Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikin falon Abba. Abba da kansa yashiga d'akinsa yatasoda Rahma daketa rawar sanyi, saman kujera ya zaunar da'ita Doctor yashiga aikinsa, babu wata matsala Alhaji 'Yar damuwace kawai Dr Kaleed yafad'a. Abba ya ce, "to Dr babu wani taimako da za'ad'an bata kenan?. A'a zan mata allura da magani tad'an samu barci, insha ALLAHU daga nan zuwa yamma zata koma Normal, yanzudai idan namata allurar tad'an samu koda tee ne tasha saitasha magani tayi wanka da ruwa maid'an sanyi ta kwanta, insha ALLAHU normal zata tashi nanda anjima. To madallah Dr mungode sosai. Babu damuwa Alhaji aii aikinane. Babu 6ata lokaci Dr yayma Rahma duk abinda yadace, ummi tabata shayi tad'ansha kad'an tabata magani Wanda tashashi da k'yar Dan Rahma akwai tsoron allura da magani, bataso ko kad'an allurarma saida lallashi akayi. Bayan tasha maganin ummi ta taimaka mata tayi wanna a bayin Abba, kaya aka d'akko mata tasaka takuma kwanciyarta a gadon Abba sai barci. Hummmm wai ina Safna?. Tana nan acikingidan kuma labari yakai mata, ancanjeta da Rahma, Dan haka tadage tarink'a tsallen murna ita taci nasara, shikenan zata mallaki bobonta nanda lokaci kad'an, har ruwa tazuba k'asa tasha Dan dad'i. Cikeda farinciki takira Baseera ta guntsa mata, murna sosai ta tayata harda jinjina da yaba k'ok'arinta na dagiya. Bayan sungama da baseera takira zeenat itama, zeenat ta ce, " wlhy Safana kin tafka babban kuskure a rayuwarki, na tabata nangaba saikinyi Dana sani Mara iyaka, son zuciya yasa kin bijirema iyayenki akan Wanda baima San da zamankiba, ke kanki bakisan Inda yakeba yanzu, bakida tabbacin zai kar6eki kobazai kar6i soyayyarkiba, wlhy kidaina biyema hud'ubar baseera zatayita kaiki tana baroki a tashar wahala ne...... Safna ta k'atseta atsawace, kee!!! Dallah malama yimin shiru, nakiraki nafad'a mikine danki tayani murna ba surutun banzaba, aiikin banza kawai mtsowww taja tsaki tana yanke wayar. "Daga can Zeenat ta girgiza kai tana fad'in ALLAH ya shiryeki Safna, amma zakiyi nadama wlhy na tabbatar." Babu Wanda yakumabi takan Safna shagalin biki akacigaba da gudanarwa, itama tafita harkar kowa agidan lamuran gabanta kawai takeyi harda yima Rahma dariyar mugunta. Na ce, "hummmm. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.* Bobo ya lalubo wayarsa dake wringing daga aljihun jins d'insa, ido yad'an zaro tareda kallon Ya Sulaiman dake duba yarinyar da akaima fad'e. Lfy kuwa bobo?. Tab ya Is'haq ne kasanfa sunacan suna jiranmu..... K'ara kiran da akayine yasa Yakuma kallon wayar, ya is'haq d'innedai, d'agawa yayi tareda yin sallama. Abdulmalik wai kuna inane kaida sulaiman?, ya Is'haq yafad'a daga can. Wlhy muna asibiti wajen yarinyarnan amma gamunan zuwa Ku k'ara hak'uri. Tom yakamatafa kuyi sauri Dan akwai abubuwa agabanmu masu yawa. Gamunan yanzunan insha ALLAHU. yanke wayar yayi tareda dawo da kallonsa kan ya sulaiman, ya Sulaiman yakamatafa muje kasandai masifar babban yaya, muk'arasa kafin ya k'ulu. Gsky ne muje kawai aii nagama harma takoma bacci. Bobo yad'an lek'a fuskarta, ya ce, " baiwar ALLAH, wlhy rashin maganar yarinyarnan yana damuna, yakamatafa ace iyayenta sunsan halin datake ciki. Hakane gsky to amma yazamuyi? tunda bamusan idan takeba, saidai mucigaba da addu'a. Idan kuma tak'ara samun lfy mubi shawarar Ammi mumaidata wajenta kawai. To shikenan bobo yafad'a yana fitowa. Waje yanufa shikuma ya sulaiman yashiga office Dan ajiye kayan hannunsa. Babu dad'ewa yafito, mota yashiga Inda bobo ke zaune a mazaunin direba, bobo yatada motar suka fice daga asibitin. .