Chapter 11
Chapter 11
daga motan ko kallon inda suke beyi ba ya shige cikin masjid din,amma su da take sun ganshi shine fah. Yadade sosai a bakin gate din daga karshe yashiga motan ya gyara parking din agefe yanufi masjid din yayi alwala yashiga ciki. Su kuwa daga Mashahuda har zuhra kowacce takanta tayi don kaitsaye apartment din bodejo zuhra tashige,koda tashigo bodejo bataji shigowanta ba tana kitchen itada nana mai aikinta itama dattijuwa ce suna abincinsu ita da Galadima don suna da diabetes. Shiyasa bataji shigowar zuhran ba,can bedroom dinta tashige tare da sanya key tafada kan bed tana dafe kirji,gabanta banda dukan uku uku babu abinda yakeyi,tadade anan kwance zuwa can tamike tashiga toilet don dauro alwala. Bata jimaba tafito koda tafito kunna dum light tayi ta shimfida praymat ta tada sallah. Koda ta idar zama tayi har akakira sallahn isha'i tayi sanna tabude bedside drower dinta tafito da cake da doughnut wanda mommy tamata kafin su koma,cake uku ta dauka doughnut biyo,tabude dan fridge dinda ke cikin dakin ta dauko lemon mountain dew. Kan bed din takoma tahau tare da dauko phone dinta tashiga tiktok,da videon wannan yarinyar da ta shahara a duniyar tiktok tafara cin karo,wato Aakeelah Mancy don tashi take amfani,bude videon zuhra tayi nan taciddata taci kitson attached,tana sanye da riga da wando murna takeyi tayi tanama fans dinta albishir din cewa ankusa samata rana,sai ihu da tsalle take . Dan siririn tsaki zuhra taja kasa kasa a ranta tace"Kai wannan yarinyar ta cika rawar kan tsiya. Bodejo kuwa sai da sunacin abinci hankalinta yadawo jikinta cewa su Zuhra fa basu dawo ba tun wajen biyar da suka fita,dai dai Sauban yayi sallama. Galadima da bodejo suka amsa masa idanuwansu na kansa cike da tsantsar soyayyan sa a zuciyoyinsu, cike da zolaya yace"Don Allah tsofaffin nan kada kucinye ni batare da nima naga 'yayana da jikoki na ba,ku gwara daku don da alama har tattaba kune zaku gani. Dariya suka sanya bodejo tace"Ungo nan,tayi maganar tana aika masa da daquwa,murmushi yayi tare da jan kujerar Galadima ya zauna,bude warmer din yayi yazuba lafiyayyen dambun accan Wanda yaji kayan ciki tare da vegetables. Duban shi Galadima yayi yace"ai shiyasa kaji muka damu dakayi auren kaima shiyasa muka zaba maka mata. Dan hade face yayi yana Kai lomar dambun bakinsa. Murmushi kawai Galadima yayi yana girgiza kansa don tabbas yasan cewa Sauban biyayya kawai yake kokarin yimusu amma batare da yanason yarinyar ba. Galadima yace"munyi magana da mahaifinka kan zasuje gidan Laure wajen Sani a tsaida ranar aurenku....cikin sauri Sauban yadago tare da sauke ajiyar zuciya. Dan yatsine face yayi cike da aji da natsuwa don kowata macen albarka yadubi Galadima yace"please Galadima kada asa ranar nan kusa nida so samune ma asa nan da two year's. Wani kallo Galadima yayi masa irin na yhu re not serious dinnnan,budejo kuwa dariya tayi. Sauban yace"bakace komai ba Galadima. Galadima yace"kabari anjima sai kaje wajen mahaifinka ka tuntubeshi abinda yace shikenan. Wani wawan ajiyar zuciya Sauban ya sauke yace"ai idan nayi magana kamar nayi rashin kunya ne inhar nayari Daddy da zancen. Murmushi Galadima yakuma saukewa a karo nabiyu yasake cewa"Kaje kasamu Hasheem kayi maganar dashi. "Huhhhhhh wannan tsohon sam bazai ganeba, Sauban yafada a ransa yana share gumin dake keto masa duk da kuwa AC dake a wajen. Koda suka kammala cin abincin mikewa Sauban yayi yamusu sai da safe, bodejo tace"kabiya sashin Aisha katuromin Zuhra. "Hmmmm kawai Sauban yace yafita kai tsaye apartment din Ammi yanufa,da 'yar siririyar muryansa yashiga parlon da sallama,babu kowa sai Mashahuda tana waya,ganin shi yasa takatse wayar tafara tsilla-tsilla da idanuwa,sake hade face yayi don yana sane dasu. "Ke