Chapter 57
Chapter 57
haka yakeyi. Dammmmm safna taji gabanta yafad'i, azuciyarta ta ce, "soyayya kuma?, wani kululun bak'in ciki yatokare mata mak'oshi ta had'iyeshi dak'yar, zamewa tayi takwanta visa gadon su khursiyya tana sauk'e ajiyar zuciya wadda su bama sukulaba hankalinsu nakan rigima akan wani wandon jins dakowa ya ce, " yanaso sukahau kokawa, can ALLAH yabama khursiyya sa'ar kwacewa daga hannun khairiyya ta sambad'a da gudu zuwa waje. Itama khairiyya ta take mata baya tana fad'in wlhy baki isaba saidai kowa yahak'ura mu badashi, daidai zasushiga d'akin Ammi bobo yashigo falon da sallama. Sanye yake cikin suit blue, komai na jikinsa blue ne amma banda belt da takalmi dasuka kasance jajaye, dressing d'in bak'aramin feeting d'insa yayiba, masha ALLAH. hannunsa yatura cikin aljihun wandonsa yajingina da kujera yana kallonsu khairiyya daketa zagaye falon batareda sunkula dashiba. Ganinfa bamasu gansaba yasakashi daka musu tsawa, kai!!! Wane irin iskancine wannan?, zaku maida mana gida filin polo?. Can suka tsaya suna mazurai, yacire hannunsa daga aljihu ya nunasu Ku nakula kafin kubar gidannan saina ta6a lfyar jikinku?, dannaga wani tashen iskanci kukeji yanzu?, to ubanmiye ya had'aku?!!. suduka saida sukad'an razana da tsawar dayayi, sukad'anja baya khairiyya ta CE, "Yaya wandonefa nad'auka shine ta kwace tagudo. Tsaki yayi ya ce, " wandon nawaye?. Da Sauri khursiyya ta ce, "nawanefa, itama khairiyya ta CE, " Yaya k'arya takeyi nawanefa. Kansa yadafe Dan suna Neman samasa ciwonkai ma wlhy... Ammi tafito ta ce, "miya faru kuma tom and Jerry?. Suduka suka nufi Ammi suna mata bayani..... Hannu Ammi tad'aga musu ta ce, " ainagaya muku kubar sayen Abu guda d'aya saboda gudun irin wannan ranar to gashinan kun saya kuma yanzu bawaje d'aya zaku kasanceba sannan kowa yanaso. Khairiyya tayi kwalkwal zatayi kuka, Ammi tafasan Nafi son wandon kuma nace ta d'auki rigar nitabani wandon amma tak'i yarda. Hannu bobo yamik'a ya ce, "kubani wandon.... Jikin khirsiyya na Rawa tamik'a masa, yana kar6a ya haura saman Appa batareda yasake maganaba. Khairiya tafara hawaye tana hararar khursiyya Ammi ta ce, " wlhy ALLAH yabaku sa'a kunsandai halin mukarram sarai ba bak'oku bane, idan darabon saiya zaneku kuna a amare kukuka sani, idan kunason kanku da arzik'in toku kama kanku danni babu ruwana wlhy, tana gama fad'a itama tahaye saman Appa. Jiki asanyaye suka koma d'akinsu, Safna ta kallesu tana fad'in kukuma lfy INA wandon?. Baki Khairiyya ta turo ta ce, "bataja ya Abdulmaleek ya kwaceba. Zumbur safna tamik'e tana fad'in yazone?. Basu tanka mataba Dan duk haushinsa ya ishesu. Itama bata saurari amsa daga garesuba tafito falon, jin k'amshin turarensa daya tafi yabari yasakata murmushin jindad'i, tasan yanzu yana wajen iyayensa danhaka tafito harabar gidan. Ganin motarsa yasakata k'ara sakin wani murmushin, bud'e gaban motar tayi tashige Dan bai kulleba. Shikam yanayanacan gaban Appa suna magana. Appa ya ce, "Mukarram tunda Alhaji sunusu dala yabada hak'uri miyasa bazaka hak'ura dakaishi koti ba, bakamar yanda kayi niyya tun farko ba?. Appa idan na k'yaleshi to bansan mizaimin agaba ba, badan ALLAH ya tak'aita wahalabafa nasan yaransa zasu iya kashe Rahma da Nawal alokacin nan, Amma shine yanzu zai dawo yana 'Yar murya wai ayi hak'iri, naga da ko magana baya maka amma dayake yanzu yasan miya shirya shine zaizo yay maka dad'in baki akan kahanani kaisa kotu?. Hakane mukarram amma ni aganina duk bak'in halin mutum idan yay nadamar kuskure dayayi to yanada k'ayau agafarta MASA tunda ALLAH ma muna MASA laifi kuma idan muka rok'eshi saiya yafe mana, amatsayina na mahaifinka INA rok'ama alhaji sunusi gafara agareka da iyalanka, daga nan idan yasake yunk'urin cutar dawani namu saika d'auki matakin daduk yadace bazan hanakaba saidai na taimaka maka akan