Chapter 26
Chapter 26
kauda fuskarta tana tura Baki gaba. Shima bakin yata6e yacigaba da aikinsa. Da zame zame da mazurai aka gama wannan gashin k'afar, yad'auki maganin shafawar ya shafa mata sannan yakwashe kayan yafice itakuma ta kwanta tana sauke numfashi. Bai sake shigowa d'akinba harsu Ammar suka iso shida matarsa da yaransu biyu duk maza. Cikin farinciki yataresu, yanda yaketa murmushi saika d'auka bashibane yagamawa Rahma mazuraiba yanzu. Cikin falon suka k'araso, Sumayya matar Ammar ta ce, "nibanga amaryarba ko ka sakata ta 6uyane?. Murmushi yayi ya ce, " 6uyan lfy, tana d'aki kwance batada lfy. Ammar yashek'e da dariya mutumina komun samu k'annen Nawal ne?. Harararsa yayi kaifa bakada kirki wlhy, to Abu ta taka ak'afarta d'azu da safe. Ammar ya ce, "ayya ALLAH yakiyaye gaba, amma yanda na sanka d'innan ai yanzu munsami baby duk wani zame ²n ka. Kadaiji dashi d'an iska, bobo yafad'a yana nufar d'akin Rahma. A zaune ya Tatar da ita tagama saka kaya, Dan k'afar tad'an saki shine taje tayi wanka. Ki taso su Ammar sunzo. To. tafad'a atak'aice, haryaje k'ofa takatseshi dafad'in bafa zan iya fitaba. Cak yatsaya kuma bai juyoba, yakai minti uku ahaka saikuma ya waigo, yawani saki murmushin mugunta danyasan maganar dazaiyi, okey kinaso nad'aukeki Dan kinji Ammar ya ce, " namiki ciki ko?, kinaso su tabbar kenan?. Ido Rahma ta gwalalo waje ta ce, "nid'in?. Baki ya ta6e tareda takowa har inda take, taho na d'aukeki nikuma namiki alk'awarin tabbatar musu da hakan. Matsawa tayi gefe, ta ce, " kabarsa kawai zan iya. Dariya yayi ya ce, "Yar rainin hankali, yana gama fad'a yafice yana cigaba da dariyarsa. Rahma tarike baki o ni Rahma dama haka mutumin nan ya ke?, barikiga natashi kafin yaje ya nafkamin wani sharrin. Haka ta d'ingisa har zuwa falon, ta zauna suka gaisa sunata tsokanarta, itadai bata iya cewa komai sai murmushi, mik'ewa tayi danufi basu ruwa da abin motsa baki, ya ce, " ina zaki?. Ruwa zan basu tafad'a tana tafiya da d'ingishi. Sumayya ta ce, "kinga dawo kizauna amarya, bari na d'akko mana aimu ba bak'i bane, Rahma ta ce, " haba daga zuwanku sai asaka ki aiki?. Karki damu kinji, idanma kika kusa haihuwa nan gidan zan dawo, hannu tasa tarufe fuskarta Dan kunya, Ammar Kuma yayi dariya, Bobo ya ce, "Ashe na huta nikam?. "Aiko ka huta." Sumayya ce tamusu komai daya dace Rahma tayi, abincima atsakar falon sukaci, mutuminku sai wani kaffa² yakeyi da Rahma, ita abunma kunya da dariya yaringa bata, idan kukaga kulawar dayake bata saika d'auka haka suke kullum. Har dare su Ammar suna gida, sai bayan isha'i suka tafi, bobo kuma yatafi d'akko Nawal Dan gobe zasu koma makaranta. Rahma tad'an daddogara kamar gurguwa tad'an gyara abinda yadace sannan tayi wanka, shirin barci tayi tazauna jiransu. Bayan wasu 'yan mintuna da zamanta saigashi ya iso da Nawal akafad'a tayi barci. Saman gadon ya kwantar da ita, Rahma ta ce, " sannu. Yauwa, tafad'a atak'aice. Batabi ta kansaba harya sauyama Nawal kayan barci, shima baice mata komaiba yafita, babu dad'ewa saigashi da ruwa da Kofi, abakin gadon ya zauna yaciri magungunanta ya mik'a mata, tuni ta 6ata rai amma babu yanda zatayi haka ta amsa tana matse ido ta shanye, hawaye harsun cika mata ido. Baki yata6e yayi kamar baiga hawayenba, yad'auki maganin shafawar yad'ago k'afarta yad'ora saman cinyarsa, maganin yashafa mata, ta lumshe idanu danji take kamar yana mata tafiyar tsutsa. Shikanshi cikin nishad'i yake shafa k'afar, Dan yakai minti 7 yana shafa maganin, saida tad'an janye k'afarta sannan yadakata. Mik'ewa yayi yamusu sallama yafita. Rahma ta sauke ajiyar zuciya aranta ta ce, *_"Zaki na Ammi da Appa kafi karfin wargi"._* _(Nikam Bilyn Abdul kirarin nata yabani dariya, nima zan kiya naringa yima my Abdul d'ina lol.)_ .