Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wani wawan birki da k'arfin tsiya Dan ganin wasu zaratan samari majiya k'arfi agabansa, sai faman huci suke suna mummurd'ewa, alamar jin karin k'aimi akan burinsu. d'an tsaki yaja tareda cije le6ensa na k'asa, afili ya ce, "wad'annan k'ananun karnukanfa nawaye?. “na ce, " hummmmm.” Murfin motar yabud'e cikeda Isa yafito, kuma fuskarsa tana nuna alamar hankalinsa kwance yake, yarufe murfin sannan yajingina ajikin motar, hannayensa yatura cikin aljihun farin wandonsa, ya hard'e k'afafunsa biyu dake sanye cikin Jan takalmi sau ciki mai k'yawun gsk, idanunsa sanye da siririn farin gilas, yad'an karkace kansa gefe yana k'are musu kallo d'aya bayan d'aya, shi dariyama suka bashi, Dan haka yasaki wani lallausan murmushi mai birkita ma'abocin kallonsa Wanda Ammar yasakama suna murmushin mugunta, Dan yafi bomb had'ari. Cikin muryarsa mai taushi da amo ya ce, ''yan samari halan lafiya dai?. Zaratan samarin suka k'ara babban k'aro k'irji gaba had'eda hura hancinansu danjin furucin BOBO maicikeda rainin wayo. d'aya daga cikin samarin ya ce, "lafiya idan kabamu abinda muke nema, amma babu lafiya idan kace zakayi kuskuren hanamu. Tofa, yafad'a yana k'ara sakin lallausan murmushi, lokaci d'aya kuma yahad'e fuska tamkar hadarin gabas, yasaka d'anyatsa d'a yajawo gilashinsa k'arshen hanci, saikuma yasakeyin murmushi, Yakuma gyara tsayuwarsa, ya ce, "to yan samari miye buk'atar taku?. Kallon juna sukayi Dan aganinsu yaji tsoro, nafarkondai yasake yin magana, d'an uwa takardun dake cikin motarka Daka kar6a yanzu muke buk'ata. 'Yar dariya yayi akaro na farko, yakai hannunsa na dama ya shafa lallausar k'asunbarsa ya ce, " tofa, aikin babbane Ashe, hannunsa yacire daga aljihu, yatako ahankali yak'araso har Inda suke, yakuma binsu da kallo d'aya bayan d'aya, sannan yamaida kallonsa akan mai maganar, Wanda nake k'yautata zaton shine ogansu. Cikeda Isa ya ce, "yan samari bayan takardu mikuke buk'ata?. Wata mahaukaciyar dariya babban yasaki, saida yayi mai isarsa, BOBO na tsaye yana binsa da kallo, shima yakalli BOBO cikeda izza ya ce, "d'an saurayi konace matashin lauya bama buk'atar komai bayan takardunnan dai, sukad'ai sun wadatar damu.............. Kafin yarufe baki yaji wani shegen naushi akumatunsa na haggu. Tuni oga yazube ak'asa a sandare, BOBO yabishi da kallo yana murmushi tareda shafa gemunsa na gayu, 'yan samari har wannanma bakwa buk'atane????. Gaba d'aya sauran zaratan samarin sukayo kan BOBO, wani juyi yayi akansu saiga biyu ak'asa. 🚶🏻‍♀sum sum nakoma bayan motarsa namak'ale kafin a maujeni👊🏻 kurasa mai d'akko muku rahoton kuma. Tabd'ijan masu karatu nifa azatona a film kawai ake irin wanga Abu, Ashe afilima anayi, cikin 'yan mintuna saiga 'yan samarin nan kwance ak'asa gaba d'ayansu. Daga mai karyayyen hannun saimai karyayyar k'afa, saimai zubabben hak'ori. Amma gwarzon naku ko zoben dake yatsansa bai fad'iba barema ayi zaton yaji ciwo. Yataka hannun wani yana tsaki mtsowwwwww shashashu k'ananan karnuka kawai.... Uban waye ya aikoku gareni??, Ku karnukan farautar wayeeeee!!!!!!?. Yay maganar cikin k'araji!!!!!.............. " wayyo masu karatu, tsawar BOBO tarazanani, tuni nakwasa da gudu na6uya bayan wata bishiya, inaga kuyi hak'uri kawai zuwa gobe idan nasamu nutsuwa saina idabaku rahon yanda BOBO yak'are da karnukan farautarnan kamar yanda yake fad'a musu........ *"_hummmmm kowaye ya aikoma BOBO 'yan daba?. Shin Safna zatayi nasara kuwa?, towai ma ta Yaya zata iya ciyar da BOBO wanga kayan tsubbu?._* Kudai kucigaba da bibiyar 'Yar mutan kanawa da katsinawa danjin yanda zata kaya. _bilyn Abdul ce😘👌🏼_ *_luv u oll my fan's_* *_(((S))).......2017_* [11/12, 2:55 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 🤝 *_Assalamu alaikum. Happy new Islamic year 1439AH. Wish you all the best in this new Islamic year. Amen thumma Amen._* 4⃣8⃣ Mota yakoma yad'auki d'aya daga cikin wayoyinsa, sai hura hanci yakeyi, bugu biyu akad'aga, ad'an kausashe ya ce, "Ammar ina buk'atar yaranka. My guy lfy kuwa?. Mtsooowww wasu wawaye aka turomin, so nad'an koyar dasu zaman tarbiyya ne. Murmushi Ammar yayi, Dan yasan waye abokin nasa, okey kabani 15m. Katsal. Baice k'alaba ya yanke wayar, cikin motar yakoma ya zauna, amma murfin abud'e yake, k'afafunsa duk suna k'asa. Mintuna kad'an saiga motar police, tuni aka yayibi karnukan farauta acewar BOBO aka watsa amota. Bobo yakalli police d'in ya ce, " kukaisu asibiti, abasu kulawa ta musamman, zuwa gobe kuma natsincesu a Stations, yana gama fad'a yashige motarsa. Suma 'yansan Dan mota suka shiga, harya tada mota wani police ya kwankwasa MASA, sauke gilas d'in yayi yana kallon matashin police d'in batareda yayi maganaba. Umm yaya dama cewa nayi kozamu fara rakaka inda zaka tukunna. Fararen idanunsa yad'ago, wad'anda ahalin yanzu sukad'an canja kala zuwa jaa, no karka damu Musadiq kuje kukaisu asibiti, sune keda buk'atar taimako baniba, saidai zuwa gobe kutabbatar da sunk'ara cin ubansu, harsai sunfad'i wanda yaturosu. d'an murmushi Musaddiq yayi wanda daga gani akwai sanayya tsakaninsa da bobo, ya ce, "ok yaya ALLAH ya tsare. Shima bobon murmushi yayi tareda jinjinama musaddiq sannan yaja mota yay gaba. Musaddiq yabi motar da kallo yana murmushi, shidai arayuwarsa yana k'aunar ya Abdulmaleek domin mutumin kirkine, yanzudai kalli anturo mutane dansu cutar dashi, yakuma sassanbad'esu amma saboda adalaci ya ce, " akaisu asibita abasu kulawa ta musamman, (ALLAH sarki aunty Ni'ima, ALLAH yajik'anki, inama kina darai har yanzu, daduk gidanmu sainace kinfi kowa dace da miji nagari). “araina na ce, "kenan k'anin marigayiya Ni'imane shi?.”🤔 Guri yasamu yay farking cikeda tak'ama yanufi office d'insa, sai rissinawa ma'aikatan wajen suke suna kwasar gaisuwa, ransa a6ace yake danhaka ko amsa musu bayayi, hannu kawai yake d'aga musu. Sakatariyarsa ta jinjina kai, aranta ta ce, " yau kuma boss afusace akazo?. Zama tayi bayan yashige, turare tad'auka tak'ara fesama jikinta tareda k'ara gyara fuskarta, sannan tanufi office d'in. Kamilu masinja yata6e baki yana fad'in yarinya wahala bata ishekibane, nasan ko matan duniya sun k'are wlhy oga bazai sokiba. Ahankali ta tura k'ofar tashiga, yana zaune akan kujerarsa ta alfarma, kwance yake acikin kujerar idonsa alumshe yanad'an lilawa ahankali, tabishi da kallo zuciyarta na zungurarta da wani Abu, a zuciyarta ta ce, "ALLAH ya mallaka minkai amatsayin mijina. Na ce, " hummm." K'arasawa tayi Inda firij yake, tad'akko drinks da cup tanufi inda yake. Saida tagama tsiyaya lemon sannan ta ce, "oga ga abinsha ko kana buk'ata?. Baice mata komaiba, saidai yabud'e idanunsa dasukayi d'anja Dan 6acin rai. Waye yazo nemana?, yafad'a cikeda karsashi. Tuni takama kanta, cikin d'ari² ta ce, ''mutum 3 sunzo nemanka amma biyu sun had'u da yalla6ai Kamal. Ya ce, "d'ayanfa?. Ta had'iye yawu kuut, d'yan Ra'is ned'an gidan........ Hannu yad'aga mata alamar baya buk'atar k'arin bayani, yay mata nuni tatafi. Tafiya take cikeda salo tana juya mazaunai, hartakai k'ofa ya ce, "k zonan. Cak tatsaya k'irjinta na dukan uku², ahankali tajuyo saitaga bama ita yake kalloba waya yake dannawa, jiki a sanyaye tace sir gani. Idanunsa akan waya ya ce, "k sau nawa zan fad'a miki karki sake zuwamin nan da k'ananun kaya office?. A zuciyarta ta ce, " danka k'yasane, amma afili saitace sorry sir zan kiyaye. Tsaki yaja, har yanzu idonsa nakan waya ya ce, "wlhy daga yau kika sake banzar shiga kikazomin office abakin aikinki, 6acemin anan!!!!. Dasauri tafice Dan atsawace yay maganar. Yay kwafa tareda fad'in stupid gal kawai. Waya ya d'auka yakira kamal, bugu d'aya ya d'auka, kamal kana office ne?. Eh Abdulmaleek, ka isone?. " eh yanzu na k'araso". Okey

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});