Chapter 69
Chapter 69
jiyya kullum dangi na jerangiyar dubata, su ya ishaq dukansu sunzo da matansu suma, Rahma kullum acan take yini, bobo yakaita idan zayi aiki, idan kuma yataso yabiyo tanan su wuce gida. Zuwan bobo asibitin bak'aramin tada hankalin Safna yakeyiba, duk sanda yazo saitayi kuka a6oye shiyyasa ta k'agarama a sallamesu su koma gida. Cikin kuwa ikon ALLAH yau doctor yabasu sallama, ba k'aramin farinciki Safna tayiba Dan har fuskartama saida tanuna, to suma dangi kowa yayi farinciki damata addu'ar k'ara samun lafiya. Haka suka rankaya suka fito domin tafiya gida, akuma daidai wannan lokacinne motar bobo tashigo asibitin, fitowa yayi ya iso garesu, yarissina yamik'a gaisuwa gasu ummi tareda fad'in lfy dai naga kun fito?. Rahma ta ce, an sallamemu aii. Murmushi yayi yana kallon safna, a lallai auntymu yau sai kwanan gida ko?. Dariya akayi itakuma Safna tad'anyi murmushi. Abba ya ce, "Rahma to kibi mijinki kuwuce gida ko. Rahma ta marairaice fuska tamkar zatayi kuka, amma batace komaiba. Dafata ummi tayi ta ce, " kije kinji autata ainasanki akwai biyayya....... Bobo ya katse ummi da fad'in ummi ki barta kawai muje muyima auntynmu rakkiya har gida. Kallonsa Rahma tayi tanaijin farinciki, haka suka rankaya suka tafi. Bak'aramin farin ciki Rahma tashigaba data ganta yau agida, aiko haka taita yawo lungu da sak'o nagidan babu inda bata shigaba, itace har gidansu ya Kamal, sai bayan isha'i bobo yad'auketa suka tafi, dama Nawal tana gidansu Appa. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Rayuwa mai gudu da sauri, sakwanni sunata tafiya, mintuna sunata sauri, awoyi NATA gudu, akwana atashi babu wuya wajen ALLAH, Alhmdllh jikin safna yayi sauk'i sosai saidai abinda ba'a rasaba, shimadai jiyyar zuciyane narashin bobo. Bayan sallamota ma Rahma tad'an zazzo ganinta dukda dai bata cika sake mataba amma bata damuba............. *_luv you oll_* *_(((S))).........2017_* [11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•🅱🅾🅱🅾•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* *_"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ubangiji ALLAH ka gafartama mahaifiyar khadeeja Ahmad (kdeey), ALLAH ya yafemata Yakuma bada hak'urin rashinta, ALLAH ya albarkaci abinda tabari da mad'aukakiyar shiriya ameen🙏🏻😭"._* 6⃣7⃣ Kasancewar yau weekend bobo yana gida, yanzu ma haka yana kwance bisa gadonsa dagashi sai wando 3½ da t-shirt mara nauyi, gefensa Nawal ce kwance tana barci, sai Rahma dake d'an kai kawo atsakar d'akin tsakanin dirowa da gado, kayan bobo damai wanki yakawo take shiryawa, kad'an kad'an takan yamutse fuska da cije le6enta, bobo daketa binta da kallo tun d'azun danba k'aramin tafiya dashi dressing nata yayiba, sanye take da jins blue yasha adon duwatsu daga saman cinyarta saikuma Riga pink t-shirt ta mata, kanta babu d'ankwalli tadaiyi farking nasa da pink d'in ribom, gashin yaywani Tim atsakkiya saboda kasancewarsa roba roba, yad'an lumshe idonsa yana shak'ar kamshinta daya baza d'akin, dukkuma motsin datayi saiya bigi hancinsa. Rahma dake gyara linkin wasu kaya ta ce, "oga me wannan kalonfa?. d'an murmushi yayi yana k'ara gyara kwanciyarsa har yanzu idonsa akanta, murya akasalace ya ce, "my cute zokiji wata magana mana. 'Yar dariya tayi tareda nok'e kafad'a ta ce, " nak'i wayon, nakula yau sokake kawai mushiririce agidannan batareda nayi aikin komaiba, kallifa agogo har 12 tayi amma banshiga kicinba, mikakeso muci da rana?. Wata Narkakkiyar dariya yayi sannan Yakuma juya kwanciyarsa zuwa gareta Dan yanzun takoma jikin dirowa. Ya ce, "to aii Indai dan tanine yau kiwuni ajikina kina bani ni'imtaccen k'amshinki ina shak'a tareda jin d'umin lallausar fatarki sannan naringa kallon k'yawawan idanunnan naki fararen wad'anda sai antara mata dubu ake samun mace d'aya mai irinsa, hakan kawai ya wadatar dani kuma zai k'osar dani fiyeda abincin dazanci. Yabama