Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,185 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Tana idarwa tayi addu'a, d'an kallonsa tayi fuska a marairaice ta ce, "bacci nakeji". Da sauri ya ce, " zoki kwanta abinki my cute, ai yau ranarkice ke kad'ai. Tashi tayi tacire hijjab ta kwanta, shima yaje bayanta ya kwanta tareda rungumota jikinsa. Wata ajiyar zuciya tasaki, muryarta na rawa ta ce, "Dan ALLAH kayi hak'uri wlhy akwai wahala..... Tabashi dariya amma saiya gimtse, ya ce, " matsoraciyata kwantar da hankalinki kinji, barci zamuyi ni babu abinda zan miki. Dukda bata yarda dashiba amma tad'anji dad'i. Zuwa 'yan mintuna barci yakwashesu suduka............. πŸ’ƒβœˆ _jirgin so zaya tashi ked'ai ake jira 'Yar gata Rahman bobo kece da sarauta._πŸ˜‚πŸ˜‚ *Yau ranarkuce masoya Rahman bobo*β€β€β€β€πŸ˜˜πŸ™‹πŸΌ . δΊΊ . (___οΌ‰ . ┃口┃ . ┃口┃ . ┃口┃ . ┃口┃. δΊΊ. . ┃口┃. .-:'''"''";-. δΊΊ . ┃口┃(*(*(*|*)*))(__) ┃ - β”ƒβ•‘βˆ©βˆ©βˆ©β•‘. |口||┃ . ┃┃┃┃┃┃┃┃┃┃. |δΈ‰||┃ . ┃┃┃┃┃┃┃┃┃┃. |δΈ‰||┃ ​بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­Ω’Ω…ΩŽΩ†Ω Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­ΩΩŠΩ’Ω…β€‹ Its another yaomal jumu'ah! May Almighty Allah make it easy for us, purify our mind, put joy in our hearts , increase our iman, elevate us beyond our expectations.(Amin thumma Amin.) Juma'at mubarak.πŸ•ŒπŸ•ŒπŸ•Œ *_luv u oll_* *_(((S))).....2017_* [11/12, 2:57 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _β€’{πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύ}β€’_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* _Shafin nakune Biebie, Sawwama & Mrs Amaan gaisuwa da fatan alkairi agareku._ Luv u so much.😘 5⃣7⃣ *_8:30am_* Nawal tasakama Safna kuka ita wajen momynta zataje. Ita kanta Safna abin mamaki yake bata Dan ganin har tara saura Rahma bata fitoba, kota manta Nawal zataje makarantane?, dukda dai bobo yace mata batada lfy, amma yakamata ace tafito aii, jitai ranta yakuma 6aci, wata zuciyarta ta ce, "idan kin kwantar da hankalinki aii bobon yakusa zama naki gabad'aya....... Nawal ta girgizata, aunty naje wajen papa na tambayesa momyna. Safna tad'aga mata kai alamar eh. Bugun k'ofarne yasakashi farkawa, bobo yaja d'an tsaki sannan ya yunk'ura yatashi da k'yar, sakkowa yayi daga gadon yanufi k'ofar, wayene yay maganar dad'an haushi. Nawal ta ce, " papa nice. K'ofar yabud'e mata tashigo sannan yamaida yarufe. Papa ina momyna take?. Bobo yanuna mata gado da hannu, da gudu taje ta haye Rahma dake barci, momyna zan makara a school kitashi ki shiryani, kuma yunwa nakeji. Bobo yad'an zaro ido Shifa yama manta yau akwai aiki. Baby ya haka? Kosai kin tada momyn nakine?. Rahma tabud'e idonta ahankali, ganin Nawal akanta yasa ta yunk'ura ta tashi zaune, Nawal kin tashi?. Eh momy tund'azu natashi nake nemanki momy yunwa nakeji, kuma ba'amin wankan tafiya school ba. Bobo dake tsaye yana kallonsu cikeda sha'awa yakamo hannun Nawal yana fad'in kinga kibar momynki batada lfy kinji, makaranta kuma tunda yau juma'a ki hak'ura kawai dankin makara Tara saurafa. Kai Nawal tad'aga MASA, tamaida kallonta ga Rahma, momy kanki keyin ciwo?. Murmushi Rahma tayi tareda satar kallon bobo, ta ce, "kaina keyin ciwo amma na warke. Momy sorry, Nawal tafad'a kamar zatayi kuka. Murmushi Rahma tayi tareda jawo Nawal jikinta ta rungume, karki damu babyna nawarke aii, tashi muje namiki wanka..... Bobo yakatseta dafad'in no kwanta ki huta bara namata wankan, itada safna saina saukesu gidan Appa suje suwuni. Da Sauri Rahma tad'ago tana kallonsa, ta kwa6e fuska tamkar zatayi kuka, cikin muryar shagwa6a ta ce, " nifa?." Zama yayi kusada ita yakamo hannunta yarik'e anasa, kinga kibarsu sutafi tunda bakida lfy, Nima bazan dad'e awajen aikinba zandawo gida muyi zamnmu. Nidai ALLAH inason zuwa kumafa ni lfy ta k'alau, Rahma tayi maganar tana hawaye. Murmushi yayi yashare mata hawayen, itadai Nawal tana kallonsu, ganin