Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Shine nace masa ana zarginsa dayima yarinya fad'e. Indai tak'aice maka bayani yashiga zage zage wai sharri akaima d'ansa, wlhy saimunyi Dana Sanin kama masa yaro, harda cewa zaije yasamu dady yaji idan shine yasani naringama mutane rashin mutunci, kajimin mutumfa. Dariya sosai bobo yakeyi, ya ce, " shashasha kawai, baimaga komaiba saiya wayi gari d'ansa a prison. Ammar ma dariyar yakeyi, ya ce, "mutumina bakada dama wlhy. Dariya sukayi gaba d'aya, sukai sallama bobo yashiga mota sai gida. Gidansa Yakoma yay wanka, cikin wata d'anyar shadda blue yashiya, abinka da fari sai d'aukar ido yakeyi, yad'ora farar hula da farin takalmi, (araina nace kai guy d'innan fa yaci sunansa bobo gsky, ya iya d'aukar wanka babu k'arya), haka yafito yanata zabga k'amshi kamar Wanda yay 6arin turare, mota yashiga sai gidan Appa. .*.*.*.*.*.*.*..*.*.*.*.*. Sukam su Rahma bayam sungama shaftarsu kicin suka Shiga kamar yanda su aunty Sameera suka saba duk randa sukazo, sukeyin girki. Yauma haka suka dafa abinci kala kala, Ammi sirikar arzik'i, mai d'aukar matan 'yayanta tamkar yayan ta, sai saka musu albarka takeyi. 'Yan aikin gidan suka gyara ko ina, akaima yaran wanka kafin iyayensu su k'araso, Dan tare zasuje masallaci, kowa aka shiryashi tsaf. Sumadai iayayen wanka suka sakeyi. Rahma takar6i kayan su khairiyya tasaka Dan bata d'akko wasu kaya dabanba, kayan summata k'yau sosai kamar Dan ita akayi, dama jiya suka kar6osu faga wajen tela. Suna d'aki suna surutu harsu Bobo suka k'araso suka kwashi yaran sai masallaci, harda Appa amota d'aya suka fice, dama duk juma'a haka suke tafiya gwanin sha'awa. Sun gama suka mik'e da niyyar fitowa falo Rahma tad'auki hijjab zata saka, aunty ummy tarik'e, haba amaryarmu abari ango yazo yaga kwalliyar mana, Rahma data duk'ar dakai ta ce, "Anty ummy plzzz kibarni. Aunty Rasheeda takwace hijjabin ALLAH bazaki sakaba, sokike kima auta bak'in cikin kallon kwalliyar?, kunga kumuje, babu yanda zatayi haka tabiyosu. Abinci suka shirya a tsakkiyar falon, bayan an shifid'a k'atuwar ledar cin abinci, sungama shirya komai aka manta da wani Abu, Rahma ta ce, " bara nad'akko. Gaf taji tayi karo da mutum, da sauri tad'anja baya, tad'ago ta kallesa Bobo ne tsaye cikin gayunsa. Maida kanta tayi k'asa Dan yaymata k'yau da kwarjini, kayi hak'uri ban ganiba. Baice mata komaiba, saidai binta da kallo dayakeyi kamar yau yafara ganinta, kayan sunyi mugun mata k'yau da kama jikinta Dan siket da rigane, kuma tad'anfi su khursiyya jiki, ganin bai tankaba kuma yak'i bata hanya tawuce, ta ce, "sannunku da dawowa, zan wuce. Nanma bai motsaba, wani haushi ya turnuk'e Rahma, saikawai tajuya zata koma, caraf ya damk'e hannunta, abirkice tajuyo tana kallonsa, ga maganarsu Appa tanaji dasuke tahowa. Baki na rawa ta ce, " plzz gasu Appa nanfa...... Bata gama rufe bakiba suka k'araso wajen, ya Sulaiman ne agaba, sai ya Hamza abayansa, sai yara da Appa da ya ishaq abaya. Ya sulaiman da ya Hamza suka kalli juna suna murmushi, tuni Rahma tayi k'asa da kai, jikinta harya fara d'an rawa, amma d'an bala'in naku yak'i sakinta. Ya Hamza ya ce, "romeo d'anbamu hanya mudai. Saiyanzu yadawo hayyacinsa, Dan ba k'aramin narkar dashi Rahma tayiba yau, yasaki hannun Rahma, aiko takwasa da gudu tai ciki. Abin yabama Bobo dariya, Dan haka yay murmushin gefen Baki, karasowar su Appa yasa ya sulaiman yaja hannunsa sukayi ciki. Sannu da zuwa da gaisuwa Matan nasu suka Shiga mik'owa, bayan sun Risina sun gaida Appa, Rahma tanacan bayan khursiyya tamak'ale kamar wata muna fuka. Appa ya haura sama Dan rage kayan jikinsa. Waimiya faru naga kin dawo baki d'akkoba?, cewar Aunty Sameera dake kusadasu Rahma. Tad'an Sosa wuyanta, aunty