuyi babu me kwancen auren nan sai Allah,kutashi ku wuce"yayi maganar yana duban Sauban,cikin sauri zuhra tamike tariga fita,duk da kallon tausayawa suka bita,tafe take kawai tana hada hanya,jitayi tayi tuntu6e da wani interlock na gefen hanyar,gaba tayi zata tuntsira, Sauban dage bayanta cikin sauri yakarisa ya tarota tafada jikinsa, dai-dai kunnenta yace"Kidai kula Saboda wata can banziyar soyayyan ki kina neman kashe kanki a banza,to nina dakika ganni ba sonki nake ba domin kuwa amaryan matata tafimin ke"yana kare fadan hakan yasake ta tare da wucewa yabarta nan tsaye,wani kuka ne taji ya kufce mata tare

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});