Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

3⃣9⃣=4⃣0⃣ _washe gari_ Rahma tatashi tayi duk abinda tasabayi dukda tasan yau weekend Bobo bazai fitaba, tana cikin saka turare a falo bobo yafito sanye da jallabiya ruwan toka mai gajeren hannu, rissinawa tayi ta gaidashi, kamar yanda yasaba ya amsa da lfy. Amsa gaisuwar nan nabama Rahma haushi, amma babu yanda zatayi. Yad'anbi falon da kallo komai tsaf, gawani k'amshi na musamman, yana jin dad'in kasancewarta mace mai tsafta. Itadai cigaba tayi da abundan takeyi. Ya ce, "bari nad'anje wani waje nadawo. Aranta tace kofa wanka bakayiba, amma afili ta ce, " to ga Break. No barinaje nadawo, aiba dad'ewa zanyiba, yafad'a yana ficewa. Itama ta ce, "ALLAH ya tsare. Dukda yafita amma yajiyo addu'arta. Bayan takammala saka turaren zuciyarta tabata shawara dataje ta gyara masa d'akinsa, kamar bazatajeba saikuma tatuna nasihar mahaifiyarta da ummansu Basma. d'akin tanufa da tunanin ALLAH yasa bai rufeba, tana tura k'ofar tabud'e, k'amshinnan yana nan kamar kullum, yau tanutsu takalli ko ina na d'akin, komai farine tas, aranta tace farin Abu name tsaftane. Sai manya manyan hotunanan Ni'ima Maman Nawal, bani gurin ita kad'a, wani gurin kuma shida ita. Ko kad'an bataji haushiba bare kishinta, Bata 6ata lokaciba tafara gyara ko ina, Dan danan tagama d'akin yak'ara d'aukar haske komai yana d'aukar ido. Bathroom tashiga zata wanke saitaga kaya ajik'e abokiti. Shiru tayi tana tunanin ta wanke kota barmasa abinsa, wata zuciya ta ce, " ki wanke, kobabu komai zaki samu lada aii. Haka tazauna tahau wankin gajerun wandunansa da vest, akunyace take wankin tamkar tana gabansa, gudu gudu sauri sauri tagama bataso yazo yataddata tanayi. Dandanan tagama tawanke bayin, tad'auki kayan tafito waje, acan baya taje tashanyasu sannan tadawo d'akinta tashiga wanka, Dan Nawal bata tashiba. Shigarta wanka babu dad'ewa yashigo gidan, d'akinsa yanufa kai tsaye, baki da hanci da ido yasaki yana kallon d'akin NASA, yalek'a bayi nanma fes, bokitin daya jik'a kaya wayam, wani lallausan murmushi yasaki, labulen window d'insa yad'aga, can yahango kayan ashanye. Jiyay wani Abu nata6a zuciyarsa, afili ya ce, ''ALLAH yaymiki albarka. Fitowa yayi yanufi d'akin Rahma, hakan yayi daidai da fitowarta daga wanka, daga ita sai guntun tawul iya cinya. Wata tsayuwar sojan badakkare bobo yayi, sai Raba idanu yake akan Rahma, da wannan munafikin kallon nasa k'asa k'asa. Itakam dukta rikice, waige waigen abinda zata rufe jikinta kawai takeyi, can ta hango hijjabin sallarta, amma dole saitabi tagabansa zata d'auka, ganin haka saikawai takoma cikin bayin da sauri. Murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya, yak'arasa inda hijjabin sallarta yake yad'auka, ahankali yak'arasa har k'ofar bayin ya kwankwasa, Rahma dake jingine da k'ofa tagwalo ido waje, k'irjinta sai dukan Tara Tara yakeyi. Yak'ara kwankwasawa. Muryarta narawa tamkar zatayi kuka tace yes, yanda tayi maganar tabashi dariya amma saiya gimtse ya ce, "bud'emin k'ofar. Innnalillahi tace azuciyarta, wai mi mutumin nan yake nufi.........maganarsa ta katse mata tunani, " wai kobaki jinane?. Bayan k'ofar takoma tala6e sannan tabud'e, gaba yay tamkar zai Shiga, saikuma yamik'a mata hijjabin, dasauri takar6a tamaida k'ofar burum tadatse. Girgiza kai yayi yanad'an ta6e bakinsa, yazauna bakin gadon yana shafa kan Nawal daketa barcinta hankali kwance, shi mamakin kansama yakeyi, wai miyake jirane?, zuciyarsa ta ce, "kanason sake kallon Rahma ne. d'an tsaki yaja yamik'e yafice, shi adole zuciyarsa tayi k'arya. Saida taga yafita sannan tafito, taje tasakama k'ofar key, sannan tazauna tagyara jikinta, tasaka Riga da wando na Pakistan, nakula tana son irin kayannan sosai. Nawal ta tashi itama tayimata wanka tashiryata cikin wandon Jin's da pink d'in T shert mai k'yau. Falo suka fito, fitowarsu babu dad'ewa shima ogan yafito, haryayi wanka yashirya cikin jins blue da farar