Chapter 19
Chapter 19
after 1 month da satittika gashi zuhra jibi zata fara zuwa school(UNIMAID) sosai take jin dadi da annashuwa gashi gefe guda kuma suna tsananin mutumci ita da Shuraim da yake shi mutum ne mai barkwanci sosai duk da haka ZUHRA takasa sakemai ssai. A bangaren Kareem kuwa hakan ba karamin sosa mai rai yake ba don yanason ZUHRA tun randa yayi tozali da ita suna zaune da Shuraim yaji yana tsananin kaunar ta,wannan kenan! "Hajiya kefa kika ce zakiyi wani abu gashi wasa² anci 2months da saka ranar auren su yanzu saura fa 6 months, Rammat tayi maganar tana latso hawayen da suke gangaro mata. Itakuwa banda girgiza kafa hajiya Biba babu abinda takeyi, Mom tadan mere baki tana duban Hjy Biba"Ni kam hajiya anya aikin malamin nan naki kuwa yanay........ "Ke...k..kke ke...keke kul! Meye haka rabi nema kike kidebomin tafasashen ruwa mai dafa duk taurin nama?ki rufamin asiri kinsan kuwa aikin dangudelle na yarda dashi na yarda da aikinsa,saboda shidin shedani neeeee takarisa maganar tana wani rimi dolen dole na hada zuri'ah da Galadima da wannan makirar tsohuwan Bodejo,inaso na bawa Laure mamaki tasan cewa ni nafita hatsabiban ci wallahi dani take zancen. Duban Rammat tayi wacce take kukan cikin takaici tace"dallah ke kimin shiru,sai kace kema din ba mace ba?yanzu ke ba zaki iya jawo hankalin yaronnan gareki ba?meye amfanin macen da bata iya kissa ba kwata²n ta? hajiya Biba takarisa zancen tana huci tare da babban kada hanci. "Hmmm aini Rammat wani takaici take bani hajiya,ga Akeela nan tanaji tana gani zata kwace mata shi. Dan bata face Rammat tayi"Kai Aunty fatan tsiya haka? Wani hararan Mom ta galla mata tare da mikewa ta dauki jakar ta duban hajiya Biba tayi"Hajiya zantafi bnson baban Aseef yadawo yaga bana a gida,Kinga ba'asan na fita ba. Hajiya Biba tace"shikenan sai munyi waya,nan sukayi sallama tafita a ranta da qudurori kalakala,don ta dauki alwashin koda Rammat zata mutu ba zata yarda ta aure Sauban ba. **** **** **** Zaune take a cikin class din suna sauraren lecturer din English don da abinda aka fara tarbansu kenan sosai ta maida hankalinta akan lecture dinda ake musu,sanye take da Arabian gown coffee tayi rolling viel din sosai tayi kyau fatanta kalar half-caste yasake bayyana,duk da sanye take da facemask amma sosai taja hankalin 'yan class din. Yadauki tsawon 20minutes yana musu bayani sannan yafita anan wani lecturer din yashigo yadauki 10 minute's kana yafita,na ukun ne yadauke fifteen minutes kuma daganan wajejen 11:30 suka fito daga lectures gabadaya, student's da dama sun sami bakin department dinnasu suna hira wasu na introducing kansu ga juna saboda asaba. Zuhra kuwa kaitsaye gate tanufa don tafiya gida,tare da wasu daliban da qyar tasamu napep tahau dropped yakaita gida,cike da gajiya ta shiga gidan kaitsaye apartment din Ammi ta nufa. Moryoyi ta fara jiyowa na 'yan mata koda tashiga parlon Aunty muneefa ne da Akeela,kan dinning kuma Aunty Mashahuda. Cike da fari'a muneefa tace"A'ah students,yau UNIMAID sunyi sababbin dalibai. Dan murmushi kawai Zuhra tayi tana karisawa wajen Mashahuda dake dinning,itama cike da zolaya tace"Wai yau 'yar gidan Ammi akwai rigima. "Kai Aunty Mashahuda nifa ban gaji ba,dudu lecture's uku mukayi muka fito, takarisa maganar cikin shagwaba. Ammi da saukowan ta kenan daga stairs tace"toh mene idan anmata tausar si auta ce,duk gidan nan itace auta yimata shine zaman lafiya. Cike da tsananin jin nauyin Ammin zuhra ta duqar da Kai tana murmushi,dariya mashahuda ta saki tace"Ammi kinga zuhra wai kejin nauyinki. Murmushi Ammi tayi dai-dai nan wayanta yasoma neman agaji, duban number tayi tare da sakin murmushi tayi