Chapter 59
Chapter 59
eheβπ._* _πluv you so much, my sweet sisters, Hafsat xoxo, Hafsat Rano, 'Yar Ficika & Zarah Bukar, hajjace, Ayusha ilyasu, gaisuwa agareku dafatan Alkairi._ πππππππΌ. 6β£1β£ *_5:12pm_* bobo yamik'e tareda harhad'a takardun dazai buk'ata agida, yacire laptop d'imsa daga caji yasaka a jakka, bayan yagama had'a komai yakashe kayan wutar office d'in sannan yad'auki rigarsa ta lauyoyi ya sak'ala ahannu, yarataya jakar aikinsa akafad'a yafito. Da sauri Kamilu yataso yana fad'in oga kafito?. Nafito kamilu, zan wuce gida kuma. Kamilu ya washe baki tareda kar6ar key d'in hannun bobo ya kulle k'ofar, fitowa sukayi har wajen mota yarakishi, Dan tuni sakatariya Madeena tana gida, k'arfe hud'u da rabi yake sallamarta ita. Saida yashiga motar sannan yad'ago yana kallon Kamilu, to kashigo muwuce mana Dan naga garin kamarma hadarine. Dariya Kamilu yayi yabud'e mortar yashiga yana fad'in oga ai damunar tafara kankamane, nanda 'yan satittika zakaga ruwa yafara wadata. Murmushi kawai bobo yayi danyasan surutun Kamilu baya k'arewa, ahankali yake Murza kan motar yana kuma sauraren karatun alkur'anin dake tashi amotar cikin k'ira'ar shriek Abdurrahaman sudes, har k'ofar gida yakai Kamilu yamik'a masa kud'i yana fad'in gashi asaima uwargida kaza. Cikin washe baki Kamilu yakar6a yana godiya, wannan dalilin yanasakashi k'ara ganin kimar ogan nasu, kwatakwata bashida k'yankyamin talaka bare girmankai irinna alhazan birnin nan, gashida alkairi kullum baya gajiyawa. Har bobo yafice daga anguwar Kamilu natsaye yana kallonsa, saida ya6acema ganinsa sannan yashiga gida cikeda farinciki. Ganin hadarin nak'ara tasowa yasaka bobo k'ara gudun motarsa cikin 'yan mintuna k'alilan ya Isa gida, guri yasamu yay parking sannan yakwashi tarkacensa yanufi ciki, zuwa sannan anfara yayyafi. Rahma tana kichin Dan k'ok'arin had'a abincin dare taji ana kwankwasa k'ofa, fitowa tayi da hanzari dakuma tunanin wanene haka? Acikin hadarinnan. Batayi gaggawar bud'ewaba saida ta ce, "wayene?. Jin haka yasa bobo niyyar tsokanarta, ya mak'e murya kamar mace ya ce, " nice hafsat Xoxo budurwar bobo. Gabantane yafad'i gakuma wani k'ululn bak'inciki aranta, cikin masifa ta ce, "ai bayanan saiki koma sai sanda yadawo kizo. Pls madam ki taimakeni ruwafa na jik'ani. Yo ya kasheki mana, Rahma tafad'a ak'ufule tareda juyawarta kicin. Magana yasakeyi yaji shiru, ga ruwa yafara jik'ashi, da Sauri yanufi baya yaduba ko k'ofar kichin abud'e take ta baya, yana turawa tabud'e, yashigo da hanzari Dan tasowar wata iska mai sanyi. Da sauri Rahma tajuyo dansan ganin waye, ido tad'an zaro waje Dan mamaki, sannu dazuwa tayi maganar a cunkushe Dan tuna abundana yafaru yanzu tsakaninta da Xoxo. Dariya tabashi danganin kishi k'uru k'uru kwance afuskarta, amma saiya gimtse ya ce, " yawwa. K'arasowa tayi inda yake tsaye takar6i jakarsa da rigar, sai wani kakkauda kai takeyi. Lfy kuwa?, naganki haka?. Lfy lau tafad'a tana nufar cikin falo. Binta yayi da kallo yana murmushi, zame rigar suit d'insa yayi danta d'an jike yaja kujerar dake kicind'in ya zauna yana cire takalminsa. Rahma tadawo kichind'in ganinsa azaune yasata binsa da kallon mamaki, dukda yaji shigowarta amma bai d'agoba saida yagama cire takalmin yad'ora k'afarsa fara Sol Asama. Rahma ta ce, "azuciyarta, hummm jik'afa kamar ba'a takata ak'asa........ Bobo yad'ago shima yana kallonta, nikam Nusfulhayat wana ganin ak'ofar falo tsaye kamar mace?. Baki Rahma taturo gaba, ta kauda kanta gefe, nima bansaniba. Ido yazaro waje bakisanibafa kikace?, datazo batayi Knocking bane?. Hawayen datake mak'alewa suka zubo akumatunta, cikin shagwa6a ta ce, " bakai tazo nemaba, kuma ta ce, "budurwarkace ita. Yaso ya shek'e da dariya amma saiya dake, yamik'e da Sauri yana fad'in amma kika barta awaje ruwa na dukanta, yanzunan cute sokike kifara korarmin 'yammatane?, kwasar takalmansa yayi ahannu yawuce cikin falon. Rahma taduk'e kanta ajikin cabinet d'in kicin tana kuka. Shikam bobo d'akinsa yanufa yana 'Yar dariyar farincikin ana kishinsa Ashe?, kayansa yacire yafad'a wanka. Itakam Rahma saida taci kukanta ta more sannan tad'ago tacigaba da girkin, jitake dama batayi MASA girkinba, tsaf ta kammala komai tajere a dinning sannan tagyara kichind'in tsaf. Dubanta takai ga agogon falon, ganin lokaci yayi nisa tanufi d'akinta ta tatada Nawal dake barci Dan magriba ta k'arato, hannunta taja zuwa bayi tawanke mata fuska sannan suka dawo falo tabata ruwa.......hummm ni shinema yau ko ruwan ba'a baniba bare akula dani, maganar bobo tadaki dodo kunnenta. Da Sauri Nawal takwace hannunta taje tarungumeshi tana fad'in my papa oyoyo. Shima d'aukarta yayi yad'aga sama, my baby INA kika shigane bangankiba?. Papa barci nakeyi yanzu momyna ta tadani magriba tayi. Oh 'yargatan momynta yafad'a yana sumbatar kumatun yarinyar. Rahma dai tana tsaye tana kallonsu cikeda sha'awa, hannunsa yasa yakare fuskar Nawal sannan yad'agama Rahma gira, kauda kai tayi tanad'an murgud'a baki. Ya ce, "Niko?. Nidaifa banceba ehe, itama tafad'a kamar badashi takeba. Murmushi yayi sannan yadire Nawal, baby sauka nasha ruwa tunda an hanani. Da d'an gudu Rahma taje gaban firij tad'akko ruwa da cup takawo MASA. Bobo yayi dariya tareda fad'in ashedai ana tsoron kishiya. Gaba tayi tashige d'akinta tana tura baki, shikuma yazuba ruwa a cup yasha yana dariya. Nawal ta CE, " papa yaushe zamu tafi gidan Ammi?, gobene bikinsu aunty khursiyya. Saida ya shanye ruwan sannan ya ce, "jekiyi sallah idan nadawo masallaci zan sanar miki. d'akin momynta tanufa shikuma yadoshi hanyar fita, yabud'e sannan yad'an lek'a, ruwa akeyi sosai Dan haka yahak'ura yajuya d'akin Rahma dansuyi jam'i. Shigar tasa tayi daidai da fitowar Rahma daga bayi, da alama alwala tayi, baice da ita komaiba ya gyara shimfid'ar sallayar, itama ganin haka yasa tagane abinda yake nufi. Yana gaba suna baya itada Nawal yajasu jam'in magriba. Bayan sun idar Rahma ta d'akko alkur'ani tana koyama Nawal, shima yana zaune yana kallonsu cikeda jin dad'i, har lokacin sallar isha'i yayi suka mik'e domin gabatarwa. Saida yamusu doguwar addu'a sannan kowa yamik'e suka fito falo. Bobo yazube saman kujera yana fad'in wash ALLAH na, Nawal tazauna kusadashi my papa bakada lafiyane?. A'a baby nagajine kawai....... ga abinci fa....Rahma takatse musu zancen tana kallonsu. Fararen idanunsa yad'ago yana mata wani shu'umin kallo, ta kauda idonta daga kansa shima saiya ta6e baki. Nawal tamik'e shikuma ya ce, "nidai nagaji bazan iya hawan dining ba. Yanda yay maganar ashagwa6e saiyabama Rahma dariya, dinning tanifa tana murmushi, komai saida suka sakko dashi tsakkiyar falon. Tana niyyar zuba abincin taji ya ce, " kihad'amana a filet d'aya kawai, batace k'alaba tacigaba da zuba abincinta, bayan tagama ta tatura gabansa. Gyara zamansa kawai yayi yafara cin abincin atsanake, Rahma azuciyarta ta ce, "guy d'innan komai yahad'a, cin abincinsama abin kallone. Hakadai suka gama cin abincin anutse, daganan aka koma kallo, Nawal najikin papanta kwance yana shafa kanta ahankali. Tuni barci yad'auketa, yakalli Rahma dake kwance a 2sita tana game da wayarta, momyn Nawal zoki d'auketa tamin barci ajiki. Mik'ewa Rahma tayi domin d'aukar Nawal amma saiya jawota ta zauna akusadashi, hannunta yarik'e gam sannan yashiga k'ok'arin janye Nawal daga jikinsa cikin dabara. Rahma ta turo baki gaba, yatsu biyu yasa ya d'alli bakinta, da sauri tasaka hannunta awajen Dan zafi, cikin shagwa6a ta ce, " wayyo bakina. Habawa yarinya nagafa kamar kinfara rainani, bobo yay maganar yana matseta ajikinsa. Shinwai ni sa'ankine?. Da sauri Rahma ta ce, "a'a dantaji zafin d'allar mata baki dayayi. Ya ce, " to miye kiketa wani kumbura fuska?, nifa babu komai kaina yake ciwone. Ayya my Angel sorry, namiki kamu?. Kai tad'aga masa alamar eh. Ahankali
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83