Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ida ciroshi tana fad'in Alhmdllh, saikuma sabuwar nak'uda, mik'ama Nurse tayi jaririn takuma kar6ar sabon baby daya kunno kai. Ai Rahma na sauke wannan kaya saitayi lakaf ajikin bobo. Ahargitse yake kiran my Nusfulhayat!, my cute!, momyn Nawal!!. Katseshi doctor Fa'iza tayi da fad'in sir babu abinda yasameta tana hutun wucin gadine. Doctor Fa'iza bafata numfashi. A'a yalla6ai tanayi kalli k'irjinta kagani, kallonkuwa yayi saiyaga tana sauke numfashi ahankali. Dukda bai samu nutsuwa dukaba yaji dad'i, ko sauraren 'ya'yan baiyiba dukda yana cikin matsanancin farincikin zuwansu duniya, amma ta mamansu yakeyi yanzu, bayan shigewar mintuna Rahma tad'aga idanunta dasuka k'ank'ance tana kallon bobo, murmushi tamasa. Cikin farinciki yarungumeta yana fad'in Alhmdllhi Alah kulli'halin, sai yanzu d'unbin farincikinsa yafito fili. Tuni labari yakaigasu Ammi, anhaifi twins namiji da mace. Dan dad'i Appa har rungume ammi yayi, ya sulaiman sai kauda kai yayi yana dariya. Cikin 'yan mintuna aka gyara baby's da mamansu, bobo yad'akkosu yafito dasu wajensu ammi, bakinsa yak'i rufuwa yaukam. Had rige-rigen d'aukarsu ake tsakanin ya sulaiman dasu Ammi. 'Yan gata sun iso duniya, yara masha ALLAHU basuda maraba da yayarsu Nawal, dakuma mahaifinsu Abdulmaleek bobo. To saimuce ALLAH yaraya 'yan dugwuy-dugwuy iyalan baba. Sai karfe 8pm sukabar asibitin, aka rankaya zuwa gidan Appa, zuwa sannan labari yabaje dangi, sanda suka Isa gidan Appa cike yake dasu anty rasheeda, har and'ora ruwan wanka. Innar su hibba tayima Rahma cikakken wanka, tanata zille-zille da zame-zame har aka kammala, yarama anmusu, annad'esu cikin fararen kayan sanyi masu laushi sai barcinsu sukeyi. Rahma tafito daga bayi Dan tuni inna tafito tabarta tana k'imtsa kanta. Zama tayi tashafa mai tashirya tsaf cikin atanfa sabuwa dal, itakad'aice ad'akin mutane duk suna falon k'asa har jariran. Abincin da Anty ummy ta ajiye mata tazauna taci, shayine mai kauri da farfesun 'yan ciki, saikuma soyayen dankali, citai kad'an sanan tahaye gadon ta kwanta sai barci, dama barcin bai ishetaba.............. *_luv you oll._*. *_(((S)))........2017_* [11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _β€’πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύβ€’_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 7⃣1⃣ Falon cike yake da dangi, bobo yashigo da sallama hannunsa d'auke da leda babba, gaisawa suka shigayi da mutanan falon anata masa barka, cikeda farinciki yake amsawa, mutane dayawa dabasa ganin dariyarsa yau har mamaki sukeyi yanda yaketa yak'e hakwara. Ammi dake fitowa daga kichin ta ce, "yauwa mukarram kadawo?. Eh ammi nadawo. A'a yanaganka da 'Yar leda?, sauran Kayanfa?. Mik'a mata ledar yayi yana fad'in wlhy naje zan sayo saina tadda ya ishaq awajen yana siya, shiyyasa najuya nasiyo wad'annan kuma. Ayyo aiban saniba, to ina yayan naku yanzu?. Acan nabaroshi, amma nasan yana hanyar zuwa shima. To shikenan ALLAH yakawoshi lfy. Ameen, Ammi ina Rahma d'in?. Tana d'aki kwance tana barci, kasan jiya bawani barcin kirki tasamuba, kaima aii yakamata kaje kad'an kwanta kona awa biyu kasamu kayi. Shafa kansa yayi yana murmushi, wlhy Ammi ni namafa daina jin barcin. Dariya ammi tayi, lallaikam murnar zuwan kishiya da miji yasa idonka bushewa kenan?. Dariya sosai bobo yakeyi, ya ce, " ammi aii k'yautar ALLAH daban take, wlhy ko'a mafarki banta6a zaton Rahma zata iya haihuwar yara biyuba yanda nake mata kallon yarinya karama. Itama ammi dariyar tayi, mukarram aii ikon ALLAH kenan, Ubangiji mai hikimane, amma gsky koni bankawo Rahma tana d'auke da cikin yara biyu bane, ALLAH dai yarayasu akan turbar addinin islama. Amin ammi, bara nalek'a Rahman kota tashi?. To, ammafa Indai barci take karka tada ita kaji nagaya maka. Karki damu ammi, bobo yay maganar yana haurawa sama. Cikin barci Rahma taji ana shafa kanta, ahankali tamotsa, jin k'amshin turarensa yasakata bud'e idanunta ta sauke akansa. Murmushi yamata murya a sanyaye ya ce, "my Nusfulhayat