Chapter 73
Chapter 73
Murmushi mai sauti Rahma tayi cikin salonta ta ce, "Normal Muke, kaima muna fatan kasancewarka cikin kuzari da jarumta irin na ma'aikacin kwarai mai k'ok'arin kare hak'in al'ummarsa?. Alhmdllh my Nusfulhayat duk abinda kike hasashe agareni ALLAH yasaukar da ni'imarsa agareni musamman dakika kasance mai yawan tunatar dani waye ni akowane dak'ik'a na rayuwata. Masha ALLAH Rahma tafad'a murya anarke. K'ara lumshe idanunsa yayi dak'ara lafewa cikin kujerar yanad'an lilakansa akujerarsa alamun yanajin dad'in yanayi da hirar dasukeyi, ya ce, " mikikecine haka kiketa faman shan yaji?. Dariya mai Narkar da zuciya Rahma tayi ta ce, ''canki mana." Shiru bobo yayi yanad'an nazari, zuwa can ya ce, "tom saidaifa muyi da sharad'i?. Hummm sharad'in mi?. Idan na canka dai-dai to yaufa babu k'orafi awajen barci, dannaga wani guduna akeyi yanzu. Dariya mugunta Rahma tayi ta ce, " nayarda Dan nasan bama canka zakayiba. Shima dariyar yakeyi ya ce, "kardai ki cika baki. Batace komaiba saidai tayi murmushi. Shima shiru yayi yana tunanim mizaice?. Rahma tayi gyaran murya. Ai kamar ta zurgud'a masa allura ya ce, " d'anwake kikeci. Shiru Rahma tayi, shikuma shirun datayi yabashi damar tuntsurewa da dariya yana fad'in naci gari, yarinya yau ki shirya babu d'aga k'afa. Kukan shagwa6a Rahma tasaka masa tana fad'in itadai bata yardaba. Dariya su Basma suka saka mata har bobo na jiyosu. Safna kam tsaki taja ta na kauda kai. Rahma tajuya baya danjin suna mata dariya, jin dariyar dayake mata shima yasa tadage akan bata yardabafa. Shima dagacan cikin dariyar ya ce, "ahaf 'yammatana ai babu hanyar ku6ta, kima shirya tarbata Dana tashi daga office zanbiyo mutafi gida nasha Amarcina yanda yakamata. Da sauri ta ce, " banida lfy fa. Karki damu inada magani, yana gama fad'a ya Yanke wayar yana cigaba da mata dariyar mugunta. Ameera tarik'e ha6a oni auta d'an koyamin shagwa6ar nan mana nima na iyata, Rahma tarufe fuskar tana dariya, Ameera ta ce, "yo ALLAH kanama mijinka wannan shagwa6ar ai babu inda zai fita, shiyyasa ya Abdulmaleek baya ganin kowa saike kad'ai. Tashi Rahma tayi tabar wajen suna mata dariya. K'arfe *_5:6pm_* bobo ya iso gidan, ak'ofar gida yatsaya yakira wayarta, alokacin Rahma ta na zaune kusada ummi tana zubamata shagwa6ar wai k'irjinta na ciwo, ummi tashafa kanta tana fad'in auta saidai hak'uri, ba'a Raba mai cikin da irin wad'annan k'ananun ciwuwwukan harsai anhaihu suke dainawa. Baki tad'an turo sannan tazame ta kwantar da kanta bisa cinyar ummi. Ummi ta ce, " sannu autana. Kanta tad'aga cikin salon shagwa6a. Dariya ummi tamata tana fad'in auta Abdulmaleek yana fama da wannan shagwa6ar taki, kekiyi Nawal tayi gakuma baby zaizo. Hannu Rahma tasa tarufe fuskarta tana dariya. Ana cikin haka kiran bobo yashigo, akunyace tad'auka tasa akunne batareda tayi maganaba. Bobo ya ce, "kifito muwuce ina mota." Cikin muryar kamar zatayi kuka ta ce, "wayyo ALLAH tun yamzu?. Haba my Nusfulhayat gobe idan ALLAH yakaimufa zaki dawo, nima atausayamin mana. Baki takuma zun6urowa tamkar zatayi kuka, shikuma dagacan ya ce, " inajiranki, ya Yanke wayar batareda yajira cewartaba. Lalla6ata ummi tashigayi Dan taji wayar dasukayi, mik'ewa Rahma tayi tashirya tanatama ummi shagwa6a harda 'yan kwanlanta, tayima mutane sallama tafito, cikin mota ta iskeshi, koda yashiga sallama kawai tamasa ta zauna tajuya masa k'eya. 