Chapter 67
Chapter 67
tatafi gida batareda nasaniba?. Idonta ta rumtse tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya, wlhy bani nakori aunty Safna ba, kuma bansan abinda akai mataba tatafi, nidai naganta da kaya kawai. To miyasa baki hanata tafiyaba?, Ko kuma ki sanarmin?. Inatsoron kartamin masifane, kuma gashi acikin mutane Muke. Huci yafitar daga bakinsa, yasaka hannu ahankali yana shafa kanta, suduka sukayi shiru nad'an lokaci, jin shirunta yayi yawa yad'ago yalek'a fuskarta saiyaga barci yakwasheta. Maida kansa yayi ya kwanta shima ya lumshe ido amma ba barci yakeyiba yafad'a duniyar tunanine kawai, tundaga randa Appa yay masa maganar auren Safna harzuwa canjamasa da akayi da Rahma, bikinsu, rayuwarsu tanesa nesa, har zuwa yau dasuka zama Abu guda, yad'anyi murmushi dantuna darun Rahma, yasan kishine kawai kecin zuciyarta, jiyayi yak'ara k'aunarta nikin baninkin, yad'ago ahankali yana kallon fuskarta, ahankali take sauke numgashi ak'irjin nasa, fusakarta tayi fayau gawani annuri namusamman datake fitarwa, shiru yayi yana sauraren yanda Nawal take buga k'ofa tana kiran momy! papa!. Tashi yayi ahankali da Rahma ajikinsa, cikin hikima yazameta daga jikinsa ya kwantar da ita tareda kara mata filo, kafin yagyara mata kwanciyarma harta gyra kanta tareda jawo filo tarungume. Murmushi yayi yana mai kallon k'yak'yk'yawar fuskarta, azuciyarsa ya ce, "ragguwa da anta6aki sai barci. Jin Nawal takuma bugawa yamik'e yad'auki tawul yad'aurama k'ugunsa sanan yanufi k'ofar yabud'e. Tana tsaye abakin k'ofar, ya ce, " baby miya faru?. Papa ina momyna?. Saida yajuya yakalli Rahma sanan yadawo da kallonsa kan Nawal, momynki tana aikine jeki kijirata afalo kinji d'iyar albarka. Kanta ta jinjina, ta ce, ''papa nakalli cartoon?. Eh babyna jeki saka MBC 3 kigani, muma yanzu zamu fito. Tafiya tayi abinta tana murna, shima yamaida k'ofar yarufe harda saka key. Bathroom yashiga yay wanka, dama Rahma tahad'a masa ruwan wanka, bayan yagama k'alk'ale k'alk'alensa yafito. Kujerar madubi yaja yazauna, yana cikin shafa mai yaga Rahma yatashi afirgice tana sambatar aunty Safna! Aunty Safna!!, Dan ALLAH karki mutu, A'uzubillahi minashshaid'anirrajim!, sai jikinta ke rawa, da Sauri. Bobo yamik'e yaje yajata jikinsa yarungume, yana kiran my Nusfulhayat nutsu kinji, mafarki kikeyi ba gske bane, nutsu. Hawaye tafara zirarwa, a'a my Nurulk'albi Dan ALLAH ka kaini na ganta, kacemin bata mutuba, wayyo aunty Safna karki tafi ki barni......... Kafin tarufe baki wayar bobo tafara wringing, dak'yar tayarda ya janyeta daga jikinsa yatashi yad'auki wayar, gabansane yafad'i shima Dan ganin sunan ya Shaheed 6aro 6aro akan screen d'in wayarsa. Haka kawai yasamu zuciyarsa dayin rawa, dakuma k'ok'arin gaskata mafarkin Rahma, shiyyasa ba'ason barcin la'asar yafad'a azuciyarsa yana kallonta. Ganin kallon dayake mata saita sake fashewa da kuka, cikin muryar kuka ta ce, "yan gidammune ko?, namasan zasu fad'amin aunty Safna na tarasune kawai...... Tasaki kuka maiban tausayi da tsuma zuciyar mai saurare. Kiran ya Shaheed ne yakuma shigowa, jiki a sanyaye yad'aga yakara akunne, muryar ya Shaheed kawai dayaji yasaka zuciyarsa karaya, bayan sungaisa ya Shaheed yasanarma bobo abinda nikaina banjiba. Cikeda tashin hankali ya ce, "ya Shaheed gamunan zuwa, koda suka yanke wayar.. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai bobo ke iya ambata, Rahma tataso ta warce wayar, ganin sunan Wanda yakirashi yasakata fashewa da kuka, matsowayayi Kusada ita ya ce, " addu'a Safna take buk'ata yanzu agaremu Rahma, kinga tashi kiyi wanka muje. Kasa tashi tayi, saishine ya d'auketa yakai bathroom yaymata wankan dakansa, dak'yar yasamu tayi wankan tsarki sanan suka fito, d'akinta yaje yad'akko mata wasu kayan, babu zancen shafa mai zirawa kawai tayi, shima yasaka doguwar riga kawai yakama hannunta suka fito. Afalo suka d'auki Nawal sai gidansu Rahma. Amotama sai kuka take, shima yakasa lallashinta Dan duk arud'e yake, tuk'i kawai yakeyi cikeda damuwa.............. π€ππππ *_"Hummm masu karatu akwai damuwafa, mikuke tunani gameda Safna??????."