Chapter 43
Chapter 43
yanzu za'a Sanya mata,duban Aunty labeeba tayi tace"please labeeba zuba ma Sauban abinci. "No mommy kinsan wallahi bazan iya cin abinci a hospital ba yanzu ma zan wuce gida nayi wanka sai nayi breakfast. Da yake mommy Sarai tasan halinsa shiyasa bata jaba tace"To shikenan amma yakamata ka hanzarta don kada kayi ta zama da yunwa ko?cikin kamewa yace"insha Allah mommy yanzu zamu tashi. Duban zuhra tayi tace"Baby meza'a zuba miki?akwai Chip's nd eggs sai samosa,akwai faten Irish da hanta sai kuma doughnut wanne zakici,cikin sanyin murya tace"mommy nikam nakoshi mouth dina babu appetite ko kadan shiyasa,mommy tace"to da yunwa kike tunanin za'a barki?kitashi kici abinci ko Yaya ne sai kisha magungunanki,nannarke murya tashiga yi tana neman botsarewa,wani kallo ya aika mata dashi cikin sa'a kuwa suka hada ido. Mommy ki zuba mata abincin za'a tsaya jin tabakin ta ne?kamar bashine yayi maganar ba saboda ko dagowa beyi ba daga daddana wayan da yakeyi,kamar zatayi kuka take dubansa. Mommy tace"wanne zakici a ciki? Cikin sanyin murya tace"faten Irish din,zuba mata akayi dai-dai,dayake jikinta din ba wani kwari bane dashi, matsowa Aunty labeeba tayi ta shige bata abincin a baki,duk da bakinta babu dadi amma taji dadin faten ainun,dakyar aka lallabata ta gama shan faten shima saboda Sauban ne daya tsareta da idon dina.Shuraim kuwa jiyake tamkar yayi kuka don Allah yasani yana tsananin masifar son zuhran,duk abinda yake Sauban na ankare dashi shys gabadaya ya nemi walwalar sa yarasa jiyake kaman yaje ya kama yaron da duka. Duk suna zaune zuwa can sister's din Shuraim suka mike kan zasu wuce,'yan matan nan kuwa sun mutu akan Sauban,mommy tace"Haba kukuwa har zaku wuce da wuri haka?yarshi tadanyi murmushi tace"Ai mommy Shuraim dinne wallahi zanje gdn bikin wata cousin's dinmu but Saboda shidai nayi squeezing din time muka wuto,kinsan yanda yake son zuhra kamar ya maida ta cikin ciki yasake haifota"duk cikan 'yan dakin dariya suka Sanya har taufeeq,shikuwa ogan yasake cudu² da face sam babu walwala, Shuraim kuwa sosa kai yaketa tayi cike da kunya.Mommy tace"Allah sarki ai dama hakane,mungode sosai domin a haka ma mune da godiya matuka Allah yabar zumunci,da Ameen duk suka amsa,duban shi Aunty safiyyan tayi cikin zolaya tace"Ouncle Romeo oya let's go! Nan ma dariyar aka sanya,dan susa kai yayi yace"Aunty muje nadai taka muku don bazan iya barin ta ita kadai ba wallahi look at her Aunty gaskiya muje na taka muku,duk da mamaki ake duban sa wannan karan Sauban tsaban mamaki daskarewa yayi don ko dago face ya kasayi,yana mamakin rashin kunyar yaron,a ransa yace _Lallai dole ne yaron yayi nasarar sace zuciyar kanwar tasa,dole ya Mike tsaye._ Fita sukayi Mommy kuwa sai dariya suke, Aunty Maryam tace"Lallai zuhra wannan yaron yana matukar son ki gashi kunyi masifar dacewa don shima kyakkyawa ne,ga natsuwa da alama idan kika aure shi zakiji dadi don bai boye irin son da yake miki, Laila tace"wallahi kuwa Aunty Yaya Shuraim na matukar sonta sosai, cousin's din su ya Asheer din Aunty safeena ne,hada baki sukayi wajen fadin dagaske?Nihal tace"Allah kuwa yace mata shi idan ma akace yaturo yanzu Allah zai turo don hajiyan su da kowa nasu suma sunason hadin musamman da sukaji kanwar Aunty safeena CE, Mommy tace"Kai Nihal duk a'ina kikejin wannan labaran? Laila tace"wallahi Mommy dagaske ne ya Asheer ke fadama Aunty safeena da mukaje gidan,ai gaskiya wallahi.....batare data karisa ba ya Sauban yadaka mata tsawa yana diddilo mata wannan idanuwan da suka koma jajaye,tsit tayi daga ita har Nihal jikinsu babu inda baya rawa,ita kanta Zuhra banda rawa babu abinda jikinta keyi ganin haka yasa ta zamiye ta juya tana me rintse idanuwan ta.Maida duban sa