Chapter 83
Chapter 83
jiyo motoci anzo ɗaukar mutane don tafiya dinner,hakan yasa Zuhra taji wani iri kamar ta ƙwala ihu. Haka dai suka tafi sauban kam be wani jima ba ya shigo lokacin Zuhra tayi baccin ta abinta shi kam yana mamakin wannan baccin na kwana biyu da takeyi yauma har ɗaki ya kaita,haka ya cigaba da rainon ta like baby. Washe gari kuwa da wani azababben zazzaɓi ta tashi da mugun ciwon kai duk da kuwa taƙi yarda ya gane,sa mata abin wuya yakeyi ta jikin mirror yana kallon ta. "Baby kinyi balai'n kyau kinganki?har naji wani kishi"ɗan shagwaɓa face Zuhra tayi tace"kai yaya nidai ka barni na shiga cikin ƴan uwa na Please". "But Baby kamar baki da lafiya right? Cikin sauri Zuhra tace"Nop yaya mene kagani kuma?Ni lafiya ta ƙalau" Murmushi Sauban yayi yace"Okay to muje,anko sukayi duk da ita lace tasa doguwar riga blue Black ta sanya veil white takalmi high heel white da ƴar hand bag ɗin ta white tayi kyau ainun. Shima shadda ɗanya yasa sai maiƙo take blue Black,hulan kansa light blue haka halfcover ɗin ƙafarsa,hannun ta ya kamo suka fito,anan masallacin Alhaji Mai Deribe aka ɗaura auren sosai mutane suka halarta tare da sheda auren. Muhammad Shuraim & Lailah Taleeb Muhammad,Aliyu Abdulhakeem& Barakah Haroun Muhammad (Nihal). Aiko gida ya cika tanƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi, Zuhra tana sashin Mom don acan su Aunty Mashahuda suke,itadai tunda ta ƙyallare ido taga wannnan jollop ɗin shinkafar da yaji curry hankalin ta ya tashi,wani mugun amai taji ya taho mata,duk iya ƙoƙarin ta na ganin ta danne ina,da masifar gudu ta shige toilet. Gabaɗaya su Aunty Safeena suka bita suna lafiya?sai dai Zuhra amai takeyi sosai don jikinta har wani irin rawa yakeyi,cikin sauri Aunty Safeena ta kamota daƙyar ta gama aman nan,haka tatafi luuuuuuuu. Yaraf! Ta zube a jikin Safeena,salatin suka sanya suna tattaɓa ta sai dai babu numfashi babu alamun sam babu numfashi a jikinta. Gabaɗaya sun gigice, Mom ma ta taho,ruwa aka ɗauko a fridge aka shafa mata sai dai ko ajiyan numfashi batayi ba, Mom ta dubi Aunty Safeena cikin ruɗewa"Me yafaru da ita ne haka Safeena? Aunty Safeena taba ma Mom labarin komai. Mom tace"To ai zama be ganmu ba,maza² kikira Sauban"nan Safeena ta lalubo Number sa tahau kira,har 2 times beyi picking ba,tana shirin sake kira ya kira ta. "Hello yaya kana inane?daga can Sauban ya amsa mata, gamu nan a apartment ɗin Mom don Allah idan babu damuwa kazo"cikin sauri ya Sauban yace"What is happening Safeena? where's her Zuhra? In Ina Aunty Safeena tafara,ko kafin tayi magana ya yanke don a lokacin fitowan shi kenan daga apartment ɗin Ammi yaje gaida ƴan uwan ta,cikin zafin nama ya shigo palour ko bi takan mutanen palour beyi ba,ya danna ma Safeena kira,hakan ya tabbatar mata da ya shigo palour. Mom tace"bari ni naje. Aiko babu jimawa sai gashi sun taho da ita,tambaya ya shiga yi meya same ta?hankalin shi tashe ya ɗauke ta ya fito,nan duk suka biyo shi. Mutanen palour suka mimmiƙe Hajiya Biba tace"Subhanallah meya sameta ne haka?nan duk mutane suka fiffito,Mom da Hajiya Biba sai Aunty Safeena suka bishi don motar shi dake bakin gate ya ɗauka gabaɗaya hankula ya dawo kansu kafin kace me magana ya zagaye gida. Aiko Mommy itama shiryawa tayi tare da yayar Ammi suka bi bayan su Taufeeq da Kareem suka kaisu,duk da kuwa jama'an da Mommy keda su haka ta tsallake su. Kaitsaye hospital ɗin su Dr Ahmad suka nufa cuz sun fi zaton suna can. ******** Sauban kuwa suna isa a take anan aka nufi VIP da ita Doctor's sukayo