Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,324 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Bayan komawar su kaitsaye gidan Adda Zainab suka isa sannan duk 'yan sanda ne a bakin gate din gidan,cikin gidan,kofan parloun da cikin palour,dama or ready family din Alhaji iliyasu sun hadu,su Ummie kawai ake jira,aiko nan police din ya dubi Adda Zainab"Hajiya ke muke sauraro,nan Adda Zainab ta cigaba da bada labarin sannan tace"babban sake dinkewar alaqar mu da Hajiya Aliya shine sanadin bilkisou,kowa kallon Ummie yayi nan ta cigaba tana duban Ummie"tunda na mallake hankalina nafara jin tsanar bilkisou a dalilin komai da tafini yasa nakejin tsanan ta,tsanan ta besake nunkuwa ba sai da tasamu miji daga ahalin da suka fi nawa sannan nasake jin wata iriyar tsanar ta,alhalin mahaifiyar ta bata ta6a nuna cewa ba itace ta haifeni ba,hasalima ta fifitani akan bilkisou,daya ke bilkisou ta rigani aure a lokacin hankalina yatashi wanda har Amma taso a fasa bikin Bilkisou abari nima na samu miji ko kuma Sadeeq ya aure ni ya hakura da bilkisou, Allah yajikan baban mu shine ya hana hakan a lokacin naji matsanancin haushin sa,ana haka ne na hadu da Hajiya Aliya inda ta hadani da wani boka da yake nijar,salati aka Sanya gabadaya palourn, Ummie kuwa kuka kawai takeyi. Ta cigaba da cewa"Nice nasa akayi miki farraqu da Zuhra nayi amfani da kyallen jininki na kaiwa boka akayi asiri,tun daga lokacin kika tsane Zuhra,nan fa Adda Zainab tadinga bada labarin irin abinda suka dinga kullawa da hajiya Aliya har asirin da tasake yi mata da wancan ya karye,har zuwa sanda hajiya Aliya ta aure Alhaji iliyasu,da irin rigimar da sukeyi sannan tayi shiru tana jan shasshekan kuka, Ummie ma kuka takeyi tare dasu Amma,cikin kuka Amma tace"Zainab dama kece duk kike musu wannan farraqun?mahaifinku ya mutu da fushin bilkisou akan haka, fisabilillah kin kyauta kenan?cikin tu ajjabi hajiya kareema tace"lallai Zainab shedancin ki yakai inda yakai,yo wanda yayi wannan aikin ai kisa bazai mishi wahala ba,domn tuni aka cire miki imaninki"Adda Zainab cikin dasasshiyar muryan ta tana kuka tace"wallahi bani ce na kashe su Alhaji ba, wallahi"Ammar cikin muryan kuka yace"idan bake bace wanene Mom?please wanene?yayi maganar cikin muryan tsawa,islaha da kuka yaci karfin ta tace"why?why Mom?kinja mana abin fade Mom innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ya Allah,babu 6ata lokaci aka sanya ma Adda zainab ankwa a hannunta wata mace,kuka sosai takeyi haka yaranta dasu Amma, Ummie ta dubi police din tace"Please yalla6ai yanzu ina zaku kaita?dan sandan yace"hajiya kaitsaye daganan state CID zamu wuce da ita domin gudanar da bincike yanda ya kamata,munyi muku alqawari muddin babu saka hannunta zamu saketa,idan dasa hannunta kuma zamu turata court a yanke mata hukunci"yana gama fadar haka aka tisa keyan Adda Zainab akayi waje da ita,kowa kaganshi bashi da kwanciyar hankali. ******** Yau a bedroom dinta ta kwana domin kuwa tayi alqawari bata sake kwana daki daya da Sauban,hakanne ma yasa tun kafin yadawo ta koma dayan palour kasa tare da shigewa daya daga cikin bedroom din ta kwana,hakan kuwa sosai ya sosa ma Sauban rai tare da yanke hukuncin yau da la'asar zaibi flight,ta online yasai ticket da komai nasa ya gama batare da tasani ba,da safe tana tashi ta shirya musu lafiyayyen breakfast,babu abinda ke tashi sai na room freshener da turaren rushi,gefe guda kuma ga kamshin girki,tasan Sauban ma'abocin son macaroni ne,dalilin hakan yasa tahada masa lafiyayyen macaronin sa da yaji dakakken nama yayi kyau da dadi,sannan ta dama masa kunun gyada, Ammi ma ta aiko da breakfast din kosai da custard sai wainan kwai,shiryawa tayi cikin riga straight gown,wanda ya fito mata da cikakken surar ta ko ina yacika Masha Allah, tayi kyau sosai,abinka