kin tashi?. Kanta tad'an jin jina tana murmushi, yunk'urawa tayi zata tashi yataimaka mata, ta zauna sosai amma tana jingine ajikinsa, Nurulk'albi yaushe kashigo?. Sumbatar kumatunta yayi idanunsa cikin nata ya ce, " tun d'azun ina zaune ina gadinki aii. Tofa saikace wata sarauniya?. Aikinfi sarauniya awajena Rahma, Ubangiji ALLAH yayimiki albarka, tabbas ke Alherice arayuwata, shigowarki Rayuwata kin yalwata alkairi mafi daraja agareni, inason yara sosai Rahma, inaso yara fiye dazaton mai tunani, saigashi tashi d'aya ALLAH ya albarkacemu da samun biyu, Rahma yanzu nine da yara har uku?, kai ALLAH na gode maka godiya Mara adadin kididdiga, lale dake yasanyin idaniyata. Dad'i da farinciki duksun yalwatu afuskar Rahma, takuma narkewa ajikinsa, ngd my Nurulk'albi, ina rok'on ALLAH ya tsawaita rayuwarmu domin miyita bauta masa da kuma kasancewa tare har abada. Ameen my cuty na. Amma Dan ALLAH ina neman wata alfarma agareka. Gyara zamasa yayi Yakuma jawota sosai ajikinsa ya rungumeta, kitambayi Duk abida kikeso agareni insha ALLAH zanmiki shi inhar bai sa6ama ALLAH ba. Murmushi tamasa ta ce, "inason asakama macen sunan marigayiya aunty Ni'ima Dan ALLAH kamin wanan alfarmar, idan kamin haka zanyi farinciki sosai. Tsura mata idanu yayi nawani d'an lokaci, har jikinta yafara sanyi ko bazai aminceba, amma saitaji ya rungumeta tsam yana bata Sumba takowane 6angare ajikinta. Ammi dake tsaye tun d'azun tana kallonsu ta kauda kai tana murmushi, dama tabiyo bayansane danta tada Rahma tabama yaran nono, Dan sunfara kukan yunwa. Jin maganar dasukeyi yasa tatsaya bata shigoba Dan batason katsesu saga farincikin dasuka tsinci kayinsu. Saida bobo yagama bata hot kisses sanan yad'agota yana kallonta, ALLAH yamiki albarka shine abinda yaketa maimaitawa, cikin raunin murya ta ce, " my Zuma kayarda kenan?. Jinjina mata kai kawai ya iyayi yana murmushi, ahankali ya ce, "Rahma nazama naki, kinrigada kin dabaibaiye komai daya shafi rayuwata, aduk duniya daga iyayena saike acikin jerin Abu mafi Girman muhimmanci a tafiyar rayuwata, sai kuma 'yan uwana wad'anda suka zama jigogi kuma matakan tsaro agareni, 'ya'yana sanyin idaniyata, ALLAH ngd maka daka yalwatani da wad'annan ni'imomi naka badan Nafi sauran bayiba kabank, badan nakasance mafificiba acikinsu, badan wayonaba, badan iyawataba, badan k'arfinaba ka yalwatani ka azurtani ka ni'imtani, ka suturtani, ka ingantani, ka d'aga darajata acikin bayinka, ya ALLAH yanda kamin wanan k'yauta aduniya ka Albarkaceni dasamun mafiyinta alahira....... Hawaye suka zuraro akumatunsa, Rahma tasa hannunta tana share masa. Yacigaba da fad'in ya ALLAH karka jarabceni da kasancewa acikin masu butulci agareka, ya ALLAH karka jarabceni dagacikin masu sa6onka, ya ALLAH karka jarabceni daga cikin marasa godiya agareka, ya Ubangijin Al'arshi ma'abocin Rahma da gafara, ka gafartamin dukkan kurakuraina nida zuri'ata data musulmai baki d'aya, ya ubangijina kak'ara imani da tsoronka azuciyata, ya ubangijina katsare harshena daga sa6amaka komai ribar hakan agareni, ya Ubangijina ka tsare idanuna daga kallon haramun komai farincikin da hakan zai sakani, ya Ubangijina katsare k'afafuna daga zuwa inda haramun yake komai d'aukakar da hakan zata jamin, ya Ubangijina katsare gangarjikina, zancena, numfashina, furucina, daga afkawa tarkon shaid'an la'ananne nida dukkan zuri'ata data musulmai baki d'aya, ALLAH ka k'arama annabi daraja da fadila da Wasila, ALLAH yasa munacikin al'ummar da zaiyi alfahari damu muda zuri'armu baki d'aya, ALLAH yasa munacikin wad'anda zasu amsa kiran cetonsa awata rana mai cikeda rud'ani da hargitsi, ya ALLAH idan katashi d'aukarranmu kad'auka munacikin imani da tsoronka bacikin shagaltuwa da duniya da abinda ke cikintaba. Ameeen Rahma tafad'a tana k'ank'amesa hawaye sharkaf da fuskarta saboda addu'ar mijin NATA ta ratsa dukkan sassan jikinta da 6argon jikinta. Ammi ta share guntun hawayenta itama sannan tamusu sallama. Da Sauri Rahma ta tashi daga

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});