kanta cuz gabaɗaya Sauban ya ruɗe ganin ko motsi batayi ga jikinta ya saki gabaɗaya. Aiko nan aka ɗebi jininta tare da nasarar dai-dai ta numfashin ta,alluran bacci aka mata tare da sa mata drip suka fito,nan Dr Ahmad ke sanar dasu su kwantar da hankalin su insha Allah jikin da sauƙi ya bada jini aje lab a gwada su ɗan jira akawo result,yayi maganar yana dafa kafaɗar Sauban ganin yanda ya susuce lokaci guda. Babu jimawa su Mommy suka ƙariso tare da tambayar meyasame Zuhra sannan wani hali take ciki? Nan Mom ta shiga basu labari,can babu daɗewa Daddy, Abba, Baba Hasheem, Boɗejo, GALADIMA, Guggo Laure duk sun ƙariso suna neman cika asibitin. Wata nurse ta dubi abokiyar aikin ta tace"Oh sis su kuwa waɗannan wasu ahali ne suna neman tarewa a hospital? murmushi wancan nurse tayi tace"Galadima family kenan,kinga wancan tsohon to shine Galadiman"tayi maganar tana nuna Galadima, ɗayan tace"Wow but familyn so nice sunyi ko ta ina ga kyau"dariya wancan nurse ɗin tasa tace"ke duk wata mace zata so ta shiga family ɗin nan da sunan aure don a yanda ake bada labarin family ɗin komai sun haɗa Masha Allah"wancan nurse tace"kuma fa patient ɗin nasu ba wani ciwo bane me damuwa,don Allah ki kalli kayan alfarman dake jikinsu"wancan nurse ta sake cewa"Galadima family aka ce miki fa,I think wancan ne mijin me blue Black ɗin shaddan can,kinsan yanda ƴan mata ke rushing guy ɗin can?sai dai ance ɗan wulaƙanci ne gashi yana bala'in son matar shi,ance ma fa yarinya ce ƙarama don baza ta wuce 19yrs ba,yana son ta sosai"ko kafin wancan tayi magana Boɗejo ta katse su"kai kuwa waɗannan yara da tsinannen gulma kuke,duk a ina kukaji wannan?domin basuyi tunanin suna jin hirar su ba, gabaɗaya hankalinsu ya koma kan nurse's ɗin,su ko tsitsitsi suka shiga yi da idanuwa. Dr Ahmad ne ya leƙo tare da kiran Sauban,jikin shi na rawa ya shiga office wani mahaukacin bugu ƙirjinsa keyi. Dr Ahmad yace"bismillah Malam Sauban have a sit"zama Sauban yayi tare da ƙosawa yaji me zaice mishi,wani takadda Dr Ahmad ya miƙo masa yace"take this result nd da abinda ya ƙunsa. Ɗagowa Sauban yayi ya dubi face ɗin Dr Ahmad. [7/30, 14:53] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_* *~LAST PAGE~* ___Hannu ya miƙa masa sannan yace"Congratulation Mr Sauban Madam ɗin ka na ɗauke da juna biyu na tsawon 2weeks Allah ya sa albarka"Wani mugun farin ciki ne ya kama ya Sauban wanda ya sashi rungume Dr Ahmad babu shiri,sakin sa yayi tare da yin sujudur shukur,babu ɓata lokaci Sauban ya fice da result a hannu sai a sa ilin da ya hango su Daddy ne yaji wani irin nauyi da kunya,hakan yasa shi babu shiri ya kame kansa duk da kallo suka bisa tare da tambayar shi me Dr ɗin yace,saboda har ga Allah hankulan su a tashe yake, Sauban cikin kamewa yace"sunce da sauƙi sai dai ga results ɗin"yayi maganar yana miƙawa Mommy da tafi kusa dashi,aiko ta warware don dubawa,inda wasu suka shiga tambayar me result ɗin yace,ai kafin abada answer Mommy ta daddage ta saki guɗa wanda ya jawo hankulan mutane da dama, Mom itama ta amsa result ɗin cikin farin ciki ya shiga furta"Alhamdulillah Allah mungode maka"Boɗejo ta mere baki tace"dama sai da jiki na ya bani yanzu haka ciki ya shiga ne tunda akace tayi amai,to Allah ya ƙara lafiya,don ciwon me ciki sai haƙuri,kai Abdulkarim kuzo ku sauke ni a gida mun bar jama'a"duk dariya aka sanya,su Daddy duk wanda ka kalla fara'a ne a face ɗin sa,haka zalika Ammi wani farin ciki ne ya ziyarce ta wanda ko a cikin Mashahuda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87