Chapter 33
Chapter 33
Yana magana cike da dattaku da ilimin addini. An gabatar musu da abinci,namomi,lemukan gora, fruits kaloli inda suka so kin ci amma Galadima ya nuna musu ba ahaka dole kowa yaci abincin Yana santi don dama gaskiya surikan Galadima gwanaye ne wajen girki musamman Ammi, Ummie kuwa ta kware wajen iya na kasashen waje saboda rayuwar da sukafi yinta acan,mommy da Mom ma ba baya don idan Ammi da Ummie basu waje to sudinfa on top ne. Sai wajen karfe shida suka fita tare da tsaraban kalolin snaks sunfa kala biyar anyi raping nasu a kwalaye sai katan-katan lemuka da ruwa ammafa babu tukwici don anyi ba'ayi bane,wannan ma don gidan masu kudi ne shiyasa,sosai sukaji dadi su shidda ne haka suka tafi suna yabon wadannan ahalin. BAYAN magrib su Daddy sukasa ma'aikatan gidan maida akwatunan babban farlon Bodejo, nanfa mommy dasu nihal suka takarkare suka dinga sakin guda,don kaya kuwa Masha Allah komai washabban washabban don akwatuna goma sha hudu ne gasunan aka kawo,nanfa aka shisshigo dana Mashahuda akwatuna sha shida,gida fa ya kacame don sai da Galadima yayi musu gyaran murya don duk Wanda kaga fuskanshi kasan yana cikin farin ciki. Mom ma tayi murna don bata taba arzikin su ma'aruf dinma har takai haka ba,nanfa ta sulale tafara kiran 'yan uwanta da abokan arziki tana sanar musu, Ammi ma taji dadi sai dai damuwa karara ya bayyana kan fuskanta bayan mommy tamata bayanin abinda Sauban yace akan maganar lefensa. "Gaskiya yaron nan be kyauta ba memakon yayi komai nashi cikin kamata gaskiya sai na batama Sauban rai, Ummie ne ta dakatar da ita. "Haba Ammi kinaji fa anmiki Karin bayani yace yahada nasa bayason almubazzaranci ne shiyasa,don Allah ki kwantar da halinki ninasan yaro na wallahi ba daga baya ba", Mommy tace"Aifa kara tuna mata Ummie. *BAYAN KWANA BIYU* Akeela ce kwance akan gadon ta tana bacci, vibration din wayarta ne yatashe ta,dan tsaki taja kafin tayi picking cikin muryan bacci tace"Kai Suby barci fa nakeyi,kinsan da anshiga next week ba isasshen baccin za'ayi ba"daga can bangaren Suby tace"ke dalla can ba wannan ba ki shiga account din Rammat,kiga yanda tayi posting videos din lefen kannen mijinki,mahaukatan kayan lefe gashinan IG ta dauka. Zabura Akeela tayi ta tashi zaune cikin sauri tace"suwa kenan? "Hmm kannen mijinki da za'ayi bikin ku rada day.....ai Suby bata karisa magana ba Akeela ta datse wayar. Kaitsaye Instagram tahau,Nan ta watsa fiki-fikin idanuwan ta kan wayar,da sauri tamike tare da kama mouth"Ewwee!ai da gudu tafita bedroom dinta"Mom! Mom!! Tashiga kwalama mamanta Kira,da sauri tafito daga kitchen,"Akeela wane irin Kira ne haka? "Mom kallah,tayi maganar tana mika mata wayar,ansa tayi. Wannan lefen na waye haka?tayi mgnr ta diddilo idanuwa. "Hhhhhhhh! GALADIMA FAMILY Kenan ana fada miki, kayan lefen kannen bby Sauban ne. "Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Wai wai ko wacce gidan manya zata shiga kenan? "Ea daya zata aure Dan gidan maishanu family,dayan kuma dan Abbie daya rasu zata aura. "Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Allah yasanya alkhairi ya kade fitina,ubangiji ya basu zaman lafiya. "Mom saura nawa,amma ainima yaka mata ace ankawo nawa yanzu,tayi maganar tana bata fuska . Harara ta wugamata tare da shogewa kitchen din,da sauri itama Akeela tanufi kofan fita,kaitsaye sashin Guggo Laure ta nufa,itama nuna mata videon tayi,ai bata gama gani ba tafara sallallami"duk ankawo nasu amma ke basu kawo naki ba?to me mutanen nan suke nufi danine?sannan akasa kirana a amsa kayan dani?wallahi sai yau nasake tabbatar da Yaya Bodejo bata sona,bata son jinina,lallai ko yanzu zanje gidan. Caraf Akeela tayi"wallahi dani zaki Guggo