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Yau bobo dakansa yayma Nawal wanka, yaymata shirin makaranta, Rahma kuma tadaure tahad'a musu break da abincin Nawal na makaranta. Sauri² sukayi break d'in suka fita. Har harabar gidan Rahma tarakasu, tana musu addu'a, bobo daya tada motar yalek'o kansa yana kallon Rahma, 'Yar gurguwar gidanmu akuladai karkuma akarya d'ayar. Yana gama fad'a yafigi motar suka fice. Ita maganar tasama dariya tabata wlhy, afili ta ce, "dama yanama mutane wasa?. Tayi murmushi tareda shigewa ciki. ---------------------------+ Yana ajiye Nawal a school yanufi office, amma duk saurin dayakeyi saida yatadda mutane na jiransa, ciki harda Alh Sunusi Dala. Kasancewar kowa yasan waye Alh sunusi dala suka barsa yafara shiga domin ganin Bobo. Hannu yabashi suka gaisa, sannan ya ce, " Alhaji mike tafe dakai?. Alh sunusi yasauke ajiyar zuciya, Brr... abunda ke tafe dani babbane kuwa, d'ana 'yan sanda suka kama tun ranar juma'a, kuma sunk'i bamu belinsa wai saisun kaimu kotu, gashi lauyana baya k'asarnan naturashi wajen wasu kayana a k'asar Chaina. Alh to yanzu ni mikakeso namaka?, bobo yayi tambayar kamar baisan komaiba. Saboda sunce munemi lauya, nasa abincikamin kwararren lauya shine aka kawoni wajenka, kuma nima idona ya tabbatar mini da hakan. Shiru Bobo yayi yana karantar Alhaji sunusi, saida yaja minti biyu sannan ya ce, "Alhaji kozan iya ganin takardar sammacin da aka baku?. A wannan mai sauk'ine aii Brr, Alh sunusi tafad'a yana mik'ama bobo takardar. Saida yagama karantawa sannan ya ce, " Alhaji gsky akwai Matsala?. Matsalarmi kuma Brr......?. Wato wad'anda suke k'arar d'anka sunzo sun sameni tun ranar juma'a, kuma nine lauyansu. Wani huci Alhaji yasauke, saikuma yay k'ok'arin 6oye 6acin ransa, ya ce, "Brr kataimakeni kamaida musu, ni namaka alk'awarin zan biyaka nikin baninkin d'in abinda suka baka wlhy. Murmushi bobo yayi, sorry Alhaji hakan bazai yuwuba, duk Wanda yad'aukeni aiki a farko shinake yimawa gsky, inabaka hak'uri akan hakan, saidai nace maka mutari gaba kuma........ Kai k'aramin shashasha!!!! Alhaji sunusi yakatse Bobo a tsawace. Shima Bobo ya katseshi ta hanyar d'aga masa hannu, Alhaji sauraramin nan office d'inane ba gidan kallon boll ba, ra'ayinane kuma nayi duk abinda nakeso alokacin danakeso gakuma Wanda nakeso, Dan zaman kaina nakeyi bana waniba..... Kwafa Alhaji sunusi yayi tareda mik'ewa, yanuna Bobo dad'an yatsa yaro yarone, nakula bakasan koni wayeba, amma ina gab da sanar dakai, ni nafika zafin kai Brr...... Dan haka muzuba nidakai. Mtsowwww muzuba mana Alhaji, nidakai za'a tantance damisar takarda. Fuuuuuuu alhaji Sunusi yafice, masu tsaronsa suka take masa bayan. Bobo kuma yaja wani wawan tsaki tareda zama saman kujerarsa. *_" hummm masu karatu, bobofa yad'ebo ruwan dafa Kansa, kokuwa Alhaji sunusi ne yay gamo da gamonsa?, to kudai biyo d'iyar malam Ibraheema mata agidan Abdus'salam kusha labari."_* _labarin bobo bagajeren lbr bane, idan na gajarceshi kuma bazakuji dad'iba, Dan haka karku damu da basarwar bobo zai dawo hanyane😂🤸🏼♂._ 💃🏻💃🏻💃🏻yeeeeee ruwa akemana yanzun nan🌧🌧🌧. *_luv u oll my fan's_* *_(((S))...........2017_* [11/12, 2:52 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* *_Shafin nakune masoyan Bobo, bilyn Abdul d'in ma takuce gaba d'aya, gaisuwa da fatan alkairi su tabbata agareku masoyana, ngd da k'yauna sosai, duk masoyin Bobo ya d'auka wannan shafin nasane, Alkairin ALLAH ya tabbata agareku aduk Inda kuke._* Luv u mazga mazga🤸🏼♂😂❤🤝. 4⃣2⃣ _waye Alh Sunusi dala?._ Alh sunusi dala rik'ak'k'en d'an siyasane, kuma d'an kasuwa Wanda yay zarra akan canjin Dala, matarsa d'aya haj Falmata da yaransu hud'u, Surayya itace babba yanzun haka tayi aure yaranta biyu, sai Haneef
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83