Chapter 5
Chapter 5
sallar harma wasu masallatan sun tayar. Babu bata lokaci itama tazo tafara gabatar da sallan ta. Bayan sallar isha'i Sauban yasamu su Daddy a farfajiyar gidan don a ka'ida nan suke dawowa su cigaba da hira abinsu cike da qaunar juna,sallama yayi cike da mutumci irin na hadadden yaron tare da kamewa yaduqa yafara gaishesu. Suma cike da jin dadi suke amsawa saboda natsuwar Sauban da Kuma kamewarsa,wanda wannan dalilin ne yasa yakeda jama'a da dama a cikin family din nasu. Abba ya dubeshi yace"Sauban ya akayi ne?dan murmushi yayi tare da sake sunkuyar dakai yace"Abba dama sako ne dazu aka turomin daga can maleyshia kan suna son muje za'ayi mana interview mu goma Sha shida 'yan Nigeria,nanda 4days shine nace bari nazo nasanar daku. Ko wannensu cike da farin ciki Daddy yace"Masha Allah! Abbiel kuwa murna sosai kwance akan fuskar sa yace"Sadauki Masha Allah, congrats my son! na tayaka murna sosai,yayi maganar yana masa musabaha. Inda sabo Sauban yasaba da halin Abbie don tun yana yaro yake tare dashi,murna sosai sukayi. Daddy yace"ka fadama su Ammin naka? "A'ah Abba yanzu nakeso nashiga wajenta na fada mata sannan na fadama mom itama. Sake mishi fatan alkhairi sukayi,miqewa yayi cike da qasaita duk da cewa hakan halittarsa ce domin Sauban tsayayyen namiji ne a cike wanda dai² da maza ma 'yan uwansa yana musu kwarjini balle kuma mata. "Yanzu Sauban kasar maleyshia zakaje yin aikin?Koda Allah yasa hakan shine yafi zama alkhairi nidai abinda nakeso dakai kada ka kawomin wata 'yar qasan kacemin aurenta zakayi don magana ta gaskiya ba lamunce maka zanyi ba,don ga 'yan uwanka nan cike da dangi. Dan guntun murmushi yayi yace"sweetheart ko aikin ma ba'a samu ba kinfara kawo korafi? Ammi ta sake tsuke fuska tace"ai gaskiya ce na fada saboda nasanku ku maza shiyasa tun yanzu ma nake gaggawan taka maka birki kada naji ko nagani Koda kuwa andace ne. "Shikenan sweetheart hakama sam bazai faru ba gobe nakeso naje gidan Aunty falmata. Ammi tace"Allah yakaimu!da ameen Sauban ya amsa nan suka cigaba da hirarsu. Washegari da safe wajejen goma saura sai ga Guggo Laure itada Akeela,tsayawa nayi naqare mata kallo tasss,kyakkyawa ce sai dai ko kusa bata kamo kafar yaran gidan ba duk da cewa a ciki akwai qalilan da tafi kyau,sanye take da lutfaya baki mai ratsin jan flowers sai kafanta sanye da halfcover ja,hannunta riqe da handbag shima ja fara ce tass wanda a farin ma akedan karawa da man bleaching daga gani zatayi sa'a dasu mashahuda. Baba mansir mahaifin Akeela shine Guggo Laure tasa ya kawo su don baisamu shigowa gidan bane saboda ana jiransa ujila. Kaitsaye bangaren su bodejo suka nufa, Akeela kuwa tamkar bazata take kasa ba,Koda suka shiga sun cidda bodejo da Galadima,bodejo tana hada masa brabusko da miyar kuka Wanda yaji nama zallan tsoka daga bangaren Daddy aka kawo. "Assalamu alaikum!ga bakin sassafe fa. Guggo Laure tana fada fuskanta dauke da tsananin fari'ah saboda ganin motocin yaran gidan da alamu ma basu fitaba hakan ne yasata sake fari'arta. Galadima yace"Laure!kece a gidan?lallai jiki yayi sauqi sosai tunda gashi kin iya fitowa yayi maganar fuskansa kadaran kadahan. A inda Akeela take tsaye ta gaishesu ko rissinawa babu qiqam ta gaidasu. Cike da mamaki su bodejo ke duban ta, Galadima yace"ke haka akace miki mata na gaida mijinta?duqawa akeyi har qasa bawai atsaya a tsaye kerere ba kinji? Akeela ta wayance ta hanyar cewa"toh ai saboda bana auren tsoho irinka yasa na gaisheka a haka saboda kada tsohuwar matanka ta huramin hanci. Bodejo kuwa Sarai ta ganeta sai cewa tayi"to ai tunda kikama wannan angon haka babu irin angon da bazakiyi wa ba. Guggo Laure tace"musake gaisawa kundawo lafiya?ya gajiya Yaya bodejo? Bodejo