Riga sai zabga k'amshi yakeyi. dinning suka nufa, Rahma sai sinne kai takeyi Dan kunya, shikam ko'a kwalar rigarsa, yanacin abinci Nawal namasa surutu, iyakarsa Yamata murmushi koya d'aga kai. Rahma ta ce, " azuciyarta, muskili kafi mahaukaci ban haushi. Suna kammalawa Nawal taja hannun Rahma wai suje tamata lilo, fitowa sukai sukabarsa kwance saman doguwar kujera yana kallon film. Sunacan a lambu Rahma NATA biyema Nawal suna lilo, jiyay falon babu dad'i Dan haka yafito, jiyo dariyarsu alambu yasashi nufarcan, Rahma na zaune akan lilo, Nawal na shillata suna dariya, k'arasowarsa yasa Nawal cewa lah papa kaima zona lilaku. Kai ya girgiza mata alamar A'a. Takwa6e fuska zatayi kuka, cikin takun k'asaitarsa yak'arasa wajen lilo d'in, Rahma tayi yunk'urin sauka Nawal ta ce, "momy kubiyufa zanyimawa, sandarewa Rahma tayi azaune, kafin ta farga Bobo ya haye lilo d'in amma d'an nesa da ita. Da k'arfi Nawal ta hankad'a lilo d'in, aiko sukayi gaba kamar zasu fad'i, da Sauri Rahma ta ruk'unk'ume Bobo, shima yarik'eta. Nawal Yar kwal uba tacigaba da lila lilo da k'arfi, basuda za6i bayan rik'e junansu dak'yau, Nawal dai sai dariya takema iyayen nata, saida tagaji Dan kanta sannan tadaina lilasu. Bobo yabud'e idanunsa ahankali danjin lilo ya tsaya, ga Rahma na mutsu2n kwace kanta, yana sakinta tasauka, da Sauri tabar wajen, binta da kallo yayi yana murmushi, Nawal takatse masa tunani, baby d'orani muyi tare tunda momy tagudu. daukarta yayi yad'ora sukacigaba da lilonsu zuciyarsa cikeda tunani kala kala. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Safna zaune gaban Abba da ummi da alama fad'a ake mata, Dan fukarnan adagule take. Abba ya ce, " wlhy nabakinan da wata uku zuwa hud'u kifito da miji a had'a aurenku keda amira, inbandama auren ameerar da sati biyu zan baki, amma Abubakarne yaceceki ya ce, "abari ahad'a bikin dan a samu sauk'i." To saikiyi gaggawar sanar da Wanda kikace kinason harkikaso wulak'antamu akansa. Insha ALLAHU Abba zan kawoshi, nidai kuyi hak'uri kubar ganin laifina, ALLAH yariga yarubuta Dama shid'in Mijin k'anwatane baniba... Dallah yimana shiru!!, ummi takatseta atsawace, Mara mutunci kawai, Indai duniyace aigaki gata nan, kuma koyaya Wanda kikace kinason yake wlhy haka ZAMU aura miki shi, kijecan kiji da bak'in halinki, tashi kibamu waje mu. Mik'ewa Safna tayi tabar falon tana k'unk'uni. Na ce, " ALLAH ya shirya to. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Ad'an hanzarce takeyin aikin gidan, Sauri take tagama dawuri taje tayi girki Dan maigidan ya ce, "mata yau abokinsa zaizo da iyalinsa, tagama komai tsaf har girkin ta kammala d'akin bobone kawai yarage mata shima Dan yana kwance ad'akinne. Saiwajen 12 yafito daga d'akin yafita danufin siyo ruwa datace masa babu. Yana fita tashiga d'akin Dan gyarawa, tagama aikinta lfy lau, tsautsayi yasa takai hannunta kan wani hoton Ni'ima datayi bala'in k'yau, Ashe bai zauna da k'yauba aiko yafad'o jikake taratsatsa!!! ya tarwatse ak'asa abinka da gilas. Hakan yayi daidai dashigowar Bobo falon, da hanzari yanufi cikin d'akinsa, aiko abinda yake zarginne yagani, dandanan fuskarsa ta canja kama idonnan sukayi ja danshi aganinsa da gangan Rahma tayi saboda batason ganin hotunnan tunda dai yasan mata da kishi. Tunda yashigo jikinta ke rawa, tabud'e baki arazane zatayi masa magana yadaka mata tsawa. Dallah yimin shiru, dama kina shigowa gyaramin d'akine danki kashemin hotuna?, to wlhy idanma kishi kikeyi da ita kidaina Dan babu yanda kika iya da ita, wannan dakike gani itakad'aice nabawa zuciyata, daga itakuwa babu wata mace dazata samu haka daga gareni, wlhy akan wad'an nan hotunan sainayi mugun sa6a miki, banason cikin da iskanci. Rahma tamatso danufin tsugunnawa tabashi hak'uri amma abisa tsautsayi ta taka gilas ak'afa, runtse idonta tayi saboda azaba, dama ga hawaye tuni sun wanke mata fuska. Tsawa yasake

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});