_* *_Luv you oll_* *_(((S)))........2017_* [11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ»typing........ β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£ _β’π ±π Ύπ ±π Ύβ’_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 6β£6β£ Ganin yanufi wata hanya daban yasa Rahma tsura masa idanunta dasuka k'ank'ance saboda kuka, yana kallonta tagefen ido kuma yakula magana takesonyi amma takasa, shima bai iya cemata komaiba, gudu kawai yake shararawa, ganin sunshigo cikin asibitin Rahma takuma yarda mafarkinta ya tabbata, guri bobo yasamu yay fakin kowa yafito jiki a sanyaye, banda Nawal dabatasan wainar da'ake toyawaba, cikin asibitin suka shiga kowa da abinda yake sak'ama zuciyarsa, Rahma takan share hawaye lokaci lokaci. A Reception suka tsaya bobo yakira ya shaheed. Babu dad'ewa saigashi yazo, Rahma tana ganinsa tafad'a jikinsa tana kuka, cirota yayi daga jikinnasa yana fad'in haba Autar Ummi bakisan kin girma bane?, kinga share hawayenki kinji. Cikin shashshekar kuka ta ce, ''yaya waye bashida lfy?. Ya ce, "safna CE." K'ara share hawayenta tayi ta ce, "yaya nasamma aunty Safna tarasu ko?. Idanunsa yazaro ya CE, "haba auta wayace miki tarasu?, a'a tana nan da ranta har yanzudai tana tareda doctor's ne. Ta share hawayenta tana kallonsa, to yaya miya sameta?. Muma bamu saniba Rahma saidai idan likitoci sun fito muji. To muje kokin manta bake kad'ai baceba?. Ita saima yanzu ta tuna tare suke da bobo Dan haka takalli Inda yake tsaye rik'eda hannun Nawal dake kuka tunda taga Rahma na kuka. Da sauri tazo taja Nawal jikinta ta rungumeta tana lallashi, bobo dai da ya Shaheed suna tsaye suna kallonsu. Ganin abun bana k'are bane yasa bobo matsawa kusada ita ya CE, " yakamata mu k'arasa ko. d'agowa tayi ta kalleshi saikuma takama hannun Nawal suka shiga ciki. Acanma tana ganin su Abba taje tafad'a jikinsa tana kuka, dak'yar ya lallasheta tayi shiru, bayan sun gama gaggaisawa suma sukabi sahun 'yan zaman tagumi. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Har akayi sallar magriba likitoci nakan Safna, su bobo dasu Abba suka nufi masallacin cikin asibitin, sudai su ummi da matansu ya Shaheed duk suna nan zaune jigum jigum, Nawal kam tuni tayi barci, ummi taciro d'ankwalin kanta dayake yanada girma tabama Rahma ta ce, "ta Goya Nawal, amsa Rahma tayi tacika umarnin ummi, gama goyon babu dad'ewa saigasu ya Muneer sun dawo daga masallaci, hakan kuma yayi daidai dafitowar doctors d'in kowa yana yarce gumi, da Sauri kowa yanufesu yana tambayar halinda safna take ciki, duk zame jiki sukai suka gudu akabar doctor Kaleel kawai, kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yana share gumi, ganin duk 'yan gidane ya sauke ajiyar zuciya, ya ce, " Alhmdllh munsami nasarar ceto ranta, yanzu haka tasamu barci, yanzuma za'a wuce da'ita d'akin Hutu danhaka Ku kwantar da hankalinku alhaji, komai yazo da sauk'i aii alhaji, sauran bayani kuma sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu. Alhamdllh suka fad'a gaba d'aya, godiya sukaima doctor Kaleel sannan yawuce office d'insa. Tafiyarsa babu dad'ewa aka gunguro Safna a d'an gadon marasa lfy, kwance take sharkaf tana barcin wahala, cikeda tausayi da addu'ar samun lafiya suka bita. Zuwa yamzu fuskokin kowa garage damuwa bakamar d'azunba. Bobo yamatso kusada Rahma ya ce, "My Nusfulhayat ki sauketa mana, aii yanzu Nawal tawuce goyo karkizo k'irjinki yana ciwo. Girgiza MASA kai tayi ta ce, "bafa tada nauyi ALLAH. YA munnir dake kusadasu yana jinsu ya ce, "aidama gida kuka tafi tunda anga yanda jikin NATA yake. Abba ya ce, " gaskiyarka muneer, Abdulmaleek kutafi gida hakanan, kuma su Muneer kud'auki iyalanku Ku tafi gida saboda yara dakuka bari.. Rahma ta turo baki gaba cikin shagwa6a ta ce, "Abba nidai anan zan kwana gsky. A'a auta bazai yuwuba, idan anbarki kin kwana anan mijinkifa, bobo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83