Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

reras. Agidama khairiyya da khursiyya da Nawal sallar sukayi, ammi ma haka. Bayan an idar ammi tasakasu suka shirya abinci a tsakkiyar falon Dan yau duk su ya Is'haq anan zasuci abinci, suka gama shirya komai da taimakon 'yan aiiki sannan suka koma d'aki domin gabatar da sallar isha'i da aka kira. Basu dawoba saida akayi sallar isha'i, suka rankayo zuwa gida suna 'Yar hirarsu da tsokanar juna. Afalon suka zube Appa ya ce, ''aini zuwannan naku yamin daidai, kamar kunsan dama ina nemanku. Ya Hamza ya ce, "to Appanmu ALLAH yajishemu alkairi. Amin suka fad'a gaba d'aya. Ammi dasu khairiyya suka fito suma, rissinawa sukayi suka gaida Appa da yayyensu, Nawal taje jikin Appa tazauna. Yashafa kanta yana fad'in amaryata kinyi sallah?. Kai ta jinjina tana dariya. Tomi kika rok'amana?. Hannunta tasa abaki idonta na kallon p,o,p d'in falon alamar tunani, can takalli Appa tana washe wawulinta da hak'ori biyu yafad'i, ta ce, " Appa kasan mina rok'a?. Saikin fad'amin amaryata. Narok'i ALLAH ya kaimu Aljanna nida kai, da Ammi, da baby, da uncle Sulaiman, da uncle Hamza, da Uncle Is'haq, da aunty khursiyya da aunty khairiyya, da mom din gida uncle Is'haq, da momyn ya Ahmad da aunty Sameera, kuma nace ALLAH yasa muje makakka muduka sau dubu dubu babu iyaka muga kabarin Manzon ALLAH a madina. Tafi sukai mata gaba d'aya suna fad'in ameen mai sunan manya. Ya Is'haq dake kusada ita har sumbatar hannunta yayi. Appa ya ce, ''lallai na more da amarya Ashe. Ta ce, "Appa kasan mikuma na rok'a daga k'arshe?, ya girgiza kai yana murmushi, canayi ALLAH yasa nima naga momyna. Gaba d'ayansu kallonta sukayi, tabasu tausayi sosai, Appa ya rungumeta cikeda tausayi, Bobo kam k'asa yayi da kansa zuciyarsa tayi rauni sosai, jiyake tamkar yafasa kuka saboda tausayin 'yarsa, tausayinta yana d'aya daga cikin abinda yasa yak'i k'ara aure, bayason ya auro wadda zata takurama d'iyarsa sanyin idaniyarsa. Ya Hamza ya ta6ashi d'agowa yayi yana kallonsa, ya Hamza ya jinjina masa kai fuskarsa d'auke da tausayi. Murmushi bobo yayi. Saikuma ya kalli sauran 'yan uwannasa da iyayensa yaga dukshi suke kallo. Kansa yamaida k'asa yana cigaba da murmushi mai ciwo. Ganin haka Ammi ta katsesu da fad'in bismillah kusauka ga abinci. Kowa ya sakko tskkiyar falon in da abincin yake. Bayan Ammi tasakama Appa kowa yafa k'ok'arin zubama Kansa abinda yakeso. Falon yayi tsit bakajin motsin komai sai k'arar filat da cokali, saikam surutun Nawal lokaci2. Bayan sun kammala cin abincin 'yan aiki suka gyara wajen tsaf, Appa yakalli khairiyya ya ce, "auta zoki kaita d'aki ta kwanta. To Appa khairiyya tafad'a tana mik'ewa, d'aukar Nawal tayi daga jikin Appa tanufi d'aki. Falon yay tsit kowa ya maida habkalinsa kan Appa. Appa yamusu sallama suka amsa. Ya gyara zama cikin hikimar zance yafara musu nasiha da k'ara jaddada musu muhimmancin zuminci da hak'uri da juna, ahankali ya gangaro kan auren Bobo, Wanda tunda Appa ya ambaci sunansa gabansa yafad'i. Appa yabasu labari kamar yanda yagayama su Ammi da ya Is'haq jiya. Ya d'ora da fad'in yanzu dai mun yanke hukunci ranar juma'a idan ALLAH ya kaimu za'a tura dakomai har sadaki Dan badogon lokaci za'a d'aukaba, k'arshen watannan za'ayi bikin kowa ya huta. Zuface tafara fita addukan sassan jikin Bobo, yakasa koda motsi dukda tsokanarsa da 'yan uwansa sukeyi suna fad'in ango kasha k'amshi. Ammi ma sai dariya takeyi danjin dad'i, sai Alhmdllh take dad'i, su khursiyya kam harda 'yar bud'a. Bobo ya galla masu harara. Gaba d'aya akayi dariya harda Appa. Daganan suka cigaba da tattauna yanda biki zai gudana da shagalin daza'ayi. Appa ya ce, " suyi duk abinda sukeso bazai hanasuba, Dan Andad'e ba ayi wani shagaliba agidan. Har k'arfe tara suna gidan, saida Appa yace yakamata sutafi gida hakanan wajen iyalinsu sanan suka mik'e