Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,259 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

school tafada cike da murna da zumudi murmushi kwance saman fuskanta,daidai nan Baba mudi yafara wangale gate,hancin mota ne ta shigo kirar Corolla ( _da take bansan kan motoci ba amma motar daga gani medan tsada ce._ ) duk cikansu maida dubansu sukayi kan motar,shikuwa tun sanda yashigo gidan idanuwan sa ke kafe a inda suke zaune,sosai yaji zafin ganinta da wani,balle murfin motar yayi ya fito,dole idan zai shiga apartment din Ammi ta gabansu zai wuce,koda yakariso fuskar sa a sake yake dubansu,mikawa Shuraim hannu yayi sukayi musabaha tare da cewa"Barka da warhaka.Duk da cewa ya girmi Shuraim din sosai ma don Shuraim ai sa'an kaninsa ne na biyu kuma akwai tazarar shekaru tsakanin su. Duban Zuhra yayi face dinnan cike da fara'a yace"kanwar mu bako akayi ne haka?dan rissinar da kai tayi tace"sannu da zuwa ya Kareem,cikin fara'a yace"yawwa mun sameku lafiya?ya shirye-shiryen school Kuma? Zuhra tace"Alhamdulillah. "To Allah yabada sa'a! A takaice ya fada. Da Ameen duk suka amsa. Wucewa yayi. Duban Zuhra Shuraim yayi yace"Ina me neman gafarar ki akan maganar da nazo miki dashi bansani ba dai ko zaki iya amincewa dashi? Zuhra tace"me kenan ya Shuraim? "Idan babu komai inaso kibani wani matsayi da wajen zama a jerin masu kula dake,cikin rashin fahimta take dubansa. Gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasa yace"kibani matsayi na yayanki muzama Yaya da qanwa nidake don Allah. Murmushi tayi tace"Kai Ya Shuraim nina dauka wata magana ce,haba ai babu komai nabaka wannan matsayin Yaya. "Masha Allah kanwata godiya nake Allah yasaka da alkhairi. "Ai babu komai Yaya ta fada cikin sanyin murya,nan suka cigaba da hirarsu don Zuhra sosai ta sake da Shuraim. ** *MALAYSIA* ** Yauma kamar kullum shirinsa yayi yafito cikin suit blue black,takalminsa kamfanin Gucci ne dai cover shoe black colour sai agogon hannunsa Rolex,Kai tsaye driver yaje yabude masa back seat yashige shikuma yaja motar, gaisheshi gateman yayi sannan suka fice, laptop dinsa yafara daddanawa yana duba saqonni ta email daga wasu kasashe da dama nason takalman company nasu, wayar sace tafara neman agaji. Sai da yadau lokaci yana ringing kafin yakai hanny yadau wayar,sunan Kareem ne ya bayyana akan screen din,cikin kamewa ya dauki wayan batare da yayi magana ba,sallama Kareem yayi. Amsawa Sauban yayi nan suka fara gaisawa inda Kareem keta masa shikiyanci zuwa can yace"yawwa dama kira nayi na sanar dakai wani abu don kaine babban Yaya, kuma babban wa uba. "Malam katafi maganar ka kaitsaye, yafada cikin kamewa. "Dama akan kanwar ka nakira muyi magana don naga iri ina nema don alamu sun nuna idan banyi da gaske ba za'a mun shigo² ba zurfi,kai nifa idan na so samune ma a hada bikin mu tare. "Akan wa kake magana kenan? Sauban yayi maganar wanda ko driver din ba lallai yaji abinda yake cewa ba. Kareem yace"Akan zuhra mana nake magana gaskiya ni nagani inaso asan yanda za'ayi dani dazu na ganta da wani karamin yaro sa'an kabeer dinmu ne ma dagani wannan yaron wai yazo zance,so please ga dan gida nan. Lumshe idanuwana Sauban yayi tare da kwantar dakai dakai a jikin seat din motar wanda duk kwakwanka bazaka gane yanayin da yake ciki ba yace"menene haka Kareem?so kake ka zubar mana da mutumci yarinya karama tanemi ta raina mu?look gaskiya kada ma kafara wannan tunanin,guda nawa take wannan yarinyar neman zubda mana da mutumci gaskiya ban goyon bayanka",yayi maganar cikin kwanciyar hankali. Daga can bangaren Kareem kuwa baki da hanci yasaki yana sauraran Sauban sai da yabari yakai aya sannan yace"Nikam