Chapter 41
Chapter 41
yafara cika da yara, matansu ya sulaiman da yaransu duksun iso, tare suketa hidimar had'a abinci, ga kayan rabonan ank'ukkula, zuwa k'arfe hud'u duk Wanda suka gayyata ya iso gidan. Awannan lokacin kuma bobo da nawal suna can sun lodo kaya daya sayama Nawal sun kamo hanyar dawowa gidan, dukda abinda Rahma ta masa da safe saiyaji baiji haushintaba sosai, tun awaje yakebin motocin da akayi fakin awaje da kallo, aransa ya ce, "k'ila wani gidanne a anguwar sukayi bak'i, yay hon maigadi yalek'o, ganin shine yasa yak'araso wajen mortar batareda yabud'e masa gate ba. A'a yabaka bud'emin gate ba kuma?. Aii oga wlhy babu wajen fakinne aciki. Kamar ya babu wajen parking?, mike faruwa acikin Gidan?. Mai gadi yad'an Sosa kai Dan Rahma ta ce, " karya fad'a masa, ya ce, "saidai kashigo kagani oga. Bobo yagirgiza kai kawai batareda ya tankaba yanemi waje awaje yay fakin suka fito shida Nawal, wayoyinsa kawai yad'auka amotar Yakama hannun Nawal suka nufi cikin gidan, bin ko ina yake da kallon mamaki yajinjina kai tareda nufar cikin gidan, suka shiga falon nanma shiru babu alamar akwai mutane awajen, baigama tunanin mike faruwaba yaji yara suna tafi dafad'in. *_“happy happy birthday to you, happy happy birthday to you...... Saikuma gasu Rahma suma sun fito”._* Aibaisan sanda yasaki lallausan murmushiba, dama abinda Rahma tashirya kenan shiyasa tak'i binsu?, jiyayai tak'ara girma da daraja azuciyarta. lol Na ce, " hummm gaba gabadan bobon Appa. ------------------------ Daganan aka shirya Nawal cikin kaya masu k'yau, shima ogan kwalliya yakuma ci, aka fara gudanar da biking birthday d'in Nawal. Masha ALLAH komai ya k'ayatar abin burgewa. Wajen bada cake Nawal tacuro tasakama babanta tasakama Rahma, tabi sauran iyayen matansu ya hamza dukta basu, su khairiyyama haka, daganan aka fara cashiya. Biki dai bai tashiba sai gab da sallar magriba. Masu tafiya suka tattafi, akabar yaransu ya hamza kawai da matansu, bayan isha'i suma mazansu suka iso, saida sukaci sukasha akasha hirara zuminci sannan kowa ya kwashi family nasa sai gida. Bobo ya tsarama kansa wani Abu yau, amma saiyaji wai agidan su khursiyya zasu kwana, ba k'aramin haushi abin yabashiba amma saiya dake tunda bashida yanda zaiyi. _bayan kwana hud'u_ Duk burin da bobo yaci akan Rahma ya rushe Dan har sannan su kursiyya suna gidan, doledai yad'aga k'afa. Ranar Litinin da safe su khursiyya suka koma gida abinsu, shima bobo yafita aiki, Nawal kuma tana makaranta sai Rahma kawai agidan. Tayi aikinta tagama komai tsaf, 1:30pm tana zaune afalo tana kallo wayarta tayi wringing da sauri ta kalli wayar bak'uwar no. ce, shiru tayi Dan yau tunda tatashi gabanta ke fad'uwa, har wayar ta yanke bata d'agaba aka sake kira, ganin babu dacewa arashin d'aukar yasa ta d'auka tunda batasan ko wayeba. Sassanyar muryarsa tadaki kunnenta, ta sauke ajiyar zuciya wadda yajita har yatsan kafarsa, yad'an lumshe idanunsa yabud'e tareda jingina da kujerarsa, ahankali yake d'an lulita, ya ce, ''matsoraciya da kinzata waye to?. Murmushi tayi ta ce, "nifa ba tsoro najiba, baki yata6e tamkar yana gabanta ya ce, " dama zancemikine kid'aukko babynki a school yau aiki yamin yawa a office bazan samu damar d'akkotaba. Okey babu damuwa. So zaki iya deriving d'in ko?. Eh zan iya. Okey tom ALLAH ya tsare, saina sake kira....... d'if ya kashe kafin tayi magana, murmushi tayi kawai tamik'e tacanja kayanta. d'akinsa tashiga Dan key d'in motarta yana hannunsa, tagama dube dubenta bata ganiba, sai wani na jar motarsa a durowar gefen gadon, shita d'auka tafito. Tashiga motar daketa tashin k'amshi, tana mamakin turaren da Bobo yake amfani dashi haka, komai nashi Yakama k'amshin turarensa, mai gadi yabud'e mata gate tafice. Tafiya take ahankali saidai wani Abu mai kama da tsoro yana ta6a zuciyarta