Chapter 17
Chapter 17
kuma tayimusu biyayya, saidai tunkan ayi nisa tafara hangen tarin matsaloli a rayuwar auren nata. Domin kuwa alissafinta yau kwana takwas da kawota gidannan, saidai tundaga randa aka kawota gidan bata sake saka angon nataba a idonta, saidai taji motsin shigiwarsa dakuma fitarsa, kocin abincinsa, idan tatuna kulawar dayayta bata awajen taron bikin saitaita mamaki wlhy, mutum tamkar mai aljanu, kodayake saitaga kamar itama akwai laifinta, tunda ad'aki take wuni, saidai idan taji yunwa tadameta tafita tad'ebo abincin da Ammi ta aiko musu, gidan kansa takasa nutsuwa taimasa kallon tsaf........ Kwala kiran sallar asubane yadawo da ita hayyacinta, tamik'e domin gabatar da sallar, jitayi jikinta duk yayi nauyi saida tayi wanka sannan ta d'auro alwala. Tana idar da sallah taji wani irin barci na d'ibarta, tashitai ta haye gado ta kwanta, cikin 'yan mintuna barci yay gaba da ita. A6angaren bobo kam yamaida dukkan hankalinsa wajen binciko Wanda yayma yarinyarnan fad'e, sukansu 'yansandan dukya addabesu da masifar basusan aikinsuba, sanin shi d'an babban mutumne yasasu dagewa sosai kuma ana hangen nasara zuwa yanzu. Rahma kam yana buk'atar ganinta amma aganinsa ita yakamata tafara nemansa tunda shine babban, ganin kamar tana shamasa k'amshi shiyyasa yafita harkarta ya maida hankalinsa akan aiki. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Sai k'arfe d'aya Rahma ta tashi, takai dubanta kan agogo, kai harnakai haka ina barci?, lallai nasha barci sosai. Wanka tashiga, bayan tafito tashirya cikin Riga da siket na atanfa kayan sun bala'in mata k'yau, tayi sallar azhur sannan tanufo kicin Dan cikinta yafara kiran ciroma, gashi jiya tacema Ammi adaina kawo musu abinci zata cigaba da girkawa, Dan aganinta yakamata tamik'e wajen juya akalar mijinta zuwa gareta. Alokacin Bobo yana gidansu, Nawal tamak'ale masa saita biyoshi yakawota wajen momynta. Ammi ta ce, "Mukarram inaga katafi da ita kawai nasan insha ALLAHU Rahma zata rik'eta da Amana, kasan yarinyarnan kullum burinta ta kasance da mamanta akullum. Bobo yahad'iye yawu Ammi ba tafiya da Nawal bane matsalar ina ganin kamar idan nad'auketa ban k'yauta mukuba. Ammi tayi murmushi Wlhy ko d'aya mukarram aii munsan ba k'waceta kayiba, dama tunjiya Appanku yay maganar yau idan kazo kawuce da ita. To shikenan Ammi ngd, ahad'a mata kayanta to muwuce. Ammi tahad'o mata kayanta, wasu kam sai ahankali aringa kaimata. Nawal kam sai murna take yau zata wajen momynta. Ammi bari mutafi naga Appa haryau bai dawoba, gobe idan ALLAH yakaimu ma had'u, Dan zan koma aiki. Ammi ta ce, tom ALLAH yatsare, yakaimu lfy, tazo gefen Nawal tana d'aga mata hannu. Bobo yatada mota, yauwa Ammi idansu khairy sun dawo suhad'amin kayana duka Nima. To zan Sanar musu agaidamin da d'iyar tawa. " zataji." Haka suka fice ammi da Nawal suna d'agama juna hannu. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Rahma na zaune a falo tazurama filet d'in indome idanu, dukda 'Yar Karen yunwar datakeji amma abincin yagagara ciyuwa agurinta. Tabi falon da kallo, caraf idanunta suka sauka akan wani hoton Bobo yana zaune akan wata kujera, fuskarsa d'auke da tsadadden murmushi mai kashe zuciya, saina kusadashi shida Nawal, wanikuma a can gefe shida yayyensa maza dasu Ammi da khursiyya da khairiyya, sunyi k'yau sosai, daka gansu Kasan ciki d'aya suka fito masha ALLAH.... DA gudu Nawal tashigo tana kiran Momy! momy!!, da Sauri Rahma tamik'e Nawal tafad'a jikinta, itama saita rungumeta. Ahankali Nawal ta ce, momy I miss u. Miss u too my baby Rahma tafad'a tana mamakin 'Yar waye kuma wannan?. Nawal takatse mata tunani da fad'in , momy inakikaje kika barni?, kullum saina tambayi baby da Ammi sai sucemin kina zuwa amma baki zoba. Cikin mamaki Rahma tad'agota daga jikinta tana kallonta, gata 'Yar mitsila sai zance