+. Gidansu Safna kuwa anyi shirin kamu Wanda aka had'a a babban harabar gidan nasu, saidai matsalar amarya babu lfya tana d'akin Abba kwance tana barci. Hafsat matar ya Shaheed ta kalli ummi, ummi to yanzu yaza'ayine harfa dangin angon sun iso ga babu amarya, dama Safna zata mana alfarmar yanzu kawai saita zauna amadadin Rahma d'in. A'a barta kawai hafsat, nibanamaso muna saka Safna acinkin sha'anin bikinnan, takalli agogon dake hannunta, hafsat inaga bari kawai atada Rahma d'in dukda dai bata dad'e da kwanciyaba. A'a ummi abarta kawai likitafa ya ce, tana buk'atar Hutu, gashi dangin ango since k'arfe tara akwai mother Night, yakamata tasamu ishashshen barci kafin sannan, yanzu bari nayima Basman aunty Yahanasu magana saita shirya tazauna amadadin amarya tunda kusan kansu d'aya. Yauwa hakama yafi, dama gasu suna kama ba laifi. Haka suka saka Basma aunty yahanasu k'anwar ummi tashirya tsaf tamkar amaryar, idanma baka saniba saika d'auka Rahma d'ince Dan suna matuk'ar kama, idanuwa kawai Rahma zatafi Basma. Dahaka aka gudanar da kamu Wanda yak'ayatar da dangin ango, su khairiyya da khursiyya dasu aunty Rasheeda sai zuba lik'i suke wa amarya, Dan basusan ba amaryarsu bace. Dahakadai taro yatashi gab da magriba Alhmdllh. Duk shagalinnan da akeyi Safna tana d'aki kwance abinta, da barcima takeyi kid'an da'aka sakane yasa tatashi tana mita da tsaki anhanata barci wai, wayarta ta d'auka takira *boy danneman k'arin bayani akan aikin data bashi. Ya ce, "mata yana nan yana k'ok'ari. Tana yanke wayar takira Baseera sukaita labarinsu Rabi duk akan bobone. Na CE hummmm. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Su bobo suna isa gidan suka Tatar da ya Is'haq da ya Hamza zaune aharabar gidan, harda wasu samari wajensu bakwai, cikin samarin danginsune, ya Hamza yana cikinsu sunashan shafta. Ya Is'haq kam yana gefe zaune saman mota Dan bakomai yake Shiga cikinsuba kasancewarsa babba. Bayan bobo yayi fakin suka fito, wajensu ya Hamza suka k'arasa, hannu sukaita bama matasan samarin ana musabaha🤝. Bayan sun gama gaisawa Bobo yanufi Inda Ya Is'haq yake. Hannu yabashi shima suka gaisa. Ya ce, "kunje kun wani mak'ale a asibiti tamkar kun manta da abinda me gabanku. Sorry babban yaya, bobo yafad'a yana had'e hannayensa waje d'aya alamar tuba🙏🏻. Dirowa ya Is'haq yayi, to yazanyi idan ban hak'uraba ma. Motocine suka fara shigowa gidan, bobo yabisu da kallon yana fad'in wannan gayarfa daga ina?.... Daidainan ya Hamza da ya sulaiman suka k'araso garesu. Ya Hamza ya ce, " daga gidan amaryarka suke, sun halarci kamune. Baki bobo yad'an ta6e ya Hamza miye kuma kamu?. Kafin ya Hamza yabashi amsa aunty Rasheeda da aunty ummy suka k'araso, aunty sameera dasu khursiyya suna biye dasu. Bud'a aunty Sameera tarangad'a akunnen bobo, yay saurin toshe kunnansa, saida tagama sannan ya kalleta fuska a shagwa6e, kai aunty Sameera dodon kunne zaki kashemin?. Dariya suka shek'e dashi suduka, yayinda aunty Rasheeda tafara fesama bobo turare mai shegen k'amshi, kaima ankamaka kamar yanda mukaje kama amaryarka. Dariya su ya Sulaiman suka saka danganin yanda bobo ya kwa6e fuska tamkar zaiyi kuka, ALLAH matannan nakula kun rainani yafad'a yana hararsu. Dariya sukayi gaba d'aya harda wasu daga cikin dangi dasuka zagaye wajen. Aunty ummy ta ce, "tab wlhy Bobo matarka ta had'u jar ubancan kai, kaiga wasu idanu masha ALLAHU, (" nace hum danma bakiga na asalin amaryarba kenan), tacigaba da fad'in aifa inaga aka kawo amaryarnan bazaka ringa fitaba, aikinma hak'ura zakayi dashi. Dariya sosai ake shek'awa, dukda haushi da yacikama bobo ciki wannan bai hanashi murmusawaba, ya ce, ''yan sa ido, kunje kunata k'arema yarinya kallo, halan har muninta kun gano?. Wata Zainab acikin danginsu ta ce, "wlhy ya Abdulmalik babu mai iya gano munin Rahma amarya, masha ALLAHU kam komai yaji zam zam..... Tak'are maganar da rufe baki. Nanma dariya akayi, shikam ya ce, kwadaiji dashi sa'idinniya kawai masu barci da ido d'aya, yana gama fad'a yafito daga wajen. Wasu daga cikin 'yammatan jisuke inama sune da wannan guy d'in, lallai yaci sunansa Bobo.

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});