Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

imaninku ko sallama bakwaji ko?. Wlhy Yaya bamusan kashigoba sannu dazu. Murmushi yayi tareda nufar d'akinsa. Khairiyya ta kalli Rahma, auntynmu yaufa mijinki yana cikin nishad'i wlhy. Rahma tad'anyi murmushi, nimadai nakula da haka khursiyya, komiye yasakashi nishad'i?. Dariya sukayi gaba d'aya, Rahma ta tashi dukda zuciyarta na dukan Tara Tara Dan kwana uku kenan baya cikin wata walwalar kirki, amma yau gashi yashigo musu cikin nishad'i, ruwa ta d'auka da cup tanufi d'akin. Ahankali tayi Knocking kamar bataso. Yana kwance akan gado fuskarsa cikeda nishad'i, yau jinsa yake sakayau dashi, jin Knocking d'in k'ofa yasashi juyawa tareda amsawa, ya ce, " shigo mana. Rahma tashiga a sanyaye tareda yin sallama a can k'asan mak'oshinta. Fararen idanunsa yad'ago yana kallonta, yad'an lumshesu sannan yabud'e akanta, hakan yayi daidai da rank'wafowarta zata ajiye masa tiren agabansa, wani nannauyan numfashi ya sauke yayinda idanunsa sukayi tojali da k'irjinta daya bayyana saboda wuyan rigar babbane. Itakam dabatasan miyakeyiba ta tsiyaya ruwa akofi tad'ago zata bashi, kallo d'aya tayi. Masa ta kauda kai Dan ganin yakafeta da mayun idanunnan nasa masu hasken tsiya. Ya lashi le6ensa nak'asa tareda kar6ar kofin tamkar wani soko, tana bashi takama hanya zata fice yay saurin damk'e hannunta. Gabantane yafad'i amma bata juyoba, shima baiyi maganaba hasalima ruwansa yake sha idonsa kuma akan TV dake manne abagon d'akin, sunkai minti uku ahaka sannan ya ajiye kofin hannunsa yadawo da kallonsa kanta, bayanta yakebi dakallo aransa ya ce, "yarinyar tanada sura mai k'yau saidai tacika yarinta..... Mutsu mutsun kwacewa da takeyine yadawo dashi hayyacinsa, yakuma rik'e hannun nata sosai, cikin muryarnan tasa mai sanyin dad'i ya ce, " jimana. Maganar tabama Rahma dariya wai jimana saikace Wanda yaga budurwa a hanya, shiru bata juyoba danhaka shikuma yamik'e, haryanzu hannunta yana cikin nasa, yamatso daf da ita hartanajin saukar numfashinsa akan bayanta, tad'an runtse idanunta Dan idanhar bobo yakusanto ta takanji tsigar jikinta tana tashi.... Bata k'are tunanin nataba taji yarungumota ta baya, yazagayo da hannayensa duk biyu saman cikinta, jikintane yakama rawa cikin rawar murya ta ce, "pls kayi hak'uri su khursiyya suna jirana a falo. Murmushi yayi tareda kawo bakinsa Kusada kunnenta muryarsa tayi low sosai can k'asan mak'oshi ya ce, " wato su khairiyya sunfi mijinki muhimmanci ko?, yanda yay maganar akunnenta sai duk ta dabarbarce, tajuyo akid'ime, kallo d'aya tamasa gabanta yafad'i, Dan ganin fuskarsa ta canja hartayi d'anja, hakama idanunsa sunyi ja, girgiza kai tayi tana fad'in bafa haka nake nufiba, munayin girkine Dan Nawal takusa dawowa daga school. Baki yad'an ta6e yana jinjina kai, idonsa akanta ya ce, "aikinga anraba kenan, su khairiyya sukula da Nawal, kekuma ki kula da baban Nawal ko?. Rahma tak'ara kasa da kanta, shikuma yayi murmushi tareda saka yatsunsa biyu yad'ago ha6arta, lumshe idanunta tayi, shikuma yashiga Raba idanu bisa k'yak'yk'yawar fuskarta, muryarsa ta canja Dan akasalance yake magana, ya ce, " Abu d'aya zakimin nabarki ki tafi. Da sauri tabud'e idanunta ta ce, "minene?. Gira yad'aga mata yana wani kasa k'asa da idanu, kibiya bashin danake binki na kiss, dankinsanfa ni bana mantuwa. Zaro idanu Rahma tayi, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka, Dan ALLAH kayi hak'uri wlhy bazan iyaba. Yakuma narke murya to saboda mi?. Inajin kunya. Kunya kuma?. " eh". Lallai kinada aiki, dole ki shirya zama mara kunya kuwa indai kina taredani, danni mutumne dabayason kauce², sak nake kuma komai nawa sak yake, inaso da sauri shiyyasa nakasance mai sauri, inaso da k'arfin zuciya shiyyasa nakasance mai dakakkiyar zuciya, inayi da yak'ini shiyyasa nakasance mai nasara, inayi da ikilasi shiyyasa ubangijin al'arshi yake taimakona adukkan