Chapter 81
Chapter 81
k'ofa, Abbana miya farune?, Yayi maganar yana d'aukar Shureim dake sanye da kayan islamiyya. Papa ya Shareeff ne idokeni a zuciya. Kaikai azuciyafa Abbana?. Eh, shureim yafad'a yana d'aga kai. Fita bobo yayi dashi, Rahma dai dariya take musu, ta kwanta tana fad'in ALLAH yashiryaka Shureim a INA ake ganin zuciya dahar za'a doketa?. A can kuma bobo ya iske Shareeff ad'akinsu yana had'a littatafansa na islamiyya acikin jakka. yana ganin papansu ya yarissina yagaidashi cikeda girmamawa, Shareefa ma dake gyaran gadon su Shareeff d'in tazo tagaida papansu, suduka sanye suke da Uniform d'in islamiyya lemon green. Bobo yazauna akujerar d'akin yana fad'in ina Farhan da Anty?. Papa suna d'akinmu, wai Farhan ne baiga hularsaba. To ina aka ajiye?. Papa shiyya ajiye da kansa, waikuma ya manta. ALLAH yasa aganta to. Yaya Shareeff mi auta yamaka ka dukesa azuciya. Dariya Shareefa takeyi, Shareeff kam murmushi yayi, araina na ce, "masha ALLAH yaronnan bashida maraba da bobo tako ina. Papa littafina na Fiqhu ya yaga min, shiyyasa na rankwashi kansa, Dan yakiyaye a gaba, amma ni bandaki zuciyarsaba. Shureim Ashe kaji laifi kayima Yaya shiyya ya hukuntaka. Nawal da Farhan suka shigo da sallama, suma gaida dadynsu sukayi, ya amsa yana tambayar anga hular?. Eh papa anganta, Ashe cikin kayan Shareefa yasaka. Mik'ewa bobo yayi ya ce, " to kuyi sauri Ku k'arasa lokaci na k'ure muku. Afalo ya iske Rahma tafito, a'a momy bakiyi barcinba?. Hummm inani ina barci?, aii inaga saidai idan basawan gidan sun tafi islamiyya kuma. Zama Kusada ita yayi yana dariya. Mintuna kad'an duk yaran suka fito. Duk suka gaida Rahma, murmushi tamusu tana amsawa, tareda tambayarsu sun tashi lfy?. Kowa ya ce, ''lfy lau momy. Baby anhad'a wanki waje guda ko?, basai ashiru yazo Yata jiraba. Lah momy harma yafara wankewa, yaga akwai wuta shine yace bara yayi kafin su d'auke. Amma yayi dabara, anhad'a da kayan nan na Farhan daya had'a musu daud'a agidan Abba ko?. Eh duk nahad'a dasu. To adawo lfy. Suduka kowa yazo yasumbaci kumatun iyayensu, suma suka sus sumbacesu sanan aka fita ana fad'in sai andawo. Ajiyar zuciya Rahma tayi ta ce, "kai gidan haryayi dad'i. Dariya bobo yayi ya ce, "aizasu dawone. Amma kafin sudawo nahuta. Ya ce, " idan nabarkiba, yayi maganarne yana d'aga mata gira. Murmushi tayi ta ce, "Zumana kafa girma. Hhhh girma kuma?. Eh mana, kallifa yaranka biyar, koyanzu aka aurar da Nawal zama zatayi ga Shareefa ma tana neman kamota atsawo, yarinyarnan ni bammasan inda takwaso jikinnanba?, sainagama kamar tafi Shareeff k'iba. Zamewa bobo yayi yakwanta yad'ora kansa saman cinyarta, jikin ya Hamza takwaso aii kobaki kulaba?. Kumafa hakane wlhy Nurulk'albi, da jikin jiddahn ya Sulaiman da jikin Shareefa, amma duk tsayonka suka kwaso, jiba Nawal da Zainab d'in ya ishaq harfa rankwafawa yarannan sukayi. Wlhy hakane my cute, jiya danaje gidan ya ishaq naga Zainab cewa nayi kawai suna kammala Secondary amusu aure itada Nawal, ni idan tanima za'abi harda Sumayya yaran duk sun zangame fa. To aii girman ne babu wahala, mustapha da Sageer gasunan subasuyi tsawoba bakuma su gajarceba har Shareeff naneman finsu tsawo, amma Ahmad da Kamal d'in ya hamzama duk kune, ALLAH dai yaraya manasu baki d'aya. Ameen my cute, ALLAH ya saukeku lfy kuma, yafad'a yana shafa cikinta. Murmushi tayi ta ce, " Ameen my zumana, kasan kuwa jiya muna waya da khairiyya takecewa tanason fita takasa saboda laulayi nace mata ainida ita babu maraba, da k'yar na iya zuwa sunan Basma, shine take dariya wai Anty Safna da khursiyya sunfimu dauriya, ranar bikin taufiq da heeba sai aiki sukeyi tamkar bamasu tsohon cikiba. Dariya yayi ya ce, "dafa gsky khairiyya wlhy, wanan cikin duk yamaidake raguwa, amma cikin Shureim