Rahma dariya, Dan haka dariya takeyimasa sosai harda wata shashsheka mai d'aukar hankali dakuma kashe jiki, aikodai idanma tarkone Rahma keson d'anawa to tayi kamu, Dan kuwa tuni bobo ya narke agadon yana binta da wani shu'umin kallo, itakam dariyarta tacigaba dayi batareda tasan tarkonta Yakama zaki ba, kayan dasuka rage ta ida kwashewa tasaka adirowa, ganin yana niyyar sakkowa daga gadon yasata fita ad'akin dad'an gudunta, dariya tabashi yazauna abakin gado yanayi. Itakam kichin tanufa domin d'ora girkin rana, Abu naga tasamu tarufe hancinta sannan ta kunna gas, yau wajen kwana biyu kenan batason kamshin gas d'innman, idan zatayi girki saita to she hanci shima a daddafe take gamawa, yau kuma ga abun yana Neman had'e mata biyu Dan cikinta ciwo yakeyi yana daurewane kawai. Ruwan shinkafa tafara d'orawa sannan tabud'e firij tad'ebo naman kaji zata wanke, wani wuntsilawa da cikinta yayi ya tilasta mata rik'e murfin firij d'in, tadafe cikinta jitake tamkar tafasa kuka. Daidai nan bobo yashigo kichind'in da zummar tayata aikin dan dama duk weekend tare suke aikin gidan, haka zaita tayata tana hanashi, amma saiyace yana koyi da ANNABIN ALLAH ne, Dan wannan sunnace mai k'arfi, tun tanajin kunyar idan yana tayata suyi bak'i harma yanzu tasaba abin yazamemata jiki. Ganin takifa kanta tayi shiru yasa bobo fad'in lfy kuwa my Nusfuhayat?. Bata iya basa amsaba saidai tad'aga MASA hannu, da Sauri ya iso Inda take, tabaya ya rungumota yana k'ok'arin juyo da ita, aijitayi tamkarma yak'ara mata ciwonne, tai saurin k'adandaneshi tana fad'in wayyo ALLAHna dadyn Nawal cikina, wayyo kamar ana tsitstsinkamin hanjina, da Sauri yazame abinda tarufe hanci dashi, aiko tana shak'ar k'amshin gas d'in sai yunk'urin amai, da gudu ta fisge jikinta daga gareshi ta arce waje, shima take mata baya yayi. Abayin dake falon taja birki amai tafara zazzagawa kamar zata amayar da kayan cikinga, bobo dukya rud'e yarik'eta sai sorry yake mata. Saida tagama yataimaka mata tawanke jikinta shikuma ya wanke Inda ta 6ata, cak yad'auketa suka nufi falo, zaunar da ita yayi ajikinsa yana fad'in sorry my cute duk-ya rud'e tamkar zaiyi kuka, cikinne yak'ara murd'a mata takuma k'ank'amesa tana kuka. Shima sosai ya tallafota jikinsa, tuni ya janye hannunta daga kan cikin ya maye gurbin wajen danasa yana shafawa ahankali, can azab ta isheta takuma k'ank'amesa tana ambatar sunan ALLAH, tare suka k'arashe da bobo Daka gansa kasan yana cikin damuwa. Ganin abun NATA k'ara gaba ya ce, "my Nusfulhayat Kodai asibiti zamuje?. Da Sauri ta girgiza MASA kai tana cije le6e, hawaye da gumi kam sun jik'e fuskarta sharkaf dukda da AC dake aiki a falon. Hijjab d'inta datakan ajiye afalo Indai tasan k'ananun kayane ajikinta, gudun kar bak' yazo yasa takan ajiye, bobo yajawoshi yana share mata gumi da hawayen dasukaima fuskarta ado, wata damk'a data MASA yasakashi fad'in uchch my cute, ita batamasan yanayiba takanta take kawai, wayarsa yad'auka yakira ya sulaiman, ko gaisuwa bai tsaya sunyiba yafad'a MASA abinda ke faruwa, da Sauri shima ya sulaiman ya ce, "ganinan zuwa to. Cikin mintuna k'alilan ya sulaiman ya iso gidan, har yanzu Rahma tana jikin bobo, kai tsaye cikin gidan ya sulaiman yashigo. Bobo yad'auki hijjab d'inta yasakamata, hakan yayi daidai dashigowar ya sulaiman, basu tsaya ko gaisuwaba yashiga dubata, 'yan tambayoyi yafara mata wad'anda duk cikin kuka da zafin ciwo take amsa masa. Ya sulaiman yabama bobo wata kwalba, Abdulmaleek kakaita tayo fitsari mugani..... Aibaima bari ya sulaiman ya k'arasaba Yasureta sai bathroom d'in dake falon, fitsari tayi a 'Yar kwalbar sannan suka fito, nanmadai d'akkota yayi dukda tanata nok'e nok'e wai bataso yabarta zata iya da kanta, bai saurareta yasunkuceta suka fito. Saman doguwar kujera ya direta sannan yamik'ama ya sulaiman kwalba.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83