al'amurana, kizama jaruma sai duniya tasanki, kizama mai gaskiya sai azzalumai suji tsoronki, kizama mai zuciya saiki kasance mai k'arfi, kizama mai hak'uri saiki ganki dayawan riba, kizama mai tunani saikomai naki yazama namasu hikima da k'yak'yk'yawan tunani, Abdulmaleek nakowane amma bakowa bane na Abdulmaleek, 'yammata karki tsaya kallon ruwa kwad'o yamiki k'afa, kizama mai jarumta dankiyi nasarar maida jiyana da yau da gobena duk suzama naki kekad'ai da 'yayanmu. Yana gama fad'ar haka yasumbaci kumatunta tareda sakinta yashige bathroom. Kamar sokuwa haka Rahma tabishi da kallo harya shige, sai juya maganganunsa takeyi aranta da k'arfin tunani da kwanji, amma kaf tarasa fassara ko guda d'aya aciki, tama rasa inda maganganun suka dosa, takai tsawon minti 6 awajen tsaye amma takasa fasa koda magana d'aya aciki, takuma kasa barin wajen, shikuma har yanzu bai fitoba. Ahankali tafice tamkar munafuka, tunda tafito su khairiyya kebinta da kallo suna k'unshe dariya, tazauna tana binsu da kallon mamaki, khursiyya tamatso Kusada Rahma tana shinshina jikinta, dariya sosai khursiyya takeyi, Rahma ta ce, "wai miye abin dariya?. Cikin dariya khursiyya ta ce, " a'a babu komai nadaiji kinata zuba k'amshin turaren ya Abdulmaleek ne. Da sauri Rahma ta shinshina kayanta, ilai kuwa kamshin turaren bobo takeyi, da sauri tamik'e tashige cikin kichin, khursiyya da khairiyya suka shek'e da dariya harda tafawa. Itadai Rahma tana kichin itama dariyar takeyi k'asa², lamarin bobo yana bata mamaki wlhy............. *_luv u oll my fan's_* *_(((S)))..........2017_* [11/12, 2:56 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{🅱🅾🅱🅾}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 5⃣0⃣ Tana cikin kichin zaune danta kasa fitowa, jitake kamar su khairiyya sunsan miya faru, ihun Nawal ne yasakata fitowa dole, tasaki su khursiyya tanufo Rahma da gudu tarungumeta tana murnar ganinta, tana cikin cire mata uniform bobo yafito sanye cikin farar jallabiya, Shima Nawal taje ta rungumesa, yad'agata sama yana fad'in babyna yaushe kika dawo?. Papa yanzun nan. Toya school?. Lafiya lau my papa. To masha ALLAH sauka naje masallaci yafad'a yana direta k'asa, ya kalli Rahma datun fitowarsa tayi k'asa da kai, ya ce, "bara naje sallah. Saika dawo tayi maganar kanta ak'asa. Baice komaiba yafice. Yaudai haka Rahma tawuni atakure Dan duk inda tayi idon bobo yana kanta, ko kunyarsu khursiyya bayaji. Bayan sallar isha'i yashirya zai maidasu khairiyya Nawal tamak'ale wai saitaje, harsun fita yaturo Nawal takira Rahma itama tazo su tafi. Murna tayi sosai Dan dama tsoro takeji wlhy. Abaya ta tararda su khursiyya, dole tabud'e gaba tashiga, har Nawal zata shigo gaban ya ce, " takoma baya, Rahma tadaure ta ce, "pls kabarta muzauna aii zai ishemu. Baice komaiba yatada motar, saida yafita daga gidan sannan ya ce, " kina 'Yar lukutarnan ne kujera d'aya zata isheku?. Da sauri tajuyo tana kallonsa, amma shiba ita yake kalloba, idonsa nakan titi, d'an harara tamasa tareda murgud'a bakinta..... Babu zato ya ce, "nikikema murgud'e da harara?. Kanta tadafe Dan batasan yana kallontaba, aranta ta ce, " kai mutumin nan ya iya munafikin kallo wlhy, afili kuma ta ce, "nifa ban hararekaba, tak'are maganar da turo baki gaba. Murmushin gefen baki yayi batareda yace komaiba. Tunda suka shiga harabar gidan sukai karo da motoci reras, wannan alamace ta basawan gidan duksun zo kenan, shima guri yasamu yay fakin suka fiffito. Yana gaba suna biye dashi, da sallama suka shiga falon daya k'awatu da haske. Ya sulaiman ya ishaq ya Hamza duk suna gidan, hannu bobo yashiga basu suna gaisawa, su Rahma ma suka gaishesu tareda hayewa sama Dan gaida Ammi. Ya Hamza ya ce, " kace tare kuke gaba d'aya, bobo dake k'ok'arin zama ya ce, "yana iya baby tamak'ale saitazo, nikuma bazan iya barin Rahma ita kad'aiba shine na ce, kawai

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});