wasuma saida yafito sukasan kinada cikin aii. Tab kaidai danba ajikinka yakebane, amma cikin Shureim ma nasha zaz6in rana, wata sa'infa kamar jira kana fita aiki su Nawal suka tafi makaranta sai zazza6i yarufeni, ga son jikin tsiya har k'agara nake kadawo najini kwance ajikinka. Hhhhh mage kenan. Wlhy asanan namafi mage, cikin Farhan nedai kam bansha wahalaba sosai da cikin daya zube bayan haihuwar su Shareeff, shi saidama nayi 6arin nasan inadashi kamanta. Inafa zan manta my cute, kai ranar narud'e dayawa, dayanzu yaranmu shida ga na 7. Dariya Rahma tayi ta ce, haka ALLAH ya tsara, wad'annanma daya bamu mungode masa, wasunacan suna nema basu samuba. Hakane kuma my cute d'ina, ALLAH dai yaymiki albarka kinji. Ameen Zumana tafad'a tana sumbatar kumatunsa. Lumshe idanu yayi yana murmushi, ahankali yabud'e akanta, my cute tashi mutafi d'aki. d'aki kuma Nurulk'albi?, mizami yo?. Lada zamu samo mana, yad'aga mata gira, dariya sukayi gaba d'aya... _____________________ Duk suna zaune afalo, Shareeff da Shareefa na game dasuka had'a da TV, Rahma tana gyarama Farhan kumba Dan gobe idan ALLAH yakaimu Monday, Nawal kam tana note, Shureim najikin bobo yana barci bayan angama masa gyaran k'umba. Jisukayi ana kwankwasa k'ofa, suduka suka kalli k'ofa, bobo ya ce, "Shareeff tashi kaga waye. To papa, Shareeff yamik'e tareda ajiye handle d'insa yanufi k'ofar yabud'e. Kallon mutumin yake d'an kimanin shekara 40+, yarissina ya gaidashi. Mutumin ya amsa cikeda murmushi yana k'arema Shareeff kallo, tabbas da ace d'an Adam yana komawa baya zuwa k'uruciya dayace bobone agabansa. Ganin kallon da mutumin yake masa yasashi fad'in uncle kana Neman waye?. Murmushi yayi ya ce, " yaro ina Neman mahaifinkane, Dan daga ganinka kai jinin *_Abdulmaleek bobo_* ne, babu inda ka banbanta dashi, yaro miye sunanka?. Sunana Shareeff. Masha ALLAHU d'ana Shareeff, kacema mahaifinka Haneeff Sunusi dala ne yake sallama dashi. Jinjina kai Shareeff yayi yajuya domin isar da sak'o ga papansa. Shareeff yanaga ka dad'e?, wayene?. Papa ya ce, "sunansa Haneeff Sunusi dal....... Aii kafin Shareeff yak'arasa Rahma da bobo duksun zaro ido waje, bobo yace cemasa yashigo. Yakalli su Nawal yace kusaka hijjabanku, ak'idarsace wanan indai wani bak'o namiji zai shigo koda Ammar ne, ko 'ya'yan su ya ishaq to dolene su Shareefa su saka hijjabai, dama tuni Rahma tasaka nata.. Da sallama Haneeff yashigo, bobo ya amsa cikeda fara'a da mamakin canjawar haneeff, yazama babban mutum harda gemu,haneeff ya zauna cikeda fara'a yanabin yaran da kallo, masha ALLAH Abdulmaleek ka Tara zuri'a kam. Dariya bobo yayi yabashi hannu suka gaisa, Rahma ma ta gaidashi, su Nawal kowa ya gaidashi, sannan suka tashi suka koma d'akinsu. Dandanan Shareefa da Nawal suka cika masa gaba da kayan motsa baki. Bobo ya ce, " haneeff dama zaka iya tunawa dani?. Dariya Haneeff yayi ya ce, "Abdulmaleek kai basoyine dabaza'a manta dakaiba, kakafa tarihin dabazai gogu a duniyaba, tundaga lokacin Dana tsinci kaina gidan yari lokacin da abubuwa suka fara nisa, addini da ake koya mana ya hudani saina tabbata kai masoyine na hak'ik'a domun kataimaki rayuwata, k'ila dabaka saka ankamaniba har naje wannan gida da yanzu rayuwatama ta lalace, bazan mori komaiba, amma yanzu kalleni nazama babban malami acikin gidan, jiya jiya nafito amma nace tabbas sainazo na ganka, naje office d'inka sai akacemin aii tuni katashi, sunmin kwatancen office d'inka na yanzu, dakuma super market d'inka, to naje super market d'innne aka bani address d'in wannan sabon gidan naka, shine nazo. ALLAH sarki haneeff kar ka damu kanka aii komai yawuce, ya bayan rabuwa?. Sai godiyar ALLAH kam, ya iyalinka?. Dariya bobo yayi ya ce, "
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83