kowa yanufi gidansa. Bobo bayan yarakasu harabar gidan yanufi d'akinsa jikin a sanyaye, yama rasa wane irin tunani zaiyi shikam............. _Tofa masu karatu, Yaya kenan?, shin ina Safna?, gafa gwaninta zai angwance, kowacece amaryar Bobo?, ya wannan zama zai kasance?, kudai biyoni kawai, basirar aunty bilyn Abdul ce, nikam copy nakemuku masoya._ *_hummm wasa farin girki, masoya yanzufa aka fara, kumuje zuwa wai mahaukaci yasai kura, yanzu muka dasa alk'alamin labarin Bobo!._* *_masoya muna godiya ALLAH yanar zuminci._* [11/12, 2:15 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻 ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _{Bobo}_ _Story & editin_ *_Aunty Bilyn Abdul_* ✍🏿 _Written_ *_Marak'isiyya_* _hak'in mallaka_ *_Aunty Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Bily giro_* 1⃣3⃣&1⃣4⃣ *_Gidansu Safna_* Safna na kwance akan gado tana chart, sai faman murmushi takeyi, da alama tana jin dad'in charting d'in. Rahma dake zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani ta waigo ta kalli safna dataketa 6a66aga dariya harda rik'e ciki, kai Rahma ta girgiza tareda fad'in ALLAH ya shirya azuciyarta. Kanta tamaida tacigaba da karatunta. Safna kam bamatasan tanayiba, dariyarta taketayi cikin farinciki, hira takeyi da Baseera akan nemomata Bobo, Baseera tana gayamata akwai wani guy a unguwarsu sunansa *boy shiyakama subama aikin, Dan tasan cikin sauk'i zai samomusu bobo da labarinsa. Tak'ara wani d'an ihun farinciki, tareda fad'in saini mata agidan Bobo. Rahma takuma kallonta cike da mamaki, ganin bazata barta tayi karatunta cikin Nutsuwaba yasa tarufe alkur'anin tayi addu'oin ta tamik'e ta ajiye alkur'ani ama'ajiyarsa. Hijjabinta tacire tana fad'in aunty Safna kofa sallar magriba bakiyiba har anyi isha'i amma kina kwance kina charting akan abinda k'ilama bazai amfaneki da komaiba. ALLAHU Akbar maikaratu nagaba, Safna tafa idonta akan waya, tacigaba da fad'in malama Rahma jawo wata ayar na haddace wannan. Ajiyar zuciya Rahma ta sauke, ta ce, "Niba malamarki bace, kuma ba wa'azi nake mikiba, ina tunatar dakene dannaga kin shagala. Wani wawan dundu safna tasaukema Rahma abaya, Dan ubanki idan aljanna takice ki hanani, shegiya 'Yar iska uwar tsari, kenikam daba agabana ummi ta haifekiba wlhy danace anmata canji a asibiti, anya kuwa acikin 'yan barka wata bata sace ainahin d'iyar da ummi ta haifaba ta ajiye mata ke?. Rahma tashare hawayenta ta ce, " kije kitanbayeta k'iladai kece aka canja mata, Dan halinki daban dana mutanen gidanna. Afusace Safna taduro daga gado tana d'urama Rahma zagi. Tuni Rahma tafice tabar mata d'akin. Afalo taci karo da abbansu yadawo masallaci, sannu da dawowa Abba. Yauwa d'iyar albarka ina zuwa haka?. Ba inda zani Abba, nadai fito falone nasha iska. Masha ALLAHU, ina 'Yar uwar taki to?. Tana d'aki Abba. Yauwa jeki kiramin ita zamuyi magana, ina umminku?. Ganinan Abba Shaheed ummi dake fitowa daga d'aki tafad'a. Tamai sannu dazuwa sannan tafara shirya musu abinci. Rahma tatsaya abakin k'ofa ta ce, "aunty Safna kizo Abba yana kiranki. Shegiya munafuka gulmata kina kaimasane?. Niba munafuka bace, yace dai kizo..., tana gama fad'a tafice. Safna tasakko daga gadon tana mita, zan koya miki hankaline 'Yar banza maikan dankali. (Araina nace kekuma maikan doya ko?.) Kusada Abba taje tazauna, Abba gani. Kanta yashafa yana murmushi haba safnan Abba miya faru kika k'unshe kanki a d'aki?. Zamanta ta gyara tana ballama Rahma harara, babu komai Abba nayi sallane INA zaune ina Azkar. Da k'yau 'Yar albarka. Rahma kam ido tazaro waje danjin k'aryar da safna ta gilla, saikuma ta k'unshe baki tana dariya. Safna na kallonta, Dan haka haushi yak'ara kamata. _(Hattara iyaye kuringa kula da addinin 'ya'yanku, akwai yara dayawa masu wasa da salla irinsu Safna, wata

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});