da atamfa me dan duhu sai tayi kyau kwarai,daurin Aisha buhari ta murza mai kyau,kafarta sanye da high heel shoe brown, fitowan ta kenan daga kitchen hannunta dauke da plates taji alamun tafiyan sa,turaren sa me kamshi Arabian Oud ya buge hancin ta,dan lumshe ido tayi tanajin faduwar gaba,daurewa tayi ta cigaba da shirya dinning din. Karisowa yayi yaja kujera ya zauna,sanye yake da wata yadi me kyau tare da maiko brown colour,daka ganta kasan lallai anyi fitan nera wajen siyan ta,kansa murzazziyan kube ce,wacce kudinta zasukai dubu 35 face dinsa babu wani walwala kamar koda yaushe, Zuhra kuwa gabanta ne ya cigaba da faduwa,a hankali tayi karfin halin furta"Ina kwana Yaya"kura mata ido yayi babu ko kiftawa,almost 5 minutes sannan ya girgiza kai kawai,ajiyan zuciya Zuhra ta sauke kirjinta na cigaba da bugawa daurewa tayi tace"Yaya meza'a zuba maka?hannunsa dauke da wayar sa yana latsawa batare da yadago ba yace"meda menene akwai?Zuhra tace"akwai jallop din macaroni with kunun gyada nama nd custard wih kosai,sai wainan kwai.Dagowa Sauban yayi yana zuba idanuwan sa akan warmers din dake kan dinning din,duk da a rufe suke yace"kisamun macaroni nd kunun gyada kadan inci tukuna"yanada tabbacin itace tayi wannan, cikin nutsuwan ta take serving dinta,gabadaya ya tsareta da idanuwan sa jinta kawai take a takure, shikuwa Sauban baiki yaji Zuhra akan cinyar sa ba, wani irin shaukin son ta kawai yakeji,batare da ya ankare ba yaji maganar ta"bismillah Yaya"dan sake hade face yayi yana daukan spoon din tare da duban plate din,lumshe ido yayi yanajin wani sanyi da dadi a ransa don dakakken mama yaji a cikin macaronin Masha Allah,hadiye miyau yayi, bismillah yayi yafara cin abincin cikin mutsuwa,jiyayi wani dadi ya ratsa masa har kwakwalwan kansa,sosai yake daurewa gudun kada yayi santi,ganin ta zauna tatasa kosai da yaji tanaci yasa ya dubeta"bazaki kiyayi kanki da cin yaji haka ba?wallahi idan kikazo kina min complain din basir da ulcer ko?sai kawai yayi shiru ya cigaba da cin abincin, Zuhra kuwa dagowa tayi cikin marairaice face,tare da wata shagwa6a66iyan murya wanda ita kanta bata ta6a sanin tana da ita ba tace"kai Yaya kosai fa idan babu yaji babu dadi"wani tsam!yaji a dalilin yanda tayi maganar,batare da yayi magana ba yadaga mata kai kawai,atake anan ya cinye plate din,gyaran murya yayi mata, dagowa tayi ta kallesa,da ido yayi mata alamun akara,kara mishi tayi ba da yawa ba,itako kosan biyar taci ta basshi cuz takasa sakin jiki taci yana wajen,shiko ko a jikinsa sakin jiki yayi yaci abincin sa yayi katt,yana gamawa yadau kunun gyadan sa yafara sipping,lumshe ido yayi domin har ga Allah yaji dadin kudun sosai,be yadda yabiye ma dadin ba yadaka,don a haka ma jin cikinsa yake ya cika don dama shi ba ma'abocin cin abinci bane,tissue yadauka yafara goge bakin sa,ji sukayi anwani daka kofan palour. Da sauri suka mike, Akeela ce tashigo jikinta sanye da wata doguwar riga fitted sai dai ko kadan batayi mata kyau,sai taunar chwengum takeyi tana kare ma palour kallo,ganin canja wasu abubuwa da akayi tare da kara gyara sa,ta6e mouth tayi tana jan tsaki,nan tashiga takowa a gaban Sauban ta tsaya idanuwan ta cike tafff da hawaye tafara magana"Kaine na mijin dana fara so a rayuwa ta wanda akansa nasan menene so,amma munafukai sunyi nasarar rabani dakai a lokacin da muka kasance tare,inaso kasani wallahi bazan ta6a rabuwa dakai ba koda kuwa zanyi yawo tsirara ne sai na farauto soyayyar ka,sai nadawo cikin gidan nan matsayin mata"takarisa maganar hawayen na zubowa,duban ta ta maida ga Zuhra tana nuna ta,ke kuma inaso na Miki wata zazzafan gargani duk sanda kikasan mijina a matsayin miji wallahi babu ke babu kwanciyar hankali,banza kawai jak.....ai bata karisa

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});