Chapter 42
Chapter 42
ke karya azuciyarsa. Duksun dawo daga sallar isha'i, suna zaune afalo gidan Appa zugum², harda Abban Rahma da Umminsu, momyn ya Kamal da dad d'insu Ameera ihsan ya Muneer ya shaheed duk suna gidan Appa, Safna CE kawai babu, dantana makaranta abin yafaru, bayan tadawo mai gadi yashaida mata komai, yad'ora da fad'in 'yangidanma duk suna gidan surukan Rahma d'in. Safna ta ta6e Baki ta ce, " kaga baba bud'emin gate nashiga nahuta tukunna, Dan bazan iya zaman jigum jigum ba wlhy tunda ba mutuwa akace sunyiba. Maganar tata tarazana baba mai gadi, bayan yabud'e mata gate yabi mortar da kallo yana jin kina kai, aransa ya ce, "lallai yau nakuma shaidawa yarinyarnan batada mutumci ko kad'an, inbanda rashin mutumci d'an uwanka uwa d'aya uba d'aya ya6ata kanuna rashin damuwarka, kai ALLAH dai ya k'yauta to. Safna dai bamatasan yanayiba Dan tuni tashige cikin gida abinta, sai wata fara'a takeyi wadda nadad'e ban ganiba daga gareta. 🤔araina Na ce, " safna Kodai kidai??. *_3days_* Tsawon kwana uku kenan da 6atansu Rahma, Abu tamkar wasa, zuwa yanzu kam aii kowa yajigata, Appa yabaza rok'on ALLAH amasallatai, hakama gidan redio Dana TV, social media ma haka, amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, kuma tun ranar ba'a sake samun number Rahma ba. ALLAH sarki bobo acikin kwana ukunnan Yayi wata uwar Rama, ko abinci bayasonci sai ammi ta tsareshi tamkar yaro tabashi abaki, shima lauma hud'u zuwa Biyar zaice yak'oshi, saitata lalashinsa sannan zaiyarda yak'ara kad'an. Nikaina yabani tausayi k'warai da gsk😥. Yanzuma suna zaune afalo Ammi tana lalla6ashin sa akan yasha shayi amma sai yatsine baki yakeyi, ya mararairaice murya tamkar zaiyi kuka, ALLAH Ammi nak'oshi. A'a mukarram kadaure kasha koda kad'anne, kaga rabonka da abinci tun jiya da yammafa, komai na rayuwa hak'uri yakeso, Addu'a suke buk'ata daga garemu kaji, ALLAH ya ku6tar mana dasu idan suna Raye. Hawaye suka ziraro bisa kumatunsa, Ammi ta share masa.. Yana shirin yin magana sukaji sallmar ammar, suka amsa, yashigo ya zauna. Ammi yarissina yagaida sannan yabama bobo hannu suka gaisa🤝, cikeda tausayi Ammar yake kallon bobo. Ka kwantar da hankalinka Abdulmaleek insha ALLAHU za'a gansu, yanzu inaso naji time d'in Daka kira Rahma kafin tatafi d'aukar Nawal?. Wayoyinsa yakwaso dukya yamik'ama Ammar Dan yanzun bayason yawanyin magana sosai. Bincike sosai Ammar yakeyi a wayoyin Bobo yanayi yana waya da office d'insu, bayan sun kammala yabama bobo wayoyinsa, ya ce, "kabar wayiyinka akunne daga yanzun Duk Wanda yakiraka zamu gani, zakuma mu iyabi ta wannan hanyar dangano ko waye. Jinjina kai kawai bobo yayi batareda yayi maganaba. Ammi ta ce, " Ammar karinga yima abokinka fad'a yaringa cin abinci jibifa yanda yaketa ramewa. Ammar ya ce, "kik'ara hak'uri Ammi insha ALLAHU zai ringaci yanzu yana cikin rud'anine. To ALLAH yasa Ammi tafad'a tana mik'ewa tabasu waje. Haka Ammar yatsare bobo yad'ansha shayin da soyayyen dankalin sannan yaymasa sallama yatafi. Tafiyar Amma babu dad'ewa saigasu ya Hamza sudukansu. Guri suka samu suka zauna suna k'ara kwantarma da bobo hankali, yana kwance saman doguwar kujera yana jinsu, badai ya iya cemusu komai amma sunsan yana saurarensu, wayar bobo tafara wringing yayi burus da ita tamkar baijiba harta tsinke aka sake kira, ya ishaq ya ce, "kad'auka mana, 6ata fuska yayi tamkar zaiyi kuka amma baice komaiba, ganin wayar tana niyyar tsinkewa ya sulaiman yay saurin d'auka ya ce, " hello. Muryar data daki kunnensa CE tasakashi mik'ewa zumbur yana fad'in Rahma Rahma....... Kuna ina ne?.....miya faru daku?........ Aiikafin yafarga bobo ya warce wayar, muryarsa har rawa take ya ce, "Rahma Ku........ Bai k'arasaba wata muryar takatseshi da fad'in ba ita bace ta cancanta tabaku amsar tambayoyinku mine nan. Ku suwaye!!!?, Bobo yay maganar Afusace. Daga canma aka Daka masa tsawa, kai malam karka d'aga mana murya. Bobo ya ce, " kaga bawannan bane damuwata, miyasa kuka kamamin matana da d'iyata?, misuka muku?, waye yasakaku?, mukuke buk'ata?, idan kud'ine kufad'i konawane za'a Baku, pls karku cutar dasu. A'a a'a muba kud'i muke buk'ataba domin anrigaya an biyamu, kai kanka muke buk'ata, inkuwa bakazoba tom ran 'yarka da matarka zaizama fansar ranka amaimakonka. Bobo yarintse idonsa tareda cije le6ensa, saboda 6acin rai yagaza cewa komai. Daga can akace haba zaki kardai ace ka tsorata?, hhhhhhhh, bai kamata kaji tsoroba, munbaka daganan zuwa jibi idan bakazoba tom zaka tsinci gawar matarka da 'yarka, idan kuma kana buk'atarsu darai tom fine sai ka fanshi ransu. Saidai zuwan naka yanada sharad'i, wlhy koda wasa kada kayi gangancin zuwa da police zamu gane, na biyu saika taho zamu ringa fad'a maka hanya,, na uku idan ka 6ata mana lokaci zamu kacaccala matarka da 'yarka mu watsar, gashi kasakejin muryarta. Kafin bobo ya ce, "wani Abu saiyaji muryar Rahma cikin kuka tana fad'in dadyn Nawal karkazo pls, Dan ALLAH karka bada ranka akanmu, insha ALLAHU zanfanshi rayuwarku dagakai har Nawal, Nawal tana buk'atar mahaifi tunda tarasa uwa pls karka salwantar mata da ranka, Dan girman ALLAH karkazo, I luv you so much my Abdulmaleek. I luv you too my cute Rahma na, bobo yafad'a da saurin Baki,....kafin yakuma cewa wani Abu suka kwace wayar, cikin k'araji sukace kai wawa harka samu damar yimana soyayyane??. Wlhy kacika mana baki sai munmata fad'e hhhhhhhhhh dama gata daga gani zata bada feeling. Kaiiiiii!!!!!!!!!! Wawa, Bobo yadaka masa tsawa, wlhy kabari zuciyarka takuma kissima maka wani Abu akan matata saina tarwatsa kanka da bullet, na rantse maka da ALLAHn daya halicceni saina shayar dakai gidauniyar azaba, tabbas ni *_Zakine_* kujira zuwan zaki gareku, saina lak'umeku!!!!!!!!!, yanda yayi maganar cikin tsawa harsu ya ishaq da Ammi Appa su khursiyya duksun tsorata da yanayinsa, gabad'aya jikinsa yayi jajur abinka da fari, gashi jikinsa dukya mimmk'e, hakama jijiyoyinsa duksunyi rud'u², yay jifa da wayar, da sauri ya Hamza ya cafeta. Kowa yasan kuma ransa ya6aci kenan, k'arasawa yayi gaban Appa da Ammi yana yawaye ya ce, "iyayena kusamin Albarka zanje nataho dasu yanzun nan da kaina. Yanda yake magana dukya basu tsoro da tausayi, Ammi ta ce, " mukarram kayi hak'uri Ammar yazo kutafi tare, kai yagirgiza mata ya ce, "Ammi kedai sakamin Albarka kawai, basu musaba suka dafa kansa tareda saka masa Albarka da k'yak'yk'awar addu'a. Ya mik'e afusace zai fice, ya sulaiman yay saurin shan gabansa, wata irin hankad'awa bobo yayma ya sulaiman yay taga taga zai fad'i ALLAH yasoshi ya ishaq nakusa yarik'eshi yafad'o jikinsa. Bobo kam kota kansu baibiba yayo waje, yana fitowa ammar yashigo gidan, da sauri yatsayar da bobo, badan yasoba yatsaya yana kallon ammar dayaci wanka cikin shadda harda babbar Riga, wani d'an guntun tsaki bobo yayi danshi Ammar d'in yabashi haushin kwalliyar dayayi. Ammar baice masa komaiba yamik'o masa babbar Riga ta shadda. Galala bobo yatsaya kallon Ammar, wannanfa? yafad'a yana huro hanci. Kaga kasaka mutafi, Dan mungano Inda suke tasanadin wayar dakukayi yanzu, kasandai babu yanda za'ayi muje kai tsaye dole saimun canja kama gudun karsu San da zuwanmu su cutar dasu. Bobo yanajin haka yakar6i babbar rigar shaddar yasaka shima harda hula, duk abinda ke faruwa su Appa Ammi ya sulaiman ya ishaq ya Hamza khursiyya khairiyya duksun futo sunajinsu. Appa ya ce, " ALLAH yayi muku Albarka yayi taimako. Amin suka amsa. Bobo da Ammar dawasu police uku suka shiga mota d'aya, su ya ishaq ma mota d'aya,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83