Chapter 46
Chapter 46
Nawal ne kawai keta kaikawo agidan, suka gama had'a break fast suka gyara gidan tsaf. *_10:6am_* Bobo yatashi, yagama komai na al'adar rayuwarsa sannan yafito falo cikin dogon wandon jins blue da farar t-shirt mai gajeren hannu, sai zabga uban k'amshi yakeyi. Rahma da Nawal suna zaune afalo tana ma Nawal kalba, da gudu Nawal taje ta rungumeshi tana fad'in my papa ina kwana. Lfy lau baby yafad'a yana rik'e hannunta sukazo suka zauna. Rahma ta gaisheshi ya amsa amma fuskarsa babu walwala. Azuciyarta ta ce, "boss yaukuma muskilancin ne yamotsa?, afili kuma ta ce, "ga break. Yad'an kalleta, atausashe ya ce, ''kawomin tea kawai. Mik'ewa tayi tahad'o masa tea mai k'auri takawo masa, ya amsa yana binta da kallo, ahankali ya ce, "ngd, itama d'an kallonsa tayi takauda ido. Yana shan shayi yana kallon film d'in dasuke kallo wani India film yakula Rahma tanason film d'in India komiyasa?. Safna tafito itama, Rahma ta kalleta aunty harkin tashi?. Saida tad'an ta6e baki sannan ta ce, " eh natashi. Takalli Bobo dayayi tamkar baima san da shigowartaba kuma yanajinsu. Ta ce, "ina kwana?. K'ara d'aure fuska yayi sannan ya ce, " lfy." Rahma bataji dad'in yanda ya amsama auntyn ta gaisuwaba amma yaza yayi. Takalli Safna dake zaune tana kallon bobo ta gefen ido, aunty gafa break. Uhum kawai safna tace mata. Haka akaita zaman kurame afalon, saidai Nawal daketa surutunta, shi bobo yanayine saboda Safna, itakuma Rahma tanajin haushin yanda yake share 'Yar uwarta, itakuma safna suduka haushi suke bata. Shima yalura da Rahman amma sai itama ya shareta. Bayan takammala abincin Rana tajere a dinning tak'ara gyara gidan tsaf, dama Safna bata tayata, saidai idansu khursiyya sunzo, to sukuma yanzu sunk'ara zama busy Dan bikinsu baifi saura 12days ba. Rahma tanufi d'aki zatayi wanka, Dan Nawal nawajen dadynta. Yaukam ALLAH yabama safna sa'ar zuba magungunanta acikin abincin bobo, bayan tagama takoma falo ta Fiske abinta. Mintuna kad'an Rahma tafito cikin doguwar rigar material ja, kayan yayi mata k'yau sai zabga k'amshi takeyi. Ta kalli safna dake zaune afalo, aunty bara nakirasu muci abinci ko?, tawuce batareda jiran amsar Safna ba. Baki safna ta ta6e tareda raka bayan Rahma da harara. Yana kwance rigingine Nawal tana gefensa tana barci, idanunsa na kallon p,o,p d'in d'akin da alama yana duniyar tunanine. Rahma tashiga d'akin da sallama, shi baima jitaba sai k'arar rufe k'ofar yaji, yad'ago kai yana kallonta, tamasa k'yau kwarai da gsk, idanunta suna k'ara narkar dashi akanta...... Takatse masa tunani dafad'in dadyn Nawal gafa abinci yana jiranka. Bai tankaba amma yatsura mata ido tamkar zai cinyeta. Tasake maimaita masa sannan yay ajiyar zuciya, dama inason ganinki yafad'a yana yunk'urin tashi, saida yazauna sosai sannan yanuna mata bakin gadon alamar ta zauna. Tad'an zauna nesa dashi kamar mai tsoron wani Abu. *_RAHAMA!!._* taji sunanta har cikin kwakwalwarta, Dan ya iya fad'ar sunan. Yakuma fad'in _Rahama!._ Itama akasalance ta ce, "na'am. Yagyara zamansa sosai yana fuskantarta, tsareta yayi da mayun idanun nan nasa ya ce, "inaso daga yau kidawo kwana d'akin nan. Cikin sauri tad'ago takalleshi, hanjin cikinta ma saida suka yamutsa danjin furucinsa. Fuskarsa babu alamar wasa Dan haka tamaida kanta k'asa, muryarta na rawa ta ce, "saboda mi zandawo kwana d'akin nan?. Ya ce, " saboda ni *mijinki* ne, umarni nake baki ba shawara ba, kuma daga yau nakeson ki fara. Bata iya cewa komaiba Dan yau yakoma mata ainahin *_Abdulmaleek_* data fara gani ranar aurensu. Shima baisake cewa komai yamik'e yashiga bathroom. Tana nan zaune tamkar gunki harya fito daga bayin yacanja kayansa zuwa shadda milk colour d'inkin boda yayi k'yau masha ALLAH. yad'auki Braun d'in takalmi yasaka agogoma haka, yafesa turarurrukansa tareda kwasar wayoyinsa da key d'in mota, saina dawo yay maganar yana k'ok'arin fita, itakuma tabisa da kallo tamkar sokuwa, ganin zai fice daga d'akin ta ce, "abincinfa?. Tsayawa yayi amma bai juyoba ya ce, nak'oshi yay gaba abinsa. Safna tana zaune afalo yafito, tamik'e da sauri tasha gabansa.............. Kuyi hak'uri dajina shiru, munyi sunan babyne, sunanta *_ummu habeeba_* (Iman). *_luv you oll_* *_(((S))).....2017_* [11/12, 2:57 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ»typing........ β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£ _β’{π ±π Ύπ ±π Ύ}β’_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* *_Happy independence day, God bless you and God bless Nigeria. π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬ We love Nigeria._* 5β£4β£ Wani kallon sama da k'asa yamata ya ce, "bani hanya. Ta ta6e bakinta tareda fad'in aidama zan baka, amma inaso na tunatar dakai maganar jiya. Ya watsa mata harara amma baice komaiba. Murmushin ko a jikina safna tayi, ta ce, "Nasan bakason Rahma, Dan dakana sonta bazaka fice batareda kaci abincin taba. Tsaki yayi cikin nuna razanarwa da kaushi ya ce, "dallah bani hanya kokuma wlhy yanzunnan namiki abinda har jikokin jikokinki saisun samu labari, banza jahila kawai. Ganin gaba d'aya kamaninsa Sun canja tamkar zai daketa yasa tabashi hanya tana murgud'a baki da yin k'unk'uni. Ficewa yayi yana Jan tsak'i, adaidai lokacin Rahma tafito, amma bataga abinda yafaruba. Itakam Safna bak'incikine yarufeta da fargaba, kardai ace mutumin nan yak'icin abincin nan, lalai daya cuceta. Rahma takatse mata tunani, auty Safna lfy kuwa?. Safna taja numfashi tana wani kicin kicin da fuska, lfy lau mikika gani?. Rahma ta ce, "a'a nagadai kamar bak'ya cikin nutsuwarkine?. Cikin masifa safna ta ce, " to k'alau nake, tatashi tabar wajen. Rahma tagirgiza kai, Dan indai dasabo tasaba da halin yayar tata. %%%%%%%%%%%% Sai dare bobo yadawo gidan, Nawal taje dagudunta ta tarosa. Rahma da Safna suka masa sannu suma, ya amsa fuska ad'aure, d'akinsa yawuce itama Nawal tabisa. Itama Rahma tamik'e tad'auki ruwa tabi bayansu, Safna taja tsaki tareda mik'ewa tashige d'akin Rahma. Rahma ta shiga d'akin da sallama, saidai bayanan yashiga wanka, Nawal ce kawai take zaune tana wasa da wayarsa, ta ajiye ruwan ta ce, "Nawal zomuje ki kwanta. Nawal ta nok'e k'afad'a tareda kwa6e fuska, ta ce, " um um momy ni ad'akin papa zan kwanta, Rahma tayi tayi amma Nawal tak'i Dan haka ta k'yaleta takoma d'akinta. Bata dawo d'akinsaba sai 10:34pm, yana zaune yana danne dannen laptop tashigo, Nawal kam tayi barci. Takai minti 3 da shigowa sannan yad'aga kai yakalleta sau d'aya yamaida kansa ga laptop, ki d'auki Nawal kikaita d'akin ki mana, yay maganar cikin nutsatstsiyar murya. Rahma ta shagwa6e murya ta ce, "Dan ALLAH kabarta anan mana. Yanda tayi maganar yasa dole yad'ago yana kallonta, tawani narke fuska, saiyaji wani Abu ya mintsini zuviyarsa, yad'an lumshe idanunsa harda yin wanid'an murmushin gefen kumatu, Wanda itakanta Rahma bataga yayibama, ya ce, "yaza'ayi ta kwana anan? aitayi girma da kwana tare da mu, in dama babu kowa a d'akin saikice anbarta ita kad'ai, amma tunda dakowa acan zata kwanta, yamaida kansa yacigaba da aikinsa abinsa. Haka tad'auketa badan tasoba tanufi d'akinta da ita, Safna tana zaune tana danna waya Rahma tashigo tacanjama Nawal kaya sannan tagyara mata kwanciya. Ta kalli safna, aunty Safna saida safe. Safna takalleta cikeda mamaki, cikin yatsine fuska ta ce, " ina zakije? Kike fad'in saida safe?. Cikin d'anjin nauyinta Rahma ta ce, "d'akin dadyn Nawal". d'akin dadyn Nawal kuma?, tofa sabon salo kenan wai gemu akafad'a, yaukuma?. Rahma dai batace komaiba tafice abinta. Har yanzu yana gaban laptop, tashigo tazauna akujerar d'akin. Yad'an kalleta bayan yakalli agogo, sannan yamaida kansa kan aikinsa. Bayan kamar minti biyu ya ce, bakijin barcine?
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83