Chapter 68
Chapter 68
yad'an shafa Kansa idonsa ak'asa ya ce, "Abba abarta ta kwana Indai Dan tanine babu wata matsala. A'a a aiba hauka akeba Cewar ummi dake Harar Rahma. Abba ya ce, "kutafi gida kinji auta, ALLAH yay muku albarka gaba d'aya, gobe idan ALLAH yakaimuma aii ranace ko. Bobo ya ce, " to Abba bara muyi sallar isha'i, Dan komun tafi a hanya zata riskemu. Eh gsky ne to kubari ayid'in. Bayan sallar isha'i badan Rahma tasoba suka fito gaba d'aya harsu ya Shaheed da matansu domin tafiya gida. Abba da ummi kad'ai aka bari a asibitin zasu kwana. Har yanzun Nawal tana bayan Rahma agoye saida zasu Shiga mota bobo ya taimaka mata ta sauketa ya kwantar da ita a sit d'in baya sannan suka Shiga mota kowa yanufi gida. Babu maima wani magana harsuka Shiga cikin gidan, bayan mai gadi yabud'e musu suka Shiga, bobo yay fakin suka fito, harzata d'auki Nawal ya ce, "tabari ya d'auketa, bata Musa masaba tabari ya d'auketa suka Shiga cikin gidan. Har d'akinta yakai Nawal ya kwantar, ita kuma tashiga wanka. Shima d'akinsa yanufa yacire doguwar rigarsa yasaka kayan barci, fitowa yayi yanufo dinning Dan yunwa yakeji. Rahma tafito wanka ta rama sallolinta sannan tanufo falo domin d'aukar Abu. Ganin bobo zaune a dinning yatuna mata dabaifa ci abinciba Ashe, jitayi yabata tausayi, tak'araso Inda yake tana fad'in sorry Nurilk'albi muntafi ko abinci bakaciba. Murmushi yay mata ya ce, " karki damu o, kina arikicannan ta'inama zaki tuna da cikina. Marairaice fuska tayi tamkar zatayi kuka, ta ce, "pls kamin afuwa. Ayya my Nusfulhayat karki damu ai nasan bakiyi da niyyaba. Itama murmushin tamasa. Ya CE, " babynkifa?. Tana barcinta har yanzu. OK tom zoki zauna muci abinci, Nima yunwace ta addabeni shiyyasa ban nemekiba. d'an yatsine fuska tayi tareda ta6a cikinta ta ce, "nikam na k'oshi." Kamo hannunta yayi, yajawota ta zauna saman cinyarsa, shima hannunsa ya d'ora akan cikin nata yana shafawa ahankali, haba my Nusfulhayat kinaso ki haifamin babyna d'an k'aramine?, nifa k'atoto nakeso Wanda Nawal zata d'auka da k'yar. Kallonsa tayi tad'an juya idonta dasuka kummbura saboda kuka, tasaka hannu tarufe fuskarta tana fad'in Nurulk'albe baby kuma?, a INA?. Hannunta ya janye ya d'aga mata gira, ya ce, "acikinki mana. Tad'an zaro ido tana tura baki gaba ta ce, " nidai kabar fad'a. Ya ce, "miyasa?." Since kanta tayi ak'irjinsa cikin sassanyar murya ta ce, "wlhy inajin kunya. Tabashi dariya Dan haka yay murmushi mai sauti tareda d'agota yana fad'in Ashe kunyarnan har yanzu ban gama fiddataba?, shikenan nadaina tashi muci abincin. Girgiza masa kai tayi. Ya ce, " pls ko kad'an kici. Yunk'urawa tayi zata tashi, ya maida ita ya zaunar, no yizamanki kawai. Badan tana son cin abincinba ya matsa mata, dakansa yarink'a bata shima yanaci, tana zame zame damasa ta6aradai har sukaci da d'an yawa sannan suka mik'e, ya taimaka mata suka gyara wajen tsaf sannan kowa yanufi d'akinsa. Harta kwanta ta rungume Nawal taji motsin shigiwarsa shima gadon yahawo, suka saka Nawal a tsakkiya, yamusu addu'a ya shafama kowa sannan yahad'asu yarungume sai barci.. Nima dai homajeep d'in k'afafuna naja natafi wajen my Abdul d'ina nabar Rahma Dana itama.😜 .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Washe gari bayan sunyi breakfast Rahma tabisu, yasauke Nawal A school sannan suka nufi asibitin. Har cikin yashiga shima, yatayata d'aukar kulolin kayan breakfast d'in Data had'o musu, ahanya suka had'uda Abba zai fita, suka rissina suka gaisheshi, cikeda fara'a ya amsa musu, Yakoma yimusu bangajiyar jiya, suma suka tambayeshi yamai jiki?, ya ce, "a dasau kam Dan tana nanma zaune yanzu haka. Alhmdllh suka fad'a atare. Ya ce, "kuk'arasa ciki to, nima zanje gidane na shirya nawuce kasuwa. Saika dawo. Da sallama suka shiga d'akin, Safna