Chapter 29
Chapter 29
Rahma tamik'e da sauri Nawal tafad'a jikinta, d'agata tayi tana juyi da ita afalon suna dariya. Hayaniyarsu ce ta tada Bobo, yamik'e dak'yar Dan Marar tasaki saidai zazza6in shima kad'an, falon yafito, sukam bama su gansaba sunata murnar ganin juna itada Nawal d'inta. d'an murmushi yayi yashige d'akinsa, ko babu komai yanajin dad'in yanda Rahma take kula masa da yarinyarsa, idan ba fad'a maka akayiba bazaka ta6a cewa ba ita ta haifetaba, saidai kawai idan ka kalli Rahma d'in zakaga yarinyace batakai ta haifi kamar Nawal ba, ammafa duk wata kulawa irin ta uwa akan d'anta Rahma tana k'ok'arin bama Nawal, kuma har zuciyarta takeson yarinyar. Kama hannunta tayi suka shiga d'akin, tabi gadon da kallon mamaki to ina yaje?, tafad'a azuciyarta, tad'an lek'a bayi daga nesa taga wayam, inaga to yana d'akinsa. Da wannan tunanin tacirema Nawal kayan makarantar. ‘Nawal!.’ Na'am momy. Kije d'akin papa kigani barci yakeyi, idan barci yakeyi muje can namiki wanka. Lah momy bayinmu fa?. Akwai ojuju aciki ina tsoron shigane. Kai, momy kema kinajin tsoron Ojuju. Dariya Rahma tayi ta ce, "kinga kedai jeki duba kidawo. Tamata hakane Dan tambayar ta tsaya haka. Da gudu Nawal tafita sai d'akin Papanta. Fitowarsa kenan daga wanka, yana zaune abakin gado yana shafa mai, Nawal ta shigo aguje tafad'a jikinsa. Uccch yafad'a yana rungume Nawal d'in, saboda yaji zafi data fad'a jikinsa. baby bana hanaki guje²n nan bane?. Sorry papa nadaina. Yalumshe idanunsa yana kad'a kai, toya School?, harkun dawo?. Eh papa, tad'ago tana kallonsa, papa kaima bakada lfy kamar momy?. Kallonta kawai yakeyi yakasa magana, ta girgizashi kaji papa, ajiyar zuciya ya sauke, a'a baby lafiya ta k'alau, itama momy aita warke ko?. Eh mana ta warke, yanzuma catayi Nazo naduba idan kana barci saitazo tamin wanka a bayinka, wai bayinmu akwai ojuju tanajin tsoronsa. Papa dama idan mutum yay babba yanajin tsoron ojuju?. Bobo dake shafa mai yanajin zancen Nawal yayi murmushi, baby Momynki tacika tsaorene, amma zan koya mata yanda zata daina, jekice mata tazo tamiki. Papa nima zaka koyamin Dan nadaina tsoron ojuju d'in?. Eh zan koya miki, jeki kirata. Fita Nawal tayi kiran Rahma. Momy tahoto kimin. To Babyna, amma papa fa?, yananan ad'akin. Atunanin Rahma yana barci Nawal take nufi Dan haka takama hannunta suka fito zuwa d'akin bobo. Kanta tsaye tashiga d'akin, saikuma tatsaya cak Dan ganin bobo tsaye yana saka ma6alin rigarsa, baya tayi zata koma, batareda ya kalletaba ya ce, " kizo kimata wankan mana. Rahma tayi k'asa da kai kamar wata munafuka tanufi bayin rik'eda hannun Nawal. Shikam baki yata6e yad'auki brush yana k'ara kwantar da sajensa bak'i sid'ik, yak'ara fesa turare sannan yafice daga d'akin. Masallaci yanufa, saida yayo sallah yadawo sannan ya d'auki Jakar aikinsa daga fallo, yamanta a can yabarta, yacire laptop d'insa da wayoyi ya ajiye a tebird'in tsakkiyar falon sannan yakawo jakkar d'aki Yakuma fita. d'akin Rahma yashiga, yanufi bayimta danya kashe matsa tsakar, dube² yahauyi, can yahangota kwance a bango, tsintsiya yasa yabugota tafad'o, Yakuma bugunta ta mutu, yawanke hannunsa yafito. Daidai nan Rahma tashigo d'akin itada Nasal. Batareda ya kalletaba ya ce, "gatacan na kashe saiki fidda. Tuni hawaye sun cika idon Rahma, kanta ak'asa tace, " Dan ALLAH ka fidda wlhy bazan iyaba. Eh tunda nazama yaronki ko?. A'a Dan ALLAH ka taimakeni nidai. Tausayi tabashi, yalura harga ALLAH tsoron tsaka takeyi, komawa yayi yasharota a faka, yay nufin tsokanar Rahma, danhaka gadan gadan ita yanufa. Ganin tsaka afaka kuma wajenta yayo tadaka tsalle tareda kwallah k'ara. Tabashi dariya amma saiya gimtse saida yafita sannan ya shek'e da dariya harda rik'e ciki, mai gadi yana hangensa abin yabashi mamaki