yayi ga Mommy yace"haba Mommy meye amfanin ku tasa yaran nan a gaba ana firar samari?dudu shekaran su nawa da suke hirar samari?wato ana ma sane tana karatu take kula wasu 'yan iskan yara?cikin bacin rai da karaji yake magana,cigaba yayi"Lallai zaki zaba kodai auren ko karatu cikin daya kizaba daya ki aje daya,mtsewww! Yana kare fadan haka yafita yana mejin zuciyar sa na wani irin bugawa,Taufeeq ne yabi bayansa. Duk cikan su day kallon mamaki suka bisa har yafita,ajiyan zuciya Mommy ta sauke,a ranta tana ayyana abubuwa ita kadai, Aunty Maryam da Aunty labeeba suka mike suna duban mommy"Aunty Hauwa'u mu zamu wuce kinsan tafiya kaduna zamuyi akai Mashahuda gidan ta,kafin keda Ummie ku karaso, Mommy tace"Ea nasani babu damuwa ai Labeeba Allah yatsare don Allah ki tabbata tasha magunguna nan,muneefa ma na aika mata da nata,can gidan ta zamu wuce mu"Aunty Maryam tace"Insha Allah.zumbur Zuhra ta mike duk da kana ganin yanayinta kasan karfin hali take face dinta babu wani walwala kamar tayi kuka tace"Mommy!juyowa Mommy tayi tana duban ta,cikin rashin abinyi da damuwa tace"Mommy nifa inason karatu na kibawa ya Sauban hakuri nazabi karatun Amma wallahi inason ya Shuraim,duk da mamaki suke dubanta,su Laila kuwa sai guntse dariya suke. Aunty Labeeba tace"ke Zuhra ki rufama kanki asiri kibar maganar nan a yadda naga Sauban yafita a fusace ai idan kika cigaba d maganar nan zai kassara kine a banza,kuma wannnan abin tun zamanimmu ne ba kukadai ba,duk wacce karatu zatayi to bata aure sai tagama degree,bakiga su Mashahuda da muneefa bane?mu kanmu sai da muka gama diploma mukayi aure,wallahi ki rufama kanki asiri kada kikawo wani sabon tsari, Aunty Maryam tace"Ah to kidai fada mata. Mommy cike da tausayin ta take duban ta,batare da tayi magana ba suka fita ita dasu Aunty Maryam,cikin raunin murya mommy tace"wallahi Maryam inajin tausayin Zuhra,soyayya tayi gaggawan shigowa rayuwar ta da wuri duk da farin jinine ma yasake ruruta wutar wani abu,inajin tsoron abinda zaije yadawo kinsan yayyen nan naku?ita kanta tana son yaron haka zalika shima da baya iya boye sonta ko gaban wanene,a gefe daya Zuhra na matukar son karatu yana daya daga cikin abinda yasa sam tatsani wani ya mata maganar soyayya kenan to Amma kinga yaron nan yaci galaba a kanta?Suma ajiyan zuciya duk suka sauke, Aunty labeeba tace"Allah ya jishemu alheri,bari muje zamu tare me napep ne kawai tunda su sun wuce gashi munbar yara a gida. ****** Koda suke mota suna driving sam yakasa samun natsuwa,a gefe guda kuma sam zuciyar sa taki aminta da maganar da Daddy yafada yana kallonsa a just for raha,sam yakasa natsuwa shi ba abin yaje yasake tunkarar wani a cikin iyayen sa da magan ar ba,wayar sa ce tafara neman agaji,dauka yayi daga can bangaren aka fara magana,amsa yabada kamar haka"sorry Kareem muna hanya ne gamunan karisowa. Aje wayan yayi Taufeeq ya dubesa"Kareem ne ko?daga ma Taufeeq Kai yayi kamar wani me ciwon baki da kyar yace"Yana sanar dani azo ayi abinda za'ayi gasu Saif zasu wuce. Kara speed din motar Taufeeq yayi har suka karisa,a gurguje sukayi wanka suka shirya,sunyi bala'in kyau cikin wata danyar shadda cofee sunyi anko,abokin Abbie ma na Dubai bai samu zuwa ba. Nanfa aka fara hotuna. Amma ce keta surfama Ummie bala'i akan abinda ta aikata"bilkisou da hankalinki da komai da sanin addininki dai² gwargwado kina takaba amma kika zauna kinata caba ado na daukar hankali?anya bilkisou kinyiwa Sadeeq adalci kuwa?bilkisou haka ake takaba?wallahi baki kyauta ba,kinsan yanda maganganu zasuyi ta fita akanki tunda abune na yanar gizo yanzu?wallahi bakima kanki adalci ba bare 'yayanki,takarisa maganar cikin fusatacciyar murya. Cikin tsananin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87