Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nasihohi taro yatashi lfy, daga nan akayi hotuna kowa yakama gabansa. Kowa yana zuwa gida yafara shiri a gaggauce Dan ana sakkowa daga masallaci za'a d'aura auren. Kowa yafito anata shiga mota Dan tafiya sallar juma'a da d'aurin aure. Masha ALLAH nafad'a yayinda na hango muku ango Bobo yaci kwalliya cikin Sky blue d'in shadda harda babbar riga, wayyo masu karatu bayyana muku k'yan dayayi 6ata lokacine, ammafa ya had'u. Masallaci suka nufa. Bayan sakkowa suka wuce anguwar su Rahma. _Alhmdllh anguwar tacika mak'il da jama'a, wasuma akan mota suke zaune, gurin yacika har babu gurin faking, dukda nisan da su Rahma suke dashi da titi, wasu sai abakin titi sukayi faking motarsu._ K'arfe 3:30pm d'umbin al'ummar Annabi suka shaida d'aurin auren *_"Abdulmalik Aliyu Abdulmalik hamshak'i, da amaryarsa Rahma Bilal Basheer mai Gold. "_* (To ango da amarya saimuce ALLAH yabada zaman lfy da fahimtar juna ameen). Dak'ar na iya samo muku Rahma amarya ad'akinsu itada gayyar k'awayenta Wanda yawanci duk yaran family nasune, wasu kuma 'yan islamiyyarsu da boko. Tahad'u cikin less ja mai adon farin siton masha ALLAHU, amarya tafito ras saidai mak'iyi. anacewa and'aura auren tafara kuka, su Ihsan suna lallashinta. (To Rahma sai hak'uri aii). *_Safna_* Safna ana gidan su ya kamal, ita adole tayi gudun hijira, ko wanka batayiba bare kwalliya, tana kwance ad'akin Ameera tana chart abinta hankali kwance, fira suke da k'awayenta a group suna tsokanarta wai tamusu bak'inciki, dayanzu sunata shan shagalin biki. Dariya tayi ta ce, " karku damu aii kwanannan zakusha bikin nida bobona. Toma ALLAH ya kaimu... Kafin tabada amsa Zainab autarsu Ameera tashigo tana fad'in an d'aura aunren. Wata gagarumar fad'uwar gaba tariski safna dake kwance, tadafe k'irji tana fad'in ya salam, saikuma ta sauke ajiyar zuciya takoma takwanta, haka kawai taji jikinta yayi sanyi, zuciyarta tayi k'unci. Zuwa wani lokaci kuma saitaja tsaki, tomima zai dameni tunda ALLAH ya tsallakar dani daga wannan auren k'addarar. Rahma ALLAH ya yanka miki kazar wala sai aje aita figa. Sainazo gayyatarki aurena da Bobo na..... Na ce, "hummmmm. *_" kuyi mana afuwa jiya bamuyi posting ba, mai copy d'ince take mura, nikuma nayi busy, amma gashinan yau nadage nayi muku kafin ta warke tacigaba."_* Luv u oll. _bilyn Abdul ce⛹🏻‍♀._ *luv u oll my fan's_* *_(((S))).......2017._* [11/12, 2:20 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻 ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _{Bobo}_ _Story & editin_ *_Aunty Bilyn Abdul_* ✍🏿 _Written_ *_Marak'isiyya_* _hak'in mallaka_ *_Aunty Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Bily giro_* 2⃣3⃣&2⃣4⃣ Biki yacigaba da gudana cikin farin ciki da Annashuwa, gidajen biyu anata hada hada. Bayan kammala d'aurin aure anguna suka shigo cikin gida akayi gaishe gaishe da hotuna, itadai Rahma koda wasa bata yarda sun had'a ido da Bobo ba har aka gama hotuna suka tafi. Shikam jinsa yake wani iri kuma cikin nishad'i, komai na Rahma yana burgeshi, musamman yanda take komanta cikin sanyi. Haka suka k'arasa gidasu, nanma cike yake da mata, tunda suka shigo akai caa kan bobo, sai tsokanarsa su aunty Rasheeda sukeyi, baya cewa komai saidai murmushi. +.+.+.+.+.+.+.+.+.+.