don inason ganin lefen nan azahirance, shikenan maza ki shirya muje. Aiko cikin farin ciki Akeela ta fita, Guggo Laure bata jima ba tashirya tafito tana mitan har yanzu Akeela bata fito ba?Nan mujaheed dandan Baba sani yashigo gidan da mashin dinshi kirar jincheng roba -roba. "Guggo fita zakiyi ne haka? "Ea wallahi mujaheed zanje gidan Yaya muhammadu ne nadawo nida Akeela, murmushi kwance saman fuskansa yace"Au da amarya zaku fita?ni mumma dade bamu hadu da Akeela ba Guggo. Yatsine baki Guggo Laure tayi tace"to kunyar wa mujaheed?ai kunyarka,kuna gida daya bazaka shiga kaduba ta ba? "Guggo kenan,ko nashiga wataran mom zatace bata tashi ba ko batanan,to Yaya zanyi? Mere Guggo Laure tayi da baki tare da cewa"kaga bari nashiga naga dalilin da yasa ja'irar yarinyar nan shanya ni,takarisa maganar tana shiga sashen,nan tafara juyo fadar Mom. "Waike Akeela sai yaushe zakiyi hankali? meyasa baki da kunya?wallahi kika fita gidan nan nidake ne,bubbuga kafafuwa Akeela tafara. "To yayane meke faruwa ne?ni inacan waje inajiran ki ke kuma kinshanya ni. "To ba Mom bane wai bazani ba,haka kawai tace bazani ba,kafin Guggo tayi magana Mom ta cabe"fisabilillah Guggo taya za'a barta taje gidan surukai saura sati biyu biki?wallahi rashin kunyar Akeela kullum gaba yakeyi. "Maimuna kedai sai kayi bagidajiya ko mu tsofaffin da bazamu dinga wannan abinba bare ku yara,yanzu lefi ne don Akeela ta shirya munje gidan Yaya muhammadu da ita?ke don ma banyi niyya bane da wallahi ranar asabar mai zuwa zata koma can da zama,zo muje kinji",tana kare fadan hakan suka fita Akeela nabiye da ita tasha wani dan ziririn mayafi tana karkada shafaffen baya kamar andanne da iron. Mom din Akeela kuwa sakin baki tayi tana duban su har suka bar farlon,a fili ta furta"Wallahi sam abinda Guggo take bata dacewa,wannan ina mutum zai yarda yabata danshi?mtsewww taja tsaki tare da juyawa ta koma kitchen din. Su Guggo Laure kuwa koda suka isa gidan sun cidda ya sake kacamewa don Aunty Maryam ma ta iso,wasu daga cikin 'yan uwan Bodejo su uku suma sunzo,hannu bibbiyu aka tarbeta kamar yanda aka saba,nan aka shiga gaishe-gaishe Guggo Laure tace"Ashe kuma ankawo lefen yara banida labari don ba'a kirani a amsa kaya dani ba,shima a waya yanzu Akeela take nuna min shine nace bari nazo naga zahiri"tayi maganar tana dariya kasa-kasa. "To menene a amsan lefe Laure kinmanta shi taufeeq mune zamu hada mukawo? Harouna su suka kawo lefen Mashahuda shida hauwa'u daga kaduna,a ranar kuma aka kawo na muneefa,to ai ba wani abu bane,sannan yaranki duk maza ne ba mata ba balle ace suzo a amshe kayan dasu. "Amma Yaya Bodejo duk da maza ne ai naga suna da matayensu ko?ko babu komai ai ace ko su maimuna da uwar mujaheed ne a turo,ammaai babu komai dama idan ba'a dauke ka da muhimmanci ba babu abinda bazaka gani ba. "Guggo wallahi ko daya ba haka bane,kayan ma ba mata ne suka kawo ba mazane suka kawo kayan. Guggo Laure tace"Maryam to tunda mazane suka kawo,ba sai akira ko mansir bane? Aunty Maryam tace"To shikenan Guggo kiyahakuri ai akwai na wasu 'yan matan har guda uku bayan wadannan kibari idan za'ayi nasu zakiji komai mun amsa lefinmu dai wannan. Ture kaga tsiya Guggo Laure tayiwa dan kwalinta tare da hura hanci tace"da dai yafi kam. Bodejo kuwa tun sanda taji Guggo Laure tafara korafi ta yunkura tabar wajen. "To shi Sauban nashi lefen be isone kuwa ba? Dan murmushi Aunty Maryam tayi tace"Ea to ina tunanin sai next week zai iso dasu 'yan Dubai ba,kinsan shi acan yake hada lefensa"murmushi Guggo laure tayi cike da jindadi tace. "Ah Masha Allah, Allah dai ya iso mana dashi lafiya,da Ameen aka amsa gabadaya. Akeela
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87