Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abinci, wanke fuskarta tayi tafito tana murmushin yak'e, ganinan aunty ummy wani abune yashigarmin ido shine nake cirewa. Ayya sannu yafita ko?. Eh ya fita aii ruwa naita sakawa. To sannu, muje muci abinci ko. To kawai tace mata suka fito falon k'asa inda kowa yake har Ammi, mazan ne kawai babu suna sama tareda Appa. Aunty Sameera ta ce, "a'a INA safna wai?. Da sauri Rahma ta ce, " tana waje tana waya, aii muci abincinmu kawai wannan ba yanzuba, idan tafara waya sai ALLAH. Dariya sukayi gaba d'aya, aunty rasheeda ta ce, "wlhy kubarta ta soye abinta, itama muje musha biki, tunda tak'i bobon mu, madai gani ko guy d'in nata yafishine haka?. Babu Wanda yace komai saidai anyi dariya, harda Rahma datayi na yak'e, tasan sarai habaici aunty Rasheeda tayima Safna, amma bataga laifintaba tunda itama ga aunty Safnar can suna cin dunduniyarta itada mijinta datad'auki so ta d'ora masa ayanzun. Hakadai sukecin abincinsu, Rahma tanacine kawai badan dad'iba, amma jitake kamar tana cin magani. Safna da bobo kam suna lambu zaune, bobo ya d'aure fuska kamar bai ta6a dariyaba Dan ganin yanda Safna takafeshi da idanu tamkar zata cinyeshi. d'an tsaki yaja yana kauda kai daga kallinta, ke kinga inada abunyifa nazo nan nazauna, kuma matata banaso taduba bata ganniba Dan haka miye maganar taki?. Dukda maganarsa ta 6atama safna rai, musamman dayace bayaso matarsa taduba taga bata nan amma saita danne ta matso hawaye tana shashshekar kuka. Hannu ya d'aga mata, kinga ba kuka na tambayekiba fa malama. Share hawayenta tayi, ta durkusa agabansa guywa ak'asa tana cigaba da hawaye, Abdulmaleek pls kasamo mana mafita, nidai nasan kaima kana sona, idan zaka iya daurewa wlhy ni bazan iya jurewa ba ka taimaki rayuwata karta salwanta akan sonka. Wani murmushin mugunta bobo yayi, ya ce, "tabbas ina sonki amma so na 'yan uwantaka, irin Wanda nakema khursiyya da khairiyya. So na gsky irin na soyayya da tsan tsan k'auna da begen juna, mai ratsa jijiya da ruhi da 6argo mutum d'aya tak nakemashi, itace Rahma, my Nusfulhayat d'ina, farin cikina uwar 'yayana, sarauniya mai sarautar dukkan zuciyata da duk abinda ke cikinta. Safna kamar yanda na gaya miki wannan zaman shine zai zama zama na k'arshe tsakanina dake, kuma itace zata zama magana ta k'arshe tsakanina dake wadda ta danganci wannan, zan baki shawara kuma zan miki nasiha, idan kin d'auka kin huta, idan kin watsar ke wahala, nidai ALLAH yagani nafita hak'k'inki amatsayina na d'an uwanki musulmi. Zamansa yagyara yana mai k'ara tattara nutsuwarsa waje d'aya. Cikin murya mai nuna muhimmancin maganar dazaiyi ya ce, "Safna!. d'agowa tayi tana kallonsa amma bata tankaba. Ya ce, "Safna ina d'aga mini k'afane saboda darajar Rahma amma nakula ke bakisan zuruba. Zan baki shawara ta k'arshe atafiyamu Dan inaso mugudu tare my tsira tare.............. *_Luv you oll._* *_(((S)))......2017_* [11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 6⃣3⃣ Ina mai baki shawara amatsayina na mijin k'anwarki, ki nutsu kinemi miji kiyi aure kidaina wahalar da kanki akaina. Amatsayinki na wadda tayi kuskure abaya yakamata kiyi zaman gyarashi yanzu, sannan ki d'auki sona dakike ik'irarin kinayi ki jefar dashi gefe ki tsarkake zuciyarki, ki daina biyema k'awayen banza suna sakaki a hanyar hallaka na bin bokaye..... Cikin matuk'ar mamaki Safna take kallonsa, azuciyarta ta ce, "a ina yasan wannan?. Kamar yasan tunanin datake yayd'an murmushi tareda jinjina kai, yacigaba da fad'in kina mamakin ina nasani ko? Humm hakan babu inda zai kaiki wlhy saidai kiyita komawa baya arayuwarki, Safna babu abinda ke cutar da rayuwarki sai son zuciya, to son zuciya kuma facin zuciyane. Na tabbata ALLAH ya jarabceki da sonane saboda hakan yazamarma masu hali irinnaki ishara. Da'ace su Abba basuda Rahma dasunji kunya awaccan ranar