Sauban gaskiya bazan iya da wadannan halayyan naka ba menene aciki? "Komaima! Sauban yafada a takaice,a zafafe ya kuma cewa"inbanda jawo raini ina kai ina kula wannan kwailar yarinyar?yana gama fadar haka ya yanke kirar. Cigaba da danne dannensa yake a laptop din wanda sam baka isa ka karanci yanayinsa ba. Ta bangaren Kareem kuwa mamaki sosai ya gama rufeshi da halayyan aminin nasa shisam yafiye son girma da rashin son raini. ( _A daiji maganar babban Yaya Kareem don shine madaurin auren zuhra._ )😜 A haka suka isa babban company wanda gabadaya ma aikatan wajen sai girma suke bashi. **** *KADUNA JABI ROAD* Ummie ce zaune akan lumtsememen leaderseat din dake parlon ta kafa daya kan daya tana duban tashar aljazeera, Abbie ne yayi sallama tare da shigowa a hankali tadago tadubesa dan murmushi tayi tace"Sannu da zuwa yallabai. Murmushi Abbie yayi cike da zolaya yace"Yauwa yallabiya,zama yayi kusa da ita da yake cushion din two seater ne cike da gajiya yace"Am tired Madam. Dan dariya tayi tace"Toh bari naje na hada maka ruwa kayi wanka zakaji dan dama then sai kaci abinci kadan kwanta stressed ne kwana biyu baka zauna ba yallabai gashi jibi zaka tafi Indonesia. "Wallahi kuwa akan furnitures din su Mashahuda nakeso naje kinsan bikinsu 6 month akasa su ita da muneefa, shiyasa ma nakeso muje tare nida ke mu zabo musu kaya masu kyau,harda kayan kitchen. Ummie tace"iyye lallai Abbien yara ya shirya to shikenan Allah ya kaimu amma bazamu kawo komai gida yanzu ba ko? Abbie yace"to me za'a tsaya jira Bilkisou ai gwanda a kawo komai nasan kilama kayan su rigamu isowa. Kafin kuma na auta na yazo Allah yanuna min auren ta. Da Ameen Ummie ta amsa a maqoshi. Dan girgiza kai Abbie yayi yace"Bilkisou kenan Allah ya karkato da hankalin ki kan diyar ki. Cike da kwarin gwiwa Ummie ta amsa da Ameen,da mamaki sosai Abbie yadube ta saboda jin ta amsa cike da confidence. Ummie ta dubeshi murmushi kwance a fuskanta mai Kama da yaqe tace"kana mamaki koh?hmmm nima inason Zuhra sai dai tsanar da nake mata ya ninka son da nake mata,ina tsananin jin tausayin ta amma ya zanyi narasa meke damuna,takarisa maganar cikin raunin murya. "Huhhhh!Abbie yasauke ajiyar zuciya yana dubanta,zuwa can yace"Bilkisou bana fatan zagin da yakeyi yazama gaskiya. Cikin rashin fahimta Ummie ke dubansa. "Ea ina zargi,alamu suna nuna kamar akwai sihiri tsakanin ki da Zuhra. "Koh? Ummie tayi tambayar. "Kwarai da gaske, bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba. Sosai gaban Ummie ya buga hankalinta yayi kololuwan tashi. ( _Duk da kin kasance Mai biyayya akan wannan abin kinkasa wa mahaifinki biyayyaaaaa._ _To bari kiji wallahi wallahi Ina sake jaddada miki muddin baki shiga hankalinki ba Bilkisou bazan taba yafemiki ba._ ) Kalaman Amma ne suka fara dawo mata a kwakwanta hankalin ta yasake tsananin tashi duban Abbie tayi idanuwan sa a rufe tace"Don Allah kadena fadamin haka kana tayar min da hankali na insha Allahu everything will be fine. Mikewa yayi jikinsa sam babu kuzari yanufi stairs,hawaye ne masu dumi suka tsiyayo ma Ummie. *_ADDU'AN DAI SHINAKE BUKATA NAGODE SOSAI MASOYA DA WADANDA SUKA KIRA DAMA WADANDA BASU KIRANI BA SON SO FISABILILLAH 🙏🏽 Happy birthday to you my rabin jiki baby Yusuf (Ãjmãl) Allah yaraya ka ya shiryaka yabaka ilimi Mai amfani da albarka ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka Yusuf Imran Muhammad bature❤️🦋🔐_* Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 07/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 17-18 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______A kwana a tashi babu wuya

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});