Dan yadad'e baiga Bobo yana dariya hakaba, dama dariya mai yawa ba sabon bobo bace, sai Abu yakai matuk'ar tik'ewa yake bashi dariya, murmushinma saiya gadama yakeyi balle dariya. Komawa yayi ya k'ara wanke hannunsa, sannan Rahma tana shirya Nawal. Fallo yadawo ya kwanta saman doguwar kujera. Ya d'auki remote ya canja tasha, babu dad'ewa suka fito suma, Nawal taje ta zauna kusadashi tana fad'in baby kamomin MBC 3 naga cartoon. Rahma ta ce, "Nawal mikikace?. Baki tarik'e kamar wata babba, momy yi hak'uri bazan sakeba, Dan ALLAH karkice kin fasa zuwa danifa. Zanje dake ammafa idan kin daina. To na daina, papa aidai yanzu bana cemaka baby ko?. Bobo yakalli Nawal yana kad'a kai, yamaida kallonsa kan Rahma data nufi dinning, murmushi yad'anyi. Baby ina momy ta ce, " bazataje dakeba indai kina cemin baby. Nawal takawo bakinta saitin kunnen Bobo ta ce, "catayi bazataje dani makkah da madina ba muga kabarin Manzon ALLAH. (S,A,W) BOBO yak'arasa mata, to baby yanzu kindaina cemin baby kenan?. Eh bazan sake fad'aba, momyna ta ce, " nace maka papa. Jawota yayi jikinsa ya rungume, yabata kiss akumatu, I luv u my baby. Itama ta ce, "luv u too my papa. Rahma tak'araso da kuloli ta ajiye a tsakkiyar falon bayan ta janye tebir d'in, saida tagama kawo komai sannan ta ce, "ga abinci.’ Mik'ewa yayi zaune yana satar kallon Rahma, itakam sai duk'ar dakai takeyi, yakula batason had'a ido dashi tun d'azu, ko kallan ma inda yake batayi. Haka suka zauna cin abincin Wanda Bobo kejin dad'insa. Yasani lokaci d'aya Rahma taja zuciyarsa rusuna akan burin daya d'auka nayi mata rashin mutunci agidansa harsai tagudu da k'afarta, yafara gudanar da shirinsa ta hanyar fita harkarta, hartayi tsawon kwana 8 a gidan bata ganshiba, amma daga randa yakawo Nawal gidan yaci girkinta sai zuciyarsa tayi sanyi da d'ora alamar ? Akanta. Abi na biyu shine son datake nunama gudan jininsa Zuh'ra (Nawal), wad'an nan abubuwan suntaka rawar gani wajen ganinta da mutumci da daraja, dukda har yanzu bazaice yana sontaba, ‘Dan Ni'ima ce kawai macen dazaiso aganinsa‚’’ to amma yabama Rahma wani 6angare azuciyarsa kad'an kodan k'aunar Nawal datakeyi.............wringing d'in wayarsane yadawo dashi hayyacinsa, yakalli Screen d'in wayar batareda ya d'aukaba, bak'uwar number yagani. Sharewa yayi yacigaba da cin abincinsa, aka k'ara kira akaro na biyu, nanma yay burus. Rahma ce tad'ago ta kallesa danjin ank'ara kiran wayar, cikin sa'a kuwa suka had'a ido, tai saurin janye nata, shikuma yad'an lumshe idanunsa. Ba'a sake kiran wayarba harsuka kammala cin abincin Rahma tagyara wajen. Saman kujera yakoma ya zauna, yad'ora kafafunsa saman tebir, yad'auki laptop ya d'ora saman cinyarsa yana Dane dannensa na fama. Rahma kam homework take koyama Nawal. Falon yayi shiru kowa yana harkar gabansa sai k'arar TV kawai Dana AC, Wayar d'azuce dai aka k'ara kira. Wani wawan tsaki Bobo yasaki, afusace yad'auki wayar yana mita, wai miyasa mutane suke San takuramin ne?, ina gidan nawama baza'a barni nahuta da iyalina ba mtsooooow. Rahma dai tana jinsa bata d'agoba, aranta tace su iyali manya. Wayar yad'auka yasaka akunnensa batareda yayi maganaba............. _humm kowaye yakira Bobo ne?._🤔 _muje zuwa masoyan Bobo & Rahma, abinfa yafara zuwa, Dan kunsan dai akwai matsala Safna tagane bobone mijin k'anwarta, kuma Wanda taguda adaliln son Bobo d'in, hum akwaifa cakwakiya wlhy, baridai nabarku karna cikaku da magana🙊......_ *_Luv u oll my fan's_* *_(((S))).........2017_* [11/12, 2:54 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* _shafin nakune, gaisuwarma takuce, *Saffiya Galadanci, classic Feedo, & Sajna.* gaisuwa agareku mai tarin yawa da fatan alkairi, ngd sosai da k'auna, nima ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83