harfa natafi naji maganarsu Appa nadawo. Dariya aunty Rahma tayi, takira Taufiq babban d'an ya ishaq ta aikesa ya d'akko. A can kuma ya Hamza ya kalli Bobo ya ce, " mutumina kafa fetsare soyayya har a gabammu. d'an tsaki yaja Mara sauti, Yaya nifa bawata soyayya nakeba, bigenifa tayi. Ya Sulaiman dake jinsu yay dariya, danta bigeka saika damk'e mata hannu kaki saki, kumafa kallon soyayya kake mata. Shiru yayi bai tankaba, ya Hamza da ya Sulaiman suka shek'e da dariya. Ya ishaq ya ce, "kukuma lfyarku?. Bobo daya fara k'uluwa yamik'e daga tsakkiyarsu yana fad'in inafa sukaga lfy Yaya, Kusada ya ishaq yakoma yazauna, saiyayi fesin d'in Rahma sosai. Ya Hamza ya ce, " habawa auta munfa gane wayonka na komawa nan saboda..... Basu k'arasaba suka kuma saka dariya. Suma sauran duksai Kansu yakawo musu wuta, suka kalli Bobo suka kalli Rahma, sai kawai suma suka shek'e da dariyar, shimadai awannan karon ya murmusa, Dan wlhy baima kawo kamai aransaba yadai zaunane kawai saboda bayaso su ya Hamza sucigaba da takura masa. Fitowar Ammi da Appa yasa suka tsagaita, Ammi ta ce, ''tomikuma yafaru?. Ya Sulaiman ya ce, "ba komai Ammi, autanki ne zai mana gulma, yanaso yana kaiwa kasuwa. Ammi da Appa sukayi murmushi dansun gane inda zancen yadosa. Kubarmin babana yasha iskar marece, cewar Appa. Yauwa Appa na fad'amusu, wlhy sun takuramin, Bobo yay maganar cikeda shagwa6a. Shagwa6ar tasa tabama kowa dariya, harda yaran, shikam yasaki baki da hanci yana kallon Rahma dake tuntsura dariya sosai, baiyi tunanin tana dariyaba. Tana d'agowa suka had'a ido saikawai ta gumtse dariyar tadaina. Anty Rasheeda da Anty Sameera sukace kai ALLAH yayi magulmatan masoya awajennan. Kowa yaga abinda yafaru tsakanin Bobo da Rahma Dan haka dariya hardasu Appa da Ammi, bayan an tsagaita Appa ya ce, " to ya isa haka, asauka aci abinci. K'asa suka sakko sukaima falon zobe, ga abinci atsakkiya, Ammi tana kusada mijinta, sai yaran sun sakasu tsakkiya, dandanan kuma gidan yay tsit bakajin komai sai k'arar filet da cokali, kowa abinda yakeso yakeci, family's d'in Alh Aliyu hamshak'i yahad'u masha ALLAH. Shida Ammi, 'Ya'ya shidda, surukai hud'u, jikoki goma cif. Yaran ya ishaq, Taufiq, Sageer, Zainab, muhseen. Yaran ya Sulaiman, Sumayya, mustapha, Jiddah. Yaran ya Hamza, Ahmad, Kamal. Sai Bobo, Nawal. Bayan sun kammala cin abincin, 'yan aiki sukazo suka gyara ko'ina yakoma tsaf, yaran suka fice tsakar gida suna wasa. Sukuma sunata hirarsu. Duk juma'a haka suke zama, Appa yashige tsakkiyar iyalinsa asha fira, da karantar halayen dasuke ciki, babu ruwansa har matan 'ya'yansa 'ya'ya yad'aukesu. Afirarne yake sanar dasu maganar kawo kud'in auren su khairiyya dukda su mazan duk sun sani, kowa yayi murna, dafatan ALLAH yasa akai da rai. Kiran sallah la'asar ne yatadasu, mazan suka tafi masallaci sukuma sukayi agida. Har dare suna nan, akasha shafta sosai, tuni Rahma tasaki jikinta acikinsu, hakan yayma kowa dad'i sosai. Bayan isha'i sukaci abincin dare, kowa yakwashi matarsa da 'ya'yansa sai gida. Rahma kam jitake kamar ayita zama ahaka, Dan taron yaymata dad'i sosai. Kafin su Isa gida har Nawal tayi barci, Rahma tasa6eta sukayi ciki, shiya bud'e gidan suka shiga, kowa yanufi d'akinsa, babu maimagana saikace wasu kurame. Dama anyima su Nawal wanka a can, sai kawai ta canja mata kayan barci, itama tashiga wanka, bayan tafito tayi abinda yadace, harzata kwanta tatuna da shayin oga. Babu shiri tafito zuwa kichin, shayin tadafa takai masa, sallah ta tarar yanayi, Dan haka ta ajiye tafito abinta........ *_Happy juma'at Mubarak_* *_luv u oll my fan's_* *_(((S))).......2017_* [11/12, 2:51 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_*

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});