dakika nuna musu basu isaba, saboda k'ok'arin kunyatasu dakikayi akan dalilinki mara tushe. Shin alokacin kinada tabbacin sake ganina?, kokuwa idan kin ganni kinada tabbacin zan kar6i soyayyarkine?, amma saboda son zuciya kika bijirema iyayenki akaina, wannan itace jarabawa tafarko dakika fara fad'uwa arayuwarki. Safna iyayenmu sunfi kowa sonmu Dan haka bazasu cutar damuba, idan baki saniba zan fad'a miki ayau, tunda nake banta6a za6ar matar aureba da kaina. Matata ta farko ma iyayenane suka za6amin, dukda banasonta amma nayima iyayena biyayya nakar6i k'yautarsu da hannu bibbiyu, biyayyar danamusu ban bijireba sainaci riba, daga ni'ima har Rahma sunzamemin alkairi arayuwata, wadda na tabbata da auren soyayya nayi bazanci riba hakaba, kema na tabbata dakinma iyayenki biyayya dakinyi gamon katar da abinda kikeso, amma kinga sakamakon da bijirewar taja miki yanzu, saidai sharri shaid'an dana zuciya sun danneki kin kasa ganewa bare kiyi nadama harki nemi afuwar iyayenki. To inamai tabbatar miki idan baki gyaraba haka zakiyita fad'uwa ak'asa, ki k'are rayuwarki a bibiyar tamu rayuwar, gashi mukuma kullum farincikine ke k'ara baibaye rayuwarmu saboda albarkar iyaye dake bibiyarmu. _amatsayinmu na 'Ya'ya wad'anda iyayenmu sukasha wahala wajen haihuwarmu, rainanmu, karatunmu, tarbiyyarmu, basa son kukanmu, kulada lafiyarmu daduk wani motsinmu, amma ayayin damuka girma muka mallaki hankalinkanmu lokacin daya kamata mu share hawayensu, amma sai suka nemi wata alfarma agaremu muka bijire musu, saboda mu muna ganin mun waye su mutanen Dane, mukuma 'ya'yan zamani wad'anda boko tagina, shin kuwa muna ganin ALLAH zai k'yalemu kuwa?, aganina babu abinda 'ya'ya zasuyi aduniya su biya iyayensu akan hidima da d'awauniyar dasukayi dasu suna k'anana._ Akwai inda zaka iya bijirema iyaye kaci riba, shine idan sunce kasa6ama ALLAH, wannankam ba'a yarda kamusu biyayyaba. Idanfa ta gsky da tsarin addini za'abi, iyaye akace suza6ama 'Ya'ya mijin farko, idan kuma k'addara ta gifta hartayi zawarci to wannan tanada 'yancin za6ama kanta akaro na biyu tunda ta mallaki hankalin kanta. Safna kije ki tsugguna ga iyayenki kinemi gafararsu na tabbata insha ALLAHU ko yayane saikinji sona yaragu azuciyarki. Inhar iyaye na fushi dakai tom dolene kaita tsintar kanka cikin asara, bafa zaka sami sassauciba harsai sun janye fushinsu akanka, tokema ki gwada ki gani insha ALLAHU zaki dace....... Shashshekar kukan Safna ne yakatsemasa dogon bayanin daya d'akko, d'ago k'yawawan idanunsa yayi yana kallonta, ya ce, "ba kuka zakiyiba inhar nasihata tashigeki, nadama zakiyi, kuma ki d'auki hanyar gyarawa. Cikin shashshekar kuka safna ta ce, " duk abinda kafad'a gsky ne, amma wlhy akowane dak'ika na rayuwata k'ara sonka nakeyi, narasa yanda zanyi nacireka araina, ina sonka so bana wasaba. Tabashi tausayi kwari da gsk, Dan haka cikin taushin murya ya ce, "kiyi hak'uri Safna, kimik'a lamarinki ga ALLAH shine zai taimakeki, na tabbata shaid'an nak'ara hura wutar sonane azuciyarki Dan kawai yaraba zumincin dake tsakaninki da 'Yar uwarki, Yakuma cigaba da 6atar dake acikin duhuwa kikasa rok'ar gafarar iyayenki bare harkici riba a rayuwarki. Zan tayaki da addu'a ALLAH yacire miki sona azuciyarki kema yabaki miji nagari maisonki fiye da komai amadadina, nabaki kwana uku kije kiyi tunani kuma kiduk'ufa da addu'a Nina zan tayaki. Jinjina kai Safna tayi cikin sanyin jiki, ga hawaye sha6e sha6e afuskarta, yazaro farin handky d'insa daga aljihu sai tashin k'amshi yake yabata. Hannu biyu tasaka takar6a tareda fad'in ngd ya Abdulmaleek, ALLAH yabiyaka da mafificiyar nasara, yasakama rayuwarka da mafificin alkairi. Jinjina mata kai yayi tareda lumshe idanunsa fuskarsa d'aukeda murmushi Wanda bata ta6a ganin irinsaba daga gareshi. Itama mayar masa da murmushin

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});