Dan tunda tafito daga gida take gani kamar wata bak'ar mota nabinta abaya, ajiyar zuciya tayi dataga motar kamar ta6ace, dahakadai tak'arasa makarantar su Nawal ta d'akkota. Labarin makaranta Nawal keta bata, amma itafa hankalinta yafara tashi Dan yanzuma k'ara ganin motar d'azu takeyi. Sunzo daidai danja ta rik'esu saikawai taga anbud'e motarsu anshigo, atsorace takalli bayanta saitaga wasu zaratan samari majiya k'arfi zaune tamkar motar gidansu, d'aya yanunata da bindiga, d'ayan kuma yatoshe bakin Nawal. ga Motar bak'in Gilas ce, nawaje baya ganin naciki............... *_“😳masu karatu nikamdai atsorace nake, kosuwaye wad'annan mutane?, mikuma zasuyima Rahma da Nawal?.”_* Hummmm koya zata kaya?????????. _kutayamu murna my sister d'ina ta haihu mace._ *_luv u oll my fan's_* *_(((S))).....2017_* [11/12, 2:56 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{🅱🅾🅱🅾}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 5⃣1⃣ Babu dad'ewa aka basu hannu, tuni jikin Rahma yajik'e da gumi dukda AC dake aiki amotar, jikinta sairawa yakeyi, duk addu'ar datazo bakinta karantawa takeyi. Dakansu suke nuna mata hanyar dazatabi, sunyi nisa sosai datafiya awata hanyar k'auyen da Rahma batasan ko inaneba, wayartace tayi wringing harzata d'auka Wanda yake rik'e da bindiga yadaka mata tsawa, kina d'agawa zan tarwatsa kanki. Janye hannunta tayi da sauri akan wayar, Wanda yake rik'eda Nawal ne yad'auki wayar, saidai kafin yad'aga ta katse, wata uwar dariya yashek'e da ita Dan ganin sunan daya kira Rahman, *_dadyn Nawal_*. Wani gida suka kaisu, zuwa sannan Nawal tayi barci, Dan sun shak'a mata wani abune, Rahma tarungume Nawal tana kuka maiban tausayi, aranta tana tunanin misukayima wad'an nan mutane dazasu kawosu nan??. Bobo kam hankalinsa yafara tashi Dan ganin yayima Rahma kira wajen 10+ amma bata d'agaba, dukda d'umbin aikin dake gabansa haka ya tureshi yabaro office d'in. Makarantar su Nawal yafara zuwa, auntyn su ta ce, "aii tund'azu bayan yakira kamar yanda ya ce, " momynta ce tazo ta d'auketa, to babu dad'ewa tazo ta d'auketa..... Bai tsaya yagama saurarentaba yayo waje, daga nan gidansa yanufa, tun a gate yatambayi mai gadi, amma ya ce, "basu dawoba. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai yake ammabata azuciyarsa, amma dukya birkice, da sauri yaciro wayarsa a aljihu yakira khursiyya, itama ta ce, " basu zoba, Abu kamar wasa dukya rewad'e dangi dakira amma kowa amsa d'aya yake bashi *_basu zoba_*. Cikin rawar jiki yakira Appa yaturo masa number Abbansu Rahma. Cikin girmamawa ya gaidashi, tareda masa bayanin shine, Abba ya ce, "ALLAH sarki Abdulmaleek ngd ALLAH yayimaka albarka, ya su Rahma d'in?. Tun anan jikin bobo yayi sanyi, murya asark'e ya ce, " dama ita zantanbaya ko sunzo nan gidan?. Kai A'a gsky Rahma batazoba, kunyi da'ita zatazone?. A'a Abba dama...... Nan yafad'a masa yanda akayi. Abba yaja numfashi, to mud'an k'ara hak'iri zuwa d'an anjima mugani kota biya wani wajen, dukda dai nasan wannan baya d'aya daga cikin halayen Rahma, tabbas da Safna cema bazan damuba Dan nasan tanada rawarkai, amma Rahma kam batada wannan halin. To abba. Kawai bobo yafad'a ya yanke wayar, kuma kiran Number Rahma yayi amma ank'i d'auka, yadafe Kansas tamkar zai FASA ihu, yana nan tsaye ak'ofar gate saiga ya ishaq da ya Hamza, suka tambayi yanda akayi yasanar dasu. Ya hamza ya ce, "kasanarda Ammar ne?.” Girgiza kai kawai bobo yayi danya kasa magana, ya Hamza yakira Ammar yayamasa bayanin kimai, salati ammar yashiga yi, bai tsaya 6ata lokaciba yabaza yaransa ki ina. Al'amarifa kamar wasa hardare babu wani bayani, zuwa yanzun labari yakarad'e dangi, bobo kam dukya fita hayyacinsa, sai kuka yake tamkar mace, shidama haka yake akwai jarumta amma Abu kad'anne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83