picking. "Assalamu alaikum Son. Daga can bangaren Sauban ya lumshe ido cikin tsananin son Ammi yace"Sweetheart barka da rana. Murmushi kwance akan fuskanta tace"barka dai yakake ya aiki? Alhamdulillah Sweatheart jiya inata kiran number dinki yaqi shiga na Daddy ma haka nakira na Mash'huda kuma number busy tanata waya. Ammi tayi dariya me sauti tace"itada taufeeq ne nasani to ya aikin? Alhamdulillah,nima I think nanda sati biyu zan shigo zarian saboda branch dinmu na Abuja zanje naduba. Cikin jindadi Ammi tace"Masha Allah son Allah yakawo min kai lafiya cikin aminci da yardarsa. Cike da jin dadin addu'an ta ya lumshe ido yace"Ameen Sweatheart yasu Mom? don nayi waya dasu Bodejo. Ammi tace"lafiya lou Mom dinku ya kamata kkrata koh? "Ea Insha Allah haka za'ayi. Kana waya dasu Ummien naku da Abbie? Dariya mai sauti Sauban yayi wanda inba Ammi ko su Ummie dasu Bodejo ba bame ganin irinta yace. "Ahhhh kaji Sweatheart sosai ma muna waya dasu. "Yawwa son haka akeso Allah yamaka albarka. "Ameen Ammi sai anjima a gaida yaran gidan. "To Shikenan tafada tana me zare wayar daga kunnenta. Cike da zumudi muneefa da Mashahuda ke tambayar ta ya tambayesu? Ammi tace"kowa ma ya tambaya ya kuma ce a gaida kowa don nanda sati biyu zaishigo kasar. Akeela kuwa wani kululin bakin ciki dana takaici ne suka dirar mata ganin ko damuwa bai nunawa akan ta,kamar ma yamance da ranar wata akansa,hakan yasa cikin bacin rai ta tattara kwamatsanta tabar parlon,babu wanda ya lura da ita sai Zuhra,sai dai ita hakan ko a gyalen ta dan tabe mouth ma tayi. *BAYAN SATI DAYA* Zuhra ce zaune da ita da Shuraim suna hira cike da nishadi don Allah yabawa Shuraim nasarar samun Zuhra don sosai ta sake mishi. Cikin muryan dariya tace"Yaya to idan kasamu balarabiya bazaka iya auren ta ba? "Hmmm yarinya bazaki gane ba,nifa yarinyar da nakeso ko a larabawan ba lalai a masu mai kyanta da quality dinta ba,kedai kibari wataran zaki ganta. Cike da shagwaba Zuhra tace"Lallai ma yayan nan naqi wayon,kawai dai kasa ma mana lokaci wataran kakaini naganta. Zuhra tace"To shikenan Allah ya kaimu. Da Ameen ya amsa yana mejin wani nishadi a ransa na yanda yaga yarinyar tayi bala'in sake masa. Baba Mudi ne ya bude gate saboda horn din da aketa dokawa,ko gama bude gate din beyi ba aka shigo da motar a zafafe, cikin bacin rai ya balle murfin motar ya fito kaitsaye wajen Baba Mudi ya nufa,cikin rashin da'a yafara magana. "Meyasa kake hakane tsohon nan?tunda nataso a gidan nan kai nake ganin matsayin me gadi gashi karfinka yafara karewa,don Allah katafi kabawa me jini a jika shima daman shigowa ya daddale arziqi mana, mtsewwww. Yaja tsaki,shigo Baba mudi girgiza kai kawai yayi a zafafe ya nufi apartment dinsu. Dan siririn tsaki zuhra taja. "Yayadai?shikuma wancen wanene? Zuhra tace"Hmmm barshi cousin dina ne haka yake duk gidannan shine Mara da'a shine wanda baiganin darajar talaka. "Allah yakyauta ubangiji Kuma ya shiryeshi,da Ameen zuhra ta amsa,anan suka cigaba da hirarsu. "Mom Wai dagaske ne?nifa bansamu labari ba sai shekaran jiya dana ga pic dinshi a IG yanda 'yan mata keta rushing akansa har fada wasu sunayi,baya kasarnan to waya sama masa aiki? Mom tace"bansani ba,hmmm burika na biyu basu cika ba don haka bazanyi sake shima na ukun yaqi cika ba. Aseef yace"wasu burika kenan? Mom tace"naso ace ko Sauban ko taufeeq daya a ciki ya aure Muneefa amma gabadaya babu wanda yasamu,abin bakin cika wai Sauban yafika,nifa bana fatan rayuwar wanda zaifi dana ko wanene shi,shiyasa kota halin kaka sai ka aure Zuhra,takarisa maganar tana wani huci. Wani irin sanyin dadi Aseef yaji a ransa. "Ga sa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87