'Yar dariya kawai yayi yatada mota suka tafi, shima baice da ita k'alaba har sukayi nisa, tuk'insa kawai yakeyi yanabin karatun alkur'anin dake tashi amotar cikin suratul Nurr. Itama Rahma tayi shiru tanabin karatun ahankali cikin k'ira'ar shiek Abdurrahman sudies, takula bobo yanason karatunsa. Koda sukaje gida bata tsaya jiransaba tabud'e motar tafice abinta, binta yayi da kallo yana wani shu'umin murmushi, shima fitowa yayi yakwashi tarkacensa ya take mata baya. Afalo ya isketa kwance akan 3sita, tana ganinsa tafara cije le6e. Dariya tabashi Dan yasan sarai pretending ne datasaba masa a 'yan kwanakinnan, baisan miyasa yanzun batason yara6eta dasunan auratayyaba. Yi yayi kamar bai gantaba yawuce d'akinsa, harya kai k'ofa ta ce, "wai Nurulk'albi yaushe zaka d'akko mana Nawal ne?, wlhy nayi kewarta gidan babu dad'i kuma. Bakinsa yad'an ta6e cikin zolaya ya ce, " sai randa momynta tabar guduna, baki ta turo shikuma yashige d'akinsa yana murmushi. Itama mik'ewa tayi tanufi d'akinta, suduka kowa wanka yashiga. Bobo yana fitowa ya tsane jikinsa ya zira jallabiya yafito, d'akin Rahma yad'an lek'a, daga bakin k'ofa ya ce, "My Nusfulhayat natafi masallaci. Kanta kawai tad'a masa tana cigaba da tsane ruwan jikinta, Dan fitowarta kenan daga wanka itama. Bai shigoba sai bayan isha'i, tana zaune afalo daga ita sai wando na jins pink iya cinyarta tasaka best fara tas sai tashin k'amshi takeyi. Kallo d'aya bobo yamata ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, sannu tamasa, ya amsa yana lumshe idanunsa, d'akinsa yanufa, mintuna kad'an yafito dagashi sai gajeren wando da best, hannunsa d'aukeda laptop da wayoyinsa, zama yayi kusada ita yasaka hannu afilet d'in kayan marmari datake sha. d'ago ido tayi tana kallonsa, yad'aga mata gira tareda kanne idonsa d'aya. Kauda kai tayi gefe tana murmushi, zuwa can kuma ta ce, " Nurulk'albi serious ina kewar babyna fa. Hannunsa na haggu yasa yatallafota zuwa jikinsa, yankan abarba yad'auka yasaka mata abaki, ya ce, "nima ina kewarta my cute amma haka zamu hak'ura tak'arasa hutunta a can, kullum k'orafin mama ba'a kaimata Nawal Hutu, shiyyasa wannan karon nace taje ta musu kwana biyu, tokuma gashi sun rik'e mana ita, d'azuma sunzo office d'ina itada musaddiq, kiyi hak'uri kinji, data kammala hutun zata dawo garemu, Nawal batada wata uwa aduniya sai ke kinji. Kanta tad'aga tana masa murmushi, yacigaba dabata fruit d'in yana fad'in har andaina fushin?. 'Yar harararsa tayi cikin sigar wasa, ta ce, " aikasan bana iya fushi dakai Nurulk'albi, soyayyarka ta mamaye dukkan jikinna da 6argo ruhina da jinina, wad'an nan matakan tsaron daka gark'ame ilahirina jikina dasu basa Barin masarautar zuciyata dogon fushi dakai, inasonka dayawa bobona, har zuciyata tanayi tamkar zata faso daga k'irjina zuwa gareka musamman alokacin data nisanta da 'Yar uwarta. My zumana kai namusamman ne, kai jarumine acikin jarumai, kai gwanine acikin gwanaye, kazama zaki acikinsu, tutar nagarta na hannunka kad'agama sauran maza saidai subika abaya kosunaso ko BASA so kuwa..... Wani sanyin dad'ine yaratsa zuciya da 6argon bobo, yad'uki filet d'in kayan fruit d'in ya ajiye saman Santa tabir, k'ara matsota yayi jikinsa yashiga nuna mata zallar k'auna da zazzafar soyayya mai cikeda alfahari gaduk macen data sameta ga mijinta, sunkai rabin awa yana Abu d'aya, Rahma kam tana k'ara harhad'o hanyoyi da gudummawa na taimakonsa, sun lula basajinkira, gabansu kawai suke hange amma ba bayaba, saida suka nutse bisa tirbar soyayya kowa yakuma yarda da jarumtar nagartacciyar soyayya daga d'an uwan nasa sannan suka tsagaita tareda tsurama juna shu'umin kallo kowa na zubda kwallar farinciki da ni'imtaccen so tsaftatacce kuma gawurtacce. Rungumeta Yakuma yi yana lashe dukkan hawayen dake zirara bisa kumatunta tareda shiryamata nutsatstsin kalamai masu nisan kiwo ga ballagazar mace. Bayan ya sarara itama talashe nasa tas suna mai k'ara dulmiya cikin farinciki da nutsuwar kasancewa tare tamkar kowane ma'aurata dasuka kasance cikin inuwar aure. Bayan shud'ewar mintuna kamar ashirin suka 6ararraje a tsakkiyar falon, Rahma najikin bobo kwance suduka idonsu nabisa laptop d'insa dayake danne-danne da'alama yana aikin daya shafi office ne, Dan gaba d'aya daga ita harshi sun maida nutsuwarsu ga abinda yakeyine.. Sunkai tsawon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83