irin na manya. Bobo na a tsaye yana kallonsu, Wanda azahiri kallonsa akan Rahmane, Ashe k'yan dayake kallonta dashi awajen taron biki tafi k'yau a Natural batareda kwalliyaba..... Maganar Rahmace takatse masa tunani, ta kuma rungume Nawal tana fad'in tom gani nadawo babyna kiyi hak'uri kinji. Ita sai yanzu tatuna ance mata Bobo yanada d'iyama, jitayi tausayin yarinyar ya mamayeta, ALLAH sarki Rayuwa, ALLAH baya Barin wani Dan wani yaji dad'i, tafad'a acikin ranta. Nawal tazare jikinta tanufi Inda Bobo yake, hannunsa takamo cike da murna tana fad'in baby naga momyna yau. d'an murmushi yayi ya ce, "natayaki murna babyna, karasowa cikin falon sukai yazauna. Rahma ta daure ta ce, ina yini?. Lfy ya amsa batareda ya kalletaba. Rahma ta ta6e baki aranta ta CE, " dama baka amsaba aii, dama na gaidakaine saboda kana gaba dani. Maganar Nawal ce tasakata dawo da hankalinta Kansu, Nawal ce takai bakinta Kusada kunnen Bobo wai zata masa Rad'a, amma kuma kanajin maganar tata. "Baby mikayima momy tak'icin abinci?, koka duketane?. Da sauri Bobo ya kalli Nawal a'a baby ban daketaba, k'ila batada lfyane. Tamaido dubanta kan Rahma, momy waibakida lfy inji baby. Rahma tayi d'an murmushi A'a lfy ta k'alau, to momy idan lafiyarki k'alau miyasa bakici abinciba?, ko kinaso baby yabaki dakansane?...... Kafin Rahma tayi magana Nawal tamaida dubanta ga Bobo, baby kabama momyna abinci abaki kamar yanda kake bani idan nak'ici. Bobo ya ce, "to baby idan banda abinki....... Da Sauri ta ce, "baby indai baka bama momyna abinci abakiba mun 6ata daga yau, ta tashi daga kusadashi takoma kan cinyar Rahma data daskare azaune danjin furicin Nawal. Rahma tadaure ta ce, ''kinga babyna zanci dakaina, Dan lfy ta k'alau, kibar Dady yahuta kinga ya gaji ko, tashima muci tare. Nawal ta tashi zaune, Rahma taringa bata abincin itama tana dannawa badan yaymata dad'iba, saboda damuwar dataima zuciyarta yawa. Bobo yanad'an satar kallonsu, tabbas yaji dad'in yanda Rahma takar6i d'iyar tasa wadda akullum yake zullumin sama mata madadin mamanta data rasa...... Yanata tunaninsa harsuka mammala, Nawal ma tafara barci, mik'ewa Rahma tayi da ita zuwa d'aki, dama zaman dukya gundireta. Yabita da kallo k'asa k'asa babu laifi tanada k'yau daga na fuska harna jiki, saidai bazai sotaba Dan Ni'imarsace kawai keda gurbin zama azuciyarsa. "na ce, "hummmm ALLAH yasa." Itakam Rahma koda takwantar da Nawal saitayi zamanta bata sake fitiwaba, sai bayan sallar la'asar. Sannan baya falon, tanufi kicin tana fad'in baridai yau nayi girki kodan Nawal, had'ad'd'en abinci na gargajiya tahad'a mairai da lfy, tagyara kicind'in tsaf kamar ba'ayi komaiba, hakama falon takuma bad'e ko ina da nau'in turarurrukan wuta. Saida tayi Sallar magriba sannan tayi wanka tayima Nawal, shiri tayi cikin wando dariga na Pakistan sky blue, rigan iya cinya sai wandon yakamata sosai, amma tayi k'yau kamar kasaceta kagudu, itama Nawal tasaka mata 'Yar Riga Mara nauyi. Harzasu fito Nawal ta ce, "saita goyata, Rahma taduk'a Nawal tad'ane. Falon suka fito inda ta tarar da Bobo zaune akan kujera mai d'aya ya d'ora k'afafunsa saman k'aramin tebir na gilas yana karanta jarida, gefensa lemo na kwali da Kofi anzuba rabi, yana sanye da wando 3/½ fari da riga ja Mara hannu. Masha ALLAHU Rahma tafad'a azuciyarta. Baby kalleni Nawal tafad'a tana d'agama Bobo hannu. d'an d'agowa yayi ya ce, " naganki baby yamaida Kansa. Rahma tasauketa tana fad'in tonima gobe saikimin goyon. Nawal tawaro idanu waje kamar wata babba, lah momy bazan iyaba saidai baby yay miki, taje tadafa bobo, baby. Ya ce, "na'am. Zaka ramama momy goyon data minko?, kagani ban girmaba, bazan iyaba.. Bobo yakalli Rahma dake zaune tana mamakin wayau da surutu irinna Nawal, Dan yau d'aya tafahimci Nawal d'in tanada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83