Chapter 35
Chapter 35
ALLAH mai k'yauta da k'ari aka silli6oki duniya, gatadai kinshashi fiye da kowa agidan, abinda kikeso shi ake miki, shiyyasa kika taso 'yargata ta6ararriya, wlhy tsiyar dakikeyi agidanku Inda Rahma takeyinta datuni tashiga wani hali. Amma harzaki bud'i baki kice anfison Rahma, duk Wanda yasan tarihin gidanku to bazai yarda da maganar kiba wlhy. Shiru Safna tayi, Dan tasan gaskiya Baseera tafad'a. Da hakadai suka k'arasa gidan malam da'u. °*°*°*°*°*°*°*°*°*°*° Tunda tatashi take hidimar gyaran gidan, bayan tahad'a breakfast tayima Nawal wanka tashiryata tsaf cikin kayan makaranta, tsaf yarinyar tafito tamkar kasaceta ka gudu, dama ga k'yau d'an asali, tana girma kamaninta nasake fitowa da mahaifinta. Rahma ta kalli agogo 7:6am, ta ce, "baby bara nayi wanka nima kafin papa yafito. To momy, Nawal tayi maganar tana k'ara gyara igiyar takalminta. Cikin d'an lokaci k'alilan tayi wankan tai shirinta cikin siket da riga 'yan kanti, d'an tsaki tayi Dan ganin rigar batada tsawo, aranta tace yanzu kanayin kuskuren d'aga hannu sai anga cikinka, da wannan mitar aranta suka fito falo. Harta zauna a dinning itada Nawal saikuma tamik'e Dan hangen labulen windown Kusada su ya nannad'e. Wani d'an kujera dake gefe wadda Bobo kan zauna idan baya buk'atar hayaniya ta janwo ta taka Dan tsawonta bazai kaiba, hawanta keda wahala koma labulen bata gyaraba tadai mik'a hannu zata gyara taji takun fitowarsa kwass kwass, tsintar kanta tayi da k'urama hangar tahowarsa idanu. Ya salam tafad'a yayinda bobo yabayyana, sanye yake cikin wando dariga farare tas, ya d'ora rigar suit jaa mai laushi, takalminsa agogonsa duk jajayene, sai zabga uban k'amshi yakeyi, sajen nan yakwanta luf luf sai shek'i yakeyi. Tashagala sosai akallonsa batareda tasaniba, shima gareshi hakan take, tsaye yake k'yam tamkar andasashi, idonsa nakan farar fatar cikinta data bayyana sakamakon d'aga hannu datayi zata gyara labulen daya nannad'e. Ganin ya motsa yasa ta firgita, abisa tsautsayi kukerar tad'an goce tayi baya kamar zata fad'i amma tayi nasarar rik'e k'arfen window. Ahankali yatako har inda take, fuskarsa babu yabo babu fallasa, baya murmushi bakuma a d'aure takeba, ahankali yayi maganar tamkar bayaso ko ammasa dolene. Mikike kallo haka? Dahar kike shirin fad'uwa?. Turo baki Rahma tayi, danta gaji wlhy, gashi Idan ta ce, "zatayi yunk'urin sauka fad'owa zatayi, Dan kad'an k'afarta take d'ofane akujerar. Yanda ta turo baki cikeda shagwa6a saita k'ara burgesa, dama ga kwalliyarta ta tafi dashi, yad'an lumshe idanunsa ya bud'e akanta, bazakiyi maganaba ko?, Ashe zan barki kifad'o d'iyarki tamiki dariya, yayi maganar yana kallon Nawal da hankalinta baya kansuma gaba d'aya, wasanta takeyi da cokulan da Rahma ta ajiye a dinning. Dawo da kallonsa yayi ga Rahma, cikin sanyin nan NATA tareda shagwa6a ta ce, " ALLAH hannuna zai karye please help me. Wani k'asaitaccen murmushi yayi tareda ajiye jakar aikinsa, yatura hanuwansa duka biyu a aljihu, idan na taimakeki kedami zaki biyani?. Shiru tayi tana kallonsa, can kuma ta ce, "mikake so nabaka amatsayin ramako?. Yad'an d'age kafad'a yana ta6e baki, nikomi kika bani fine. Ta marairaice murya tamkar zatayi kuka, ALLAH nagaji zan fad'o. Kauda kansa yayi gefen Nawal yana murmushi, ganin har yanzu hankalinta baya kansu yad'auke kai. Matsowa yayi Kusada Rahma tareda zare hannunsa daga aljihu ya tallafota, daga ita harshi lumshe idanu sukayi, tallafota yayi tamkar jaririya, ahankali yabud'e idonsa akanta, amma ita har yanzu nata alumshe suke, yakalli k'irjinta dayayi d'as a pink d'in rigar, ajiyar zuciya yasauke sannan yadireta ak'asa, saiyanzu tabud'e idanunta masu matuk'ar burkitashi, thanks tafad'a tana k'ara juya idanun. Shi ganima yake tamkar da gayya tamasa haka, lumshe idanu kawai yayi yana jinjina kai Dan bakinsa yayi masa nauyi, cikin salonsa ya ce, " nawafa?. Ta ce, "me?. Ramakona