Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Nidai araina na ce, "hummm. *_kotu_* Ayaune kuma su bobo suka koma kotu. Bobo bai k'asa aguywa ba yakawo manyan hujjoji da shedu masu k'arfi wad'anda suke nuna haneef ya aikata fad'e ga muheebat. Ciki kuwa harda muheebat d'in kanta, wadda ya sulaiman yayma aiki ayanzu haka tana magana. Bobo yak'arasa kusada muheebat ya ce, " muheebat kotu tanasonji miya faru dake aranar 16/8/2017?. Muheebat matashiyar yarinya mai wayo, tagyara tsayuwa, idonta na zubda hawaye ta ce, "yaya aranar data kasance 16/8 mama ta aikeni shagon Haleedu domin nasayo mata sabulun wanka. Fitowata kenan Haneef yafito daga gidansu da mota.............. *_ina mai baku hak'uri saka makon jina shiru, hakan tafarune saboda matsala da screen d'in wayata daya samu adaren Dana turo muku page 47, tom yanzudai komai ya daidaita._* _Acigaba da gashi!!!._ *_imiss you so much my fan's._*😍😍😍💋💋. *_luv u oll._* [11/12, 2:55 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 4⃣9⃣ Kamar yanda yasaba duk sanda yaganni yakanyimin murmushi aranarma haka yamin. Nad'aga masa hannu nima ina murmushi. Ya ce, "min heeban baba ina zakije?. Kasancewar alokacin bana magana namasa nuni da shagon haleedu da hannu. Yayi dariya tareda kamo hannuna, amma saina nok'e saboda inna ta hanani, ganin haka yasa yad'akko alawar dayakan bani kullum idan zani makaranta. Nikuma namik'a hannu zan kar6a saiya jawoni gaba d'aya cikin motar, daga wannan lokacin ban sake sanin inda nakeba sai a asibiti, wannan kad'ai nasani. Murmushi bobo yayi tareda juyowa ga alk'ali, ya ce, " yamai shari'a wannan hujjar kad'ai ta isa tabbatarma kotu cewa haneef ya aikata keta haddi ga heeba, abin lura anan shine haneef yadad'e yana k'ullama yarinyar gadar zare tahanyar bata alawa, ganin bazaici nasara tasauk'iba shine yasaceta tareda shak'a mata wani Abu harta rasa hankalinta, yaje ya aikata yanda yakeso da ita, awashegarin ranar yazo bakin titi nesa da anguwarsu ya jefar da ita dankar aganeshi, saidai kuma yamakaro Dan angansa harma aka d'uki number motarsa. Dan haka ina rik'on wannan kotu mai adalci datayi dubi da d'unbin shedunmu kuma da maganganunsu ta kwatoma wannan 'Yar yarinya hak'inta. She data tak'arshe itace zuwan Alh Abdurrazak abokin Alh sunusi office d'ina, yamai shari'a INA buk'atar tv, babu 6ata lokaci aka kawo TV, wani kaset bobo yasaka Wanda yayi copy d'insa daga computer office d'insa, duk abinda yafaru tsakanin bobo da Alh Abdurrazak saida suka gani. Tuni jikin Alhaji sunusi yay sanyi, yasan yau d'ansa yatafi saidai wani ikon ALLAH, amma tunda sunbama Alkali kud'i k'ila ya ku6ta. Bobo yay shiru tareda kafe alk'ali da ido tacikin gilas. Jikin alk'alifa yay sanyi, yasan tabbas duk abinda bobo yafad'a gsky ne, saidaifa matsalar yaci kud'in Alh sunusi tareda masa alk'awarin zai ku6utar da Haneef, gefe kuma ga bobo yasan Barrister AAA hamshak'i sarai bashida sauk'i, kuma zai iyayin komai danyaga yakar6ama yarinyar hakkinta, azuciyarsa ya ce, "gaba kura baya damisa kenan. Dandanan ji6i yajik'e alk'ali dukda yawan fankoki dake bada iska acikin kotun, asaitinsama akwai guda d'aya da aka aje danshi kad'ai sai abin yabama bobo dariya, Dan haka ya murmusa tareda yin wata inkiya da yatsu biyu wadda alk'aline kawai yasan miyake nufi, kuma yasan abinda bobo zaiyi inhar ya danne shari'ar, yashare gumi yana maida kallonsa ga lauya mai kare haneef, ya ce, " lauyan Wanda ake k'ara kokanada abin fad'a?. Girgiza kai lauya yayi ya ce, "a'a. Alk'ali yamaida Kansa ga k'aton littafinsa yana dubawa. Gaba d'aya ran Alh sunusi ya6aci, jira yake kawai yaji hukuncin daza a yanke, lallai yaci burin saiya koyama bobo hankali inhar d'ansa yashiga cikin garari........ Bai rufe bakiba maganar alk'ali ta dakatar dashi. Bayan Alkali yayi surutansa asashe nakaza zuwa kaza anyankema haneef d'aurin shekara 14 agidan yari, datarar nera miliyan d'aya da rabi domin inganta rayuwar yarinyar da karatunta. Wani ihu haneef yakurma, saida aka rik'eshi, sai d'urama bobo zagi yakeyi. Shikam bobo ko'a kwalar rigarsa Yakama hannun heeba suka fice yana murmushi jin dad'i da samun nasara. Awaje yatsaya har aka fito da haneef, yaja gilas d'insa k'asa yana kallon haneef fuskarsa d'auke da murmushi. Ya ce, " haneef sunusi dala, so ina fata yanzu ka shaida wanene Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak'i, yanzu idan kafito saikayi takunka da sand'a gudun karkayi gamo dani Dan ruwaneni inhar nabayyana saina cinye gari, yay kasa² damurya zanyi missing naka my lovoly haneef bye aci gabza lfy.. Yaygaba batareda yajira amsar haneef ba. Daga Alh sunusi har haneef ido sukabi bobo dashi, haneef ma kuka yakeyi, Alhaji sunusi kam ALLAH kad'ai yasan miyake kitsama zuciyarsa. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.* Bobo yakwashi su muheebat sai gida, sai saka masa albarka iyayenta sukeyi, har gida yakaisu, inna tashimfid'a masa tabarma ya zauna. Cikin nutsuwa ya ce, "baba inaso kuyarda kubini can gida wajen iyayena kamar yanda nabuk'ata d'azu da safe, saboda gsky zamanku bazai yuwu anan anguwarba yanzu, na tabbata Alh sunusi bawai ya hak'ura baneba, to Dan haka nama iyayena bayanin komai, kuma sun bani izinin yau idan anyankema haneef hukunci to nawuce daku can gidan kud'an zauna nawani lokaci har abubuwa su daidaita. Baba yagyara zamansa, ya ce, " abdulmaleek kana ganin bazamu takurasu ba?. A'a wlhy baba babu wani takurawa ka kwantar da hankalinka. To shikenan mungode ALLAH yayimaka albarka ya azurtaka da yara nagari, ya albarkaci iyalinka da zuri'arka. Amin baba ngd, yanzu Abu nagaba kuma shine idan kun koma can heeba zata cigaba da karatunta, za'a canja mata makaranta, kud'in da kotu ta kar6a mata kuma sai a ajiye mata a account harzuwa nangaba idan ta mallaki hankalin kanta saitayi abinda takeso dasu, yad'ago yana kallon idris da fuskarsa ke cikeda farinciki, dama kullum burinsa yaga tilon k'anwarsa tana karatu, amma yanayin rayuwa ya hana hakan. Mungode ya Abdulmaleek. Murmushi bobo yamasa ya ce, "karka damu, inaso naji kai INA katsaya anaka karatun, mikuma kakeyi yanzun?. Matakin secondary nagama yaya, yanzu kuma ina aikin direba agidan su Rahma matarka. Bobo yajinjina kai ya ce, " babu damuwa kabani takardunka insha ALLAHU zan nema maka makaranta. Baba d'aya su baba da inna da idris heeba suka kaure da godiya ga bobo inna harda kukan farinciki itada baba. Bayan sun had'a 'yan kayansu masu muhimmanci bobo yakwashesu sai gidan Appa. Tarba akayi musu ta mutunci dan ansan da zuwansu. Su inna sun yaba da kirkin wad'annan mutane darashin k'yamar talaka, 6angaren da aka gyara musu aka saukesu. Bayan gaishe², bobo yamik'e yana fad'in Ammi bara nad'anje gidan sai zuwa anjima zan dawo, nasan su yayama Duk zasu shigo yau. To mukarram ALLAH yakaimu, agaidamin d'iyata da Nawal. To ammi zasuji, ina tagwayenkine?. Yo basuna gidankaba. Ayya aiban saniba bara najeto. Agurguje yafito yashiga mota sai gida. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Su Rahma duk suna zaune suna kallon wani India film, sunyi mugun shagala akallon film d'in Dan ana zuba soyayya ne. Bobo yashigo da sallama amma basujiba, tsayawa yayi yana musu kallon mamaki, TV yakalla danson ganin miya d'auke hankalinsa, shima shiru yayi yana kallon yanda mata da mijin suke zabga soyayya mai k'ayatarwa. Kamar ance Rahma takalleshi tad'ago, baya tayi da Sauri tareda zaro ido, cikin Rawar murya ta ce, "sannu da dawowa. Khairiyya da khursiyya suka d'ago alokaci d'aya suma suna kallonsa. Amamakinsu saisukaga yayi murmushi tareda fad'in lallai yarannan gaba d'a film yatafi da

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});