+ *_5:30mp_* aka gama shirya amarya domin mik'ata gidan angonta, tana falon Abba inda dangi suka zagayeta anata nasiha gareta, sai rabzar kuka take tamkar zata shid'e, ummi ma kuka takeyi Dan takasa cewa komai yayinda aka kaimata Rahma gabanta dan taimata nasiha, babu abinda take fad'i sai ALLAH yay miki albarka Rahma, yanda kikai mana biyayya kema ALLAH yabaki 'ya'ya masu yimiki, kuka yaci karfin ummi takasa cigaba. Haka aka hak'ura aka fito da Rahma, Abba dakansa yasakata mota tanata kuka, ya Hamza dazai tuk'a amarya jiyayi tabashi tausayi, shima kamar yay kuka yakeji. Kuka sosai Rahma takeyi abin tausayi, momyn su Ihsan da Maman Basma suka shiga motar suma, tsakkiya suka saka Rahma daketa kuka har numfashinta na d'aukewa. Yayinda Abba yaga motocin amarya sun Lula, yatabbatar da gsk yau Rahma ta barsu, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, yasa gefen rigarsa ya share tareda juyawa gida. Canma tararwa yayi ummi NATA kuka, yashiga lallashinta damata nasiha. Gayyar amarya ta isa gidansu Bobo, Dan nan za'a ajiye amarya sai gobe idan ALLAH yakaimu amaida ita gidanta. Har cikin harabar gidan aka shiga da motar amarya. Suna fitowa saiga Ammi da gayyar k'awayenta, wasu sosuke kawai suga mace mai sa'a data samu bobo amatsayin miji, Dan sunsha bashi 'yayansu amma ya ce, a'a, (basu San itama had'asu akayiba ba soyayya bace). Sanye Rahma take cikin shadda ruwan madara zani da Riga, ta lullu6a da k'aton mayafi ruwan k'asa mai turuwa, hakama takalmin k'afarta, kanta arufe yake shiyyasa masu tsogumi basu ganiba, Ammi tarungume Rahma tana lallashi, kama hannunta tayi takai har cikin d'akinta na sama, lallashinta tad'anyi na minti biyu saida taga tad'an tsagaita da kukan sannan tafito aka tura k'awayenta. Gida ya harmutse Dan cike yake dank'am da jama'a, gashi yau Ammi takeyin yinin biki dama. Sai bayan magriba dangin amarya suka juya domin zuwa suyi shirin tafiya wajen dinner daza ayi k'arfe 8:30pm to 12:00. Gidan yad'an rage hayaniya kad'an tunda mutanen sund'an ragu babu laifi. Duk wannan hidimar da akeyi bobo yana can cikin lambun gidansu da aka k'awata da haske, shikad'aine zaune akan kujera mai lilo idonsa alumshe yana duniyar tunanin rayuwarsa shida marigayiyya Ni'ima. Yatuna itama haka akaiyi aurensu baya sonta, Dan ko taro d'aya bai halartaba alokacin na shagalin bikinsu, shiyyasa yake mamakin wannan karon komai Appa yace yayi baya musu saiyaje yayi. (Wata zuciyarsa ta CE sannan ai kana kan hayak'in samartaka ne). Hakane kuma yafad'a afili. Bud'ar data cika gidance da k'aruwar hayaniya ta tabbatar MASA da amaryarsa ta iso, yamatse idonsa dake arufe tareda fad'in ALLAH yajik'anki Ni'ima ta, kifahimceni ba laifina baneba, nima sakani akayi dole badan inason aurenba." Jiyay tamkar maganar Ni'ima acikin kunnanensa tana fad'i masa, _"karka damu mijina Nima zanyi farincikin kasancewar Rahma amatsayin matarka, kodan tarin alkairai dake tartare da ita, na tabbata Nawal tasamu uwa tagari wadda kullum take maka nacin samu, INA tayaku farincikin mallakar Rahma kaida Nawal, ka kwantar da hankalinka kakuma rik'eta amana"._ Shirun dayajine yasakashi mik'ewa zumbur yafara dube dube da mutsike idanu, Kodai mafarki yakeyi?, da gsk fa muryar Ni'ima yaji wlhy. Jikinsane yafara Rawa, cikin Sauri yabar cikin lambun Dan aganinsa wata aljanace takeson bud'e MASA ido. Cikin hanzari ya iso harabar gidan inda su ya ishaq suke, Dan bandasu wajen maida 'yan kawo amarya. Najeeb abokin ya Ishaq ya ce, "ango lfy kuwa naganka a hargitse?, ko duk murnar zuwan amaryarne?. Saurin saisaita nutsuwarsa yayi ya sauke ajiyar zuciya yanajan farar kukera d'aya ya zauna, babu komai ya Najeeb yafad'a ad'an d'arare. Wai tun d'azu kana ina?, ya Ishaq ya tambayeshi. Ina lambu." Yabada amsa atak'aice. Hira su ya Ishaq sukeyi amma bobo kokad'an baya sakamusu baki, addu'oi kawai yake zabgawa azuciyarsa, fatansa ALLAH yasa abinda yaji ya tsaya iya haka. Suna nan zaune har aka kira sallar isha'i suka tafi sukayi. Amarya tanacan ana zabga mata kwalliya, da k'yar aunty Sameera da aunty ummy suka lallasheta tayi shiru aka fara kwalliyar. Hummm amaryafa tagama had'ewa abin kamar babu gobe. Shiryata akayi cikin farar doguwar riga ta aure, amma mai dogon hannu, aka nad'a mata d'aurin d'ankwali da bak'in d'an kwali, tasha sark'ar gold wadda k'yautace daga Abba, kai jama'a yaufa take sallah, amma awajen amarya

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});