tana zaune akan gado tajingina bayanta da filo, hannunta manne da k'arin ruwa. Ummi na zaune agefenta tana had'a shayi, d'agowa sukayi gaba d'aya suna amsa sallamar, Safna kallo d'aya tamusu ta kauda kanta. Ummi ta tashi tareda turama bobo kukerar tace ya zauna. A'a ummi kiyi zamanki, zanma wuce wajan aikine, rissinawa yayi ya gaidata da tambayar maijiki, ta ce, "jiki Alhmdllh tunda gata azaune hartana magana. Ya ce, "ALLAH yak'ara sauk'i. Ameen ummi tafad'a tana fita. Rahma dake Kusada Safna tsaye tana tambayarta yajikin?, da k'yar ta amsata, Rahma dai bata kawo komai arantaba duk zatonta zafin ciwone. Ummi nafita bobo ya kalli Safna, ya ce, " antynmu ya jikinki?. d'ago manyan idanunta tayi ta kallesa, ahankali ta ce, "da sauk'i. Ya ce, " ALLAH yak'ara sauk'i, yasa kaffarane. Amin tafad'a a saman la66anta. Shiru nawani d'an lokaci, bobo yakalli agogon hannunsa sannan yakalli Rahma, my Nusfulhayat bara nawuce ko, kinsan yau k'arfe 10 zamushiga shari'armu dasu Alhaji Abdurrazaq. Itama kallonsa take tana d'an murmuahi ta ce, "to Nurulk'albi ubangiji ALLAH yabada nasara, yakuma d'oraka akansu. Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ahankali yabud'e akanta ya ce, " ngd sosai da addu'arki gareni my Nusfulhayat. Murmushi kawai tamasa batareda tace komaiba. Yamatso daf da ita, bata ankaraba taji kiss akumatunta, d'an zaro ido tayi tana kallonsa, shikuma yad'aga mata gira sannan yamik'a mata kumatunsa wai tamasa kiss, hannu tasaka tarufe fuskarta tareda fad'in kai Nurulk'albi nidai a'a gsky. Dariya yayi ya ce, " shikenan aii, ya kalli Safna da bak'incikin abinda sukeyi agabanta tamkarma sun manta da ita ya tokare mata mak'oshi. Auntynmu ALLAH yak'ara lfy fa, bara natafi office time natafiya, sai dai ganinki yasa matana takasamin adawo lfy. Murmushin yak'e Safna tayi Wanda duk Wanda yagani yasan tabbas na yak'ene, ta ce, "a'a nikam babu ruwana.. K'ofar yabud'e zai fita sannan yajuyo ya kalli Rahma yakashe mata ido d'aya yafice. Murmushi Rahma tayi tana girgiza kai. Safna tazame ta kwanta idanunta cikeda kwalla. Ahaka ummi tashigo ta samesu, sai yanzu Rahma tasami damar gaida ummi. Ummi takama hannu Rahma suka zauna ta ce, " autana ina d'iyar takine?. Tana makaranta ummi, saida mukama ajiyeta sannan muka wuto nan, ALLAH sarki aii yarinyar tanada Shiga rai wlhy, gatada wayonta masha ALLAH. aii ummi saima kin zauna da Nawal wlhy, yarinyar batada damuwa ko kad'an..... Haka sukaita hirar Nawal, Safna tana kwance tana jinsu amma tayi shiru, da k'yar ma ummi tasata ta tashi tayi breakfast da kayan Rahma data kawo. Ummi saiyabama girkin Rahma takeyi itakuma tanatajin dad'i, Safna dai batacemusu k'alaba har doctor yashigo yaduba jikinta yacire k'arin ruwan. Fitar doctor babu dad'ewa saigasu ya muneer da matansu, suma basu dad'e dazuwaba saiga 'yan gidansu ya Kamal, harma dashi ya Kamal d'in, saikuma ga Appa Ammi da inna, nanfa akashiga gaishe gaishe datambayar mai jiki. Zuwa azuhur asibin yacika da dangi, sunata tururuwar zuwa ganin Safnar, haka suka kasance da dangi, kowa yaga Rahma saita burgeshidantakuma yin bul bul da ita, ga wani k'yau da murjewa data k'ara na musamman. Aunty yahanasu Maman Basma ma cewa tayi 'yata kodai nasamu jikane?, irin sannan k'yau haka?. Hannu Rahma tasa tarufe fuskarta, aiko mutanen d'akin sukaita mata dariya, mamansu ihsan ta ce, "wlhy yaha nimadai tun d'azu nake kallonta, Abdulmaleek yarik'e mana ita da k'yau, ALLAH dai yak'ara baku zaman lfy. Akace amin. Duk firarnan da akeyi Safna jitake tamkar ta had'iyi zuciya tamutu, duk saima taji tatsani 'yan cikin d'akin. Na ce, " Safna aiduk Wanda baiji bariba to zaiji hoho.😜 .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Haka Safna tacigaba da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83