ina yarinyar nan?sosai Mashahuda cikin rudewa tace"Tatafi apartment din bodejo,don tagani wanda yake nufi. Harara ya zabga mata tare dayin kwafa yace"zanyi maganin ki soon,yana gama fadar haka yanufi corrridor dinda zai sadashi da parlon Daddy don yasan Ammi nacan. *******^^^^^^^****** Cikin muryan kuka take magana"wallahi hajiya ina sonshi nidai gaskiya ayi duk yanda za'ayi aga wannan auren baiyuwu ba tsakanin shi da wannan yarinyar,don ni natsaneta kodan fans dinda takedashi a tiktok. Wacce aka kira da hajiya na duba sai karkade kafa takeyi,face dinta murmushi kwance daga ganinta kasan idanuwan ta kyar suke. "Haba Rammat to meye kuma abin kuka?nimafa inaso ki aure Sauban don yanzu shine tauraron sa ke haskawa, Mom tayi maganar tana dafa kafadar Rammat. "Hajiya gaskiya duk yanda za'ayi ayi don ganin Rammat tashigo cikin GALADIMA FAMILY,yanda kika shiga kika fita harnima nashiga to itama tashiga,kinsan kuwa nan da 1week Sauban zai koma Malaysia akan sun daukeshi aiki,Mom tayi maganar. Ai dasauri wacce suka Kira da hajiya tadubi Mom tace"Wai Rabi dagaske kikeyi?kinfasan burina baiwuce Koda yaushe ku aure manyan mutane ba kushiga dangina dana ubanku ana girmamaku,tuntuni nayiwa Rammat sha'awar auren yaron nan,Ashe makirar Laure tarigani hada nata tuggun?hmmm nasan Laure farin sani sai dai ita batasanni ba batasan koni wacece ba,amma muje zuwa a sannu zanyi maganinta. Ki kwantar da hankalinki Rammat,insha Allahu sai kin aure yaron nan Koda kuwa zakiyi kishi da wancan kodaddiyar yarinyar ne,tuni zamuyi waje da ita bayan auren. Rammat tace"A'ah hajiya ni gaskiya bazan iya zama da wannan munanan yarinyar ba,natsaneta. Mom tace"muma bamu fata insha Allahu bazakiyi zaman kishi da ita ba aikinfi karfinta wallahi. Hajiya tace"hmmm ku yarane bazaku gane me nake nufi ba amma a hankali zanyi muku bayani, Rammat ki kwantar da hankalinki indai Sauban ne kisa aranki kinsame ahi kingama. Dariya Rammat da Mom suka sanya cike da farin ciki. _TAB CAKWALKWALIN CAKWAKIYA KENAN SAUBAN KAIKAM KAGA TAKANKA_🥴 _YANZU FA WASAN ZAIFARA KUDAI KUCIGABA DABIN ALQALAMIN OUM ÃJMÃL._ Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 22/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 08 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ____Sai bayan sallar la'asar Taufeeq da Kareem sukaje daukoshi a airport yadawo gida cike da nasara inda gabadaya farfajiyan gidan GALADIMA FAMILY cike yake da yara da jikoki don taryan Sauban. A hankali motan tashigo cikin farfajiyan gidan bata tsaya ko inaba sai parcking space,su duka ukun suka fito daga motan kowanne dariya ne kwance akan fuskar sa. Yaran gidan ne suka fara tsalle da muryan dawowan sa inda suketa tururuwan yimasa barka da zuwa. Yassir babba ne yajawo trolly bag din. Uban gayyar kuwa direct wajen Ammi yanufa kaitsaye murmushi kwance akan fuskar sa ya furta "Oyoyo sweetheart yayi,yayi maganar tare dayin hugging nata. Murmushi kwance akan fuskanta tadan bubbuga bayansa tace"Oyoyo son hope kadawo lafiya? "Alhamdulillah sweetheart ! Ya ambata. Nufar bodejo yayi da niyyar yin hugging dinta itama,da sauri taja baya tare da mere baki tace"Allah yatsareni da wannan dabi'ar yahudawan inazan iya wannan shedancin saudan?boko yagama lalataka gabadaya😏 Murmushi su Ammi suka sanya. Nufar Ummie yayi fuskar sa cike da fari'ah ya miqamata hannu don musabaha,itama miqamasa tayi don gaisuwan su kenan muddin zasu hadu. "Ummie na yaushe kuka shigo Mai din?ainazata sai gab azumi zaku iso? dariya Ummie tayi tace"aikuwa wannan zuwan munzo da wuri amma jibi zamu koma saboda school dinsu Laila da Nihal. Gyadakai yayi tare da murmushi yanufi Mom tare da rissinawa ya gaisheta itama ciki da fari'ah ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87