mana, kokin manta da yarjejeniya mukayi. Kauda fuskarta tayi gefe Dan bazata juri kallonsaba, mikaso to?. Abu biyune kawai, kuma marasa wahala. Kafad'a inji idan zan iya. Nafarko dai gyaran d'akina, Dan yayi datti, nabiyu kuma..... Saikuma yayi shiru, tajuyo tana kallonsa miye na biyun?. Wani murmushin basarwa yayi, murya kasa k'asa ya ce, " kiss me". Idanu tazaro, saikuma tajuya zata gudu, da Sauri yadamk'o hannunta, tsayawa tayi cak amma takasa juyowa..... Momy papa!!!!. Zanyi latti fa..... Muryar Nawal ta riski kunnuwansu, da Sauri yasaki hannun Rahma, itama tayi Saurin k'arasawa ga Nawal. Break fast tashiga had'a musu, Bobo yak'araso dinning d'in, kujera yagyara tamkar zai zauna yakai bakinsa Kusada kunnen Rahma, kitabbata idan nadawo saikinyi, inba hakaba zanmiki abinda yafi kiss. Kafin tad'ago yaja kujera ya zauna. Dukta daburce, itafa mamaki bobo take bata cikin 'yan kwanakinnan, tamkar bashiba, awaje idan kagansa dolene kaji tsoronsa da masa kallon mutum mai Girman kai da tsabar shariya, amma daka zauna dashi nad'an wani lokaci saika fiskanci shi mutumne mai sauk'i da iya zama da mutane, tasauke ajiyar zuciya tareda tura musu abincin kowanne agabansa. Sunacin abinci yana mata munafukin kallon nan nasa, dukta takura awajen, adaddafe dai aka kammala suka mik'e. Takama hannun Nawal suka fice shikuma yana binsu abaya har wajen mota. Rahma ta rissuna taima Nawal kiss akumatu kamar yanda tasaba, itama Nawal Tamata, bobo yak'araso yana fad'in saura ni. Shiru Rahma tayi tamkar bama tajishiba, bata ankaraba taji yabata summba (kiss) akumatu, dasauri tad'anja baya tareda lumshe ido, saikuma tajuya dagudu zuwa cikin gidan. Murmushi yayi tareda binta da kallo harta shige ciki, shima yabud'e mota yashiga yana murmushi. Saida yafara ajiye Nawal amakaranta sannan yanufi wani waje. Adaidai wani k'ofar shago yatsaya, batareda yafitoba, yamik'a hannu ta windown shagon aka mik'o masa wasu takardu. “banga fuskar wayeba nima.” burka motarsa yayi yay gaba yana bin karatun alkur'anin dake tashi amotar ahankali. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Su Safna sun samu shiga wajen malam da'u, bayan gaisuwa ta labarta masa yanda komai yafaru tundaga randa suka bar wajensa, duk cikin matsanancin kuka takeyin bayani. Shima Kansa malam da'u yarazana dajin batun na Safna, amma dayake yana son cin kud'i saiya dake abinsa. Ya ce, "toke yama akayi haka tafaru dake kika kamu dason mijin k'anwarki?. Safna tashare hawayenta, cikin rawar murya ta ce, " malam katuna da labarin farko Dana Baka, saikuma kahad'a Dana yamzu zakagane bansan *_“ABADUL-MALEEK”*_ BOBO me iyayena sukaso na auraba, sai yanzu daga baya. Jin jina kai malam da'u yayi, ya ce, "lallai kinyi Sake yarinya, amma zanyi iya bakin k'ok'arina Dan ganin kin mallakesa, Dan naga itama bata sonsa shima haka, Dan haka zamuyi nasarar rabasu cikin sauk'i, kid'aukama kinzama matarsa kawai. Wasu kayan tsubbunsu yabata, yamik'a mata wani ruwa a 'Yar jarka, ga wannan duk yanda zakiyi to kiyi Dan yasha abunnan, wannan kuma acikin abinci, sau uku zakiyi duka, Indai har yaci Yakuma sha tozaice ke yakeso, kuma zai saki k'anwarki. Wannan kwallin kuma kiringa sakawa a idonki, kiyi k'ok'ari kuma Ku kalli juna ido cikin ido. To malam ngd sosai Safna tafad'a tana washe baki, to amma malam duk tayaya zanyi wannan aiki nida ba gida d'aya mukeba?. Malam yayi dariya, kekam saikace ba maceba, kiyi duk yanda zakiyi ki aikata, wannan yarage naki, nidai nagama nawa. Tunda suka baro gidan malam babu mai magana da wani tsakaninta da baseera, kowa da abunda yake sak'ama zuciyarsa. Safna dai tunaninta nakan yanda zataci nasarar ciyar da BOBO wad'an nan magungunan. Amma zata gwada wata dabara tagani. *_(“ni bilyn Abdul na ce, " hummmmm, muje zuwa Safna.”)._* .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Jikake keyyyyyyyyyy yaja
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83