hakan. Shikenan Appa zan yafe MASA to amma Alhaji Abdurrazak fa?, na tabbata tare sukayi k'ulle k'ullen sacemin mata da 'ya. Eh nasani Dan yafad'ami. Shinema yazugashi akan suyi hakan, to amma wani nacin arzik'in wani aii, to shima Alhaji Abdurrazak yaci arzik'in Alhaji sunusi. Shikenan Appa zanfad'ama Ammar karsu tura maganar kotu dama sonake agama bikinnan sannan mushiga kotu, tunda hakane zan fad'a MASA najanye amma akwai shari'ar damukeyi da Alhaji Abdurrazak akan kisan Barrister Lawan Usman D/tofa, da ake zargin su suka saka akasheshi akan wata shari'a daya tsaya da lauyansu kuma yasamu nasara. Ranar dayaje office d'ina danyimin gargad'i kuma yaso tabbatar min dahakan saidai bodyguard d'insa yak'atseshi. Ajiyar zuciya APPA yasauke ya ce, "a'a wannan bazan hanakaba kam Dan waccan shari'ar daban wannan daban Dan haka saidai nace ALLAH yabaka Nasara, Yakuma k'ara kareka daga Sharrin mak'iya da azzalumai, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka. Ammeen Appa, bobo da Ammi suka amsa. Daganan wani zancan suka d'akko. Bobo yakalli agogo tareda mik'ewa, Ammi Appa bara nashiga Office time na wuceawa kuma inada shari'a yau k'arfe 11:30. To ALLAH yabada nasara jarumin babammu. 'Yar dariya yayi yana k'ok'arin fita, to kugaidamin inna da Baba Dan bazan samu shiga wajensuba nayi latti. To zasuji idan sun fito. Ficewa yayi da hanzari, abakin k'ofa yaci karo da Idris tareda ya sulaiman zasu shigo. Tofa kukuma daga ina haka?, bobo yay maganar yana mik'amusu hannu, gaisawa sukayi cikin musabaha. Ya sulaiman ya ce, "yanzu nashigo muka had'u da idris zashi gaida su Ammi. Bobo ya maida kallonsa ga idris, ya karatu idris?. Alhmdllh yaya komai normal munata fama. To ALLAH ya taimaka, ni bara nawuce nayi latti. To ALLAH ya tsare yabada sa'a. Ameen ngd. Ya sulaiman ya ce, " yauwa idan katashi kuma Kannada lokaci plss kad'an biyo ta asibiti dama inason ganinka. Okey babu damuwa saina shigo. Okey saina ganka shima ya sulaiman yafad'a suna nufar ciki shida idris, shikuma bobo yafito. Motarsa yanufa hankali kwance yabud'e yashiga yana fad'in masha ALLAH yanzu kuma sai office. Idan ka gama dani ko?........ Da sauri bobo yakalli gefensa dan son ganin waye?. d'aure fuska yayi tareda fad'in miyasa kina shigarmin mota?, wama yabaki izinin shiga?. Wani murmushi Safna tasaki tareda k'ara lafewa cikin kujerar tana shak'ar k'amshin mortar da turaren bobo, tayi far da idanunta tana kallon k'yak'yk'yawar fuskarsa, aibasai anbani izinin shiga motar mijina ba, tayi maganar tana d'an d'aga gira. Kauda kansa yayi daga kanta tareda k'ara had'e fuska, ke banason k'aramin iskanci fitarmin amiota. Safna ta marairaice fuska harda hawaye, cikin muryar kuka ta ce, "Dan ALLAH ka saurareni wlhy magana nazo muyi kuma mai muhimmancice. d'agowa yayi yakalleta haryanzu fuskarsa ad'aure take, ganin tana kuka saikuma tabashi tausayi, bayason mutum yashiga damuwa akansa, yad'an huro iska daga bakinsa tareda kallon jan agogon fatar dake hannunsa 8:45, batareda ya kalletaba ya ce, " nabaki minti5 Dan inada abinyi. Hawayen fuskarta ta share ta ce, "wlhy minti5 yamin kad'an pls ka k'aramin. d'agowa yayi yad'an kalleta saikuma ya kauda kai, saidai ki hak'ura kuma saina taso daga aiki Dan yanzu haka nayi latti, so idan nadawo zanzo nan saiki sameni amma ki tabbata magarki tanada muhimmanci, kuma ki tabbata itace magana tak'arshe dazata shiga tsakaninmu daga ita kifita arayuwata, ina d'aga miki k'afane saboda banaso nazama silar rushewar zumincin iyayenmu, sannan bazan iya wulak'anta jinin Rahma ba, dan itama bata wulak'anta jininaba. Batareda yasake kallontaba yatada motarsa, ya ce, " sai anjima. Jiki a sanyaye Safna ta bud'e motar ta fito, hakan yayi daidai da fitowar ya sulaiman da idris. Suduka cikin mamaki suke kallon Safna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83