papanta na sharema momyn ta hawaye itama tasa hannu tana goge mata, ta ce, "papa". Bobo ya ce, " Na'am. Papa kabar momy taje itama kaga tana kuka. Shafa kan Nawal yayi tareda fad'in baby aina barta, kutashi Ku shirya idan mukaje can saimuyi breakfast. Sakkowa sukayi, Nawal ta ce, "momy muyi wanka a bathroom d'in papa. A'a baby muje namu. Bobo ya ce, " saboda kina guduna. Ahankali yayi maganar yanda Nawal bazatajiba, Dan yakula yanzu dole su iya bakinsu agaban parrot d'innan. Babu yanda Rahma ta iya dole suka Shiga bayinsa, bobo yabi Rahma da kallo Dan ganin yanda take tafiya dad'an d'ingishi. Acikin 'yan mintuna suka gama shiryawa tsaf harda Safna, fitowarsu falo babu dad'ewa saiga bobo yafito cikin ash colour na shadda d'inkin zamani yayi k'yau sosai, Safna tashagala da kallonsa kuwa, jitake tamkar ta rungumeshi amma babu damar hakan. Rahma tanufi kichin danta rufe k'ofa, bobo yabita da kallo dantayi MASA k'yau dukda dogon hijjabine har k'asa ajikinta, tafito tanufosu safna ta ce, "waike lfyarki kuwa kike tafiya haka?. Cak Rahma tatsaya amma takasa cewa komai, bobo dake latsa waya yad'ago yakalli Rahma sannan ya maida kallonsa ga Safna ya ce, " bana fad'amiki batada lfy ba. Okey namantafa, Safna tayi maganar cikeda rainin wayau, Dan ita bata yarda Rahma batada lfy ba. Bobo ya maido kallonsa ga Rahma my cute badai haka babynki zata Fita babu d'ankwaliba?. Rahma takalli Nawal dake zaune akujera tana wasa da filoliwa ta ce, "nabata gyale bansan INA ta ajiyeba, Nawal ina mayafinki?. Nawal tad'ago tana kallonta, ta turo baki ta ce, " momy nibanason gyalen Nafi k'yau ahaka. Tsawa bobo yadaka mata zakitashi ki d'akko kosaina zanekine?. Da Sauri Nawal tamik'e zatayi kuka, Rahma tarik'e hannunta kinka fad'amin bakison wancanne na canja miki wani?. Kai Nawal tad'aga mata tana satar kallon baban ta. Bobo ya harareta Yakama hangar Fita dama Safna tafita, to kinga bisu naje nad'akko miki. Bobo yak'arasa ga mota yabud'e yashiga, wuf Safna tabud'e gaban itama tashige, k'ala baice da itaba saima k'ok'arin tada motar dayakeyi, Nawal tabud'e baya tashiga tana satar kallonsa Dan bataso yadaketa. Babu dad'ewa saiga Rahma tafito da farin siririn gyale ahannunta, takulle k'ofar falon tanufosu, tunda ta taho ioon bobo na kanta jiyake wata k'aunarta nak'ara ratsashi, ga wani k'yau na musamman dayaga yau tak'ara masa. Koda tak'araso taga Safna agaban motar batako kallesuba takama k'ofar baya zata shiga. Bobo ya ce, "dawo gaba. Kallonsa Rahma tayi, yanda yaymaganar babu wasa afuskarsa kuma ba ita yake kalloba, a ranta ta ce, " to a INA zan zauna?, afili kuma saitayi shiru tana kallonsa. Ya ce, "bakijini baneba?. Ta ce, " naji amma a INA zan zauna?, badan Nawal dake motarba dasai yafad'i abinda zai saka Safna FASA binsu amma ALLAH ya taimaketa bazai iya kowace maganaba agaban d'iyarsa. Duk abinda ke faruwa Safna nagaban mota ta kacire kamar motar mijinta. Bobo yawatsama Rahma wani kallo, muryarsa cikeda gargad'i ya ce, "madam kina 6atamin lokacifa kuma kinsan office zanje." K'ofar Rahma takama tabud'e Safna tad'ago ta kalleta suka kalli juna, badai ta ce, "komaiba amma fuskarta tanuna alamar bak'inciki. Rahma tadaure ta ce, "aunty kifito kikoma baya Dan ALLAH. Cikin masifa Safna tabud'e Baki zatayiwa Rahma magana, saidai kuma komi tatuna saita FASA ta fito, tad'an bangaje Rahma tabud'e baya tashiga. Itama Rahman gaban tashiga. Bobo yagirgiza kai kawai dama yayima Rahman hakane danyafi son taringa takwatarma kanta 'yanci awajen Safna. Ahankali yake tuk'in tamkar bayaso, wayarsace tafara wringing, yad'auka yana fad'in malam miye nawani kirana da farar Safiya?. Dariya ammar yayi, ya ce, "ho d'an duniya basaika nunamin ka girmaba aii. Shima bobo dariya yayi ya ce, " ALLAH Ammar bakada mutumci, yanzu nan nine kakecema sai yanzu na girma?. Hhhhhh eh mana, kaima

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});