tace"ai gajiya tabi jiki Laure Kuma marasa lafiya kun fito balle kumamu? Guggo Laure tace"wallahi fah kedai Bari jiya najuya yafi sau nawa? narasa gabadaya abinda kemun dadi a gidan duniya naqosa gari ya waye nazo saboda nace da zafi zafi ake bugun karfe shiyasa,tadubi Galadima tace"kada dai agaji dani akan kokari na nason aikata alkhairi. "Maganace dai akan yaran nan Akeela da Sauban shiyasa ma nace Akeelar tashirya tazo muje ayi komai a gabanta. "Shima kuma Sauban din ayi komai a gabansa. Cike da mamaki duk suke duban ta. Galadima kuwa abin duniya ne ma ya isheshi yayi dan murmushi irin nasu na manya yace"Laure kenan kekam akwaiki da wutan ciki, gashi yaran ba dukansu ne suke nan ba don shi sadeeq yau ya koma kaduna,shikuma Hasheem yaje ta'aziyyar amininshi da yarasu. Guggo Laure tace"toh nidai Yaya hakanan za'ayi hakuri ayi maganar nan yau a wuce wajen. "Yarinyar nan tana tsananin son Sauban,duk cikin jikoki na babu mafi soyuwa agareni kamar Akeela. Galadima yace"toh shikenan bari nakira taleeb din,hannunsa yakai gefen lumtsememen leaderseat dinda yake zauna yadakko wayarsa kirar sumsung yafara nemo number,baiwani dau lokaci ba yakira har takatse ba'a daga ba,ko kafin yasake danna kiran,Kira yashigo wayan nasa. Dauka yayi tare da sallama,daga can bangaren Daddy yagaishe shi,amsawa yayi kaitsaye yace"inason ganinku kai da Aliyu idan anyi sallar azahar,daga can bangaren aka amsa da toh insha Allah,sannan Galadima yakatse wayan. Guggo Laure kuwa murna takeyi kamar yakasheta,dakin da take sauka wanda aka mata nan tanufa harzata shiga sai Kuma tajuyo tace"ke Akeela zo muje mugaisa da matan gidan tukuna koh? Akeela kuwa farin ciki takeyi kamar anmata kyautan hajji,aranta kuwa fadi take itace zata mallaki Sauban jinin GALADIMA FAMILY?tabbas tayi sa'a,don Sauban namiji ne wanda da dama mata ke bibiyan sa,don ko a yanar gizo maganar sa mata keyi namiji ne mai tsadan gaske. Kai tsaye apartment and Ammi Guggo Laure tashiga,sallama tayi itama Akeela tayi cike da kissa. Su mashahuda ne a farlon,hada idon da muneefa zatayi aiko tamike da gudu tanufi Akeela tace"Kai lallai ma Akeela yau kece a gidannan haka? Akeela ta watsa idanuwa tace"aiko gani ai muneefa bakida kirki ko Guggo bakizuwa gaishewa. Mashahuda ta dubi Guggo cike da mutumtawa ta gaisheta,inda kallo daya tama Akeela ta watsar don sam ita Akeela bata burgers barin yanda take ganin tanasa pic dinta a Instagram na shirme. Muneefa tace"Tabb yaushe zaki ganmu so kike ya Sauban ya babballamu?dariya sukayi. Kujera Guggo Laure tazauna, Akeela da muneefa kuwa daki suka shige inda mashahuda tashiga kitchen don kiran Ammi,Ammi bata zama duk da masu aiki suke aiki Amma girkin mijinta ita takeyi tunda yanada suger,masu aiki kuma suyi na gida gabadaya ko da ita bata dauki wata mai aiki tayiwa mijinta girki ba. Mashahuda bajima ba tafito kitchen hannunta dauke da tray inda ruwa kekai da lemo. Ammi ce tafito fuskanta dauke da murmushi tace"Guggo ce a gidan? Guggo ta amsa fuskar ta dai kadaran kadahan tace"yauwa sannu Aisha nice. Ammi tace"inayini Guggo,kunzo lafiya? Guggo Laure tace"lafiya lou,munsameku lafiya? Ammi tace"lafiya ALHAMDULILLAH ya karfin jiki?jiya zamuzo da Rabi sai mazan sukaci mubari suje mu mazo yau Ashe jikin ma yayi sauqi? Guggo tace"jiki Alhamdulillah sai dai tasowar na dole nayi saboda mahimmiyar maganar dake tafe dani. Ammi tace"Allah sarki sannu da zuwa. "Yawwa Aisha,inasu Yaya na muhammadu? Murmushi Ammi tayi tace"Sauban yana dakinsa anata shirye²n tafiya Malaysia. Guggo cike dason jin Karin bayani tace"mekuma zaije yi can? Mumushi ammi tayi tace"zaije interview ne idan da rabon yasamu aiki a wani company a can ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87