Chapter 64
Chapter 64
cigaba da yawan kallonsa sai rankowa ya6aci awajennan Dan haka ku kama kanku. Wata ta ce, " amma ba gidannan yakeba?, Dan ban sanshiba. Dariya khairiyya tayi ta ce, "to k'arewar gidannanma shi muke bimawa, dagashi saimu. Cikin mamaki sukace amma dai wasu sun rasu a tsakaninku?, kumafa mudai bamu sanshiba, kai 'yan biyu kuji tsoron Allah. Hhhhhh lallai baku yardaba kenan?, to yagirmemu sosai Dan Ammi ta ce, " wajen ahekara 12 yabamu, bayan shi harma ta fiddarai da haihuwa saigamu mun wuntsilo, abinda yasa Baku sanshiba bashida hayaniyane, kuma bakowace sabga bace zaku ganshi aciki, shinefa wanda kukazo bikinsa wata biyar dasuka wuce baya. Idanu suka zaro, Zainab kabeer ta ce, ''wlhy bamu ganeshiba kinsan da daddare muka Ganshi awajen deener, masha ALLAHU, ina matarsa?. Tana nan bara zaku ganta aii. Bobo dabaisan sunayiba yahaye saman mota yazauna Dan bayason shiga falon saboda duk matane, harabar gidan tad'anfi k'arancin mutane tunda an ragu, Taufiq babban d'an ya ishaq yakira, ya ce, "my son ina auntynka?. Taufiq ya ce, "uncle aunty Rahma?. Eh, ita. Yanzu naganta itada heebba sunshiga falo. Yauwa jeka kiramin ita to. To uncle. Babu dad'ewa saiga Taufiq yadawo ya ce, " uncle tana zuwa. Okey my son, yanzu kuma sai ina?. Uncle muna tarene nida abokaina. Kaima gayyan kayo wajen taron mata?, maimakon kabari sai ranar d'aurin aure ko gobe wajen brother's Night. Uncle aii duk zasuzo shima. Dariya bobo yayi ya ce, "to na mata. Shima Taufiq tafiya yayi wajen abokansa yana dariya. Na ce, " masha ALLAHU yaron yafara zama saurayi, su bobo ankusa ajiye surukai, lol. Yana zaune awajen yana latsa waya saiga Rahma tafito. Kamshin turarenta kawai yaji yad'ago. Kallo d'aya tamasa ta kauda kai. Murmushi yayi yana kallonta, ya ce, "kai my Nusfulhayat kinyi k'yaufa, kamarma kece amaryar wlhy. Ganin ta kauda kai ya ce, "madam har yanzu fishinne?. Batace komaiba itadai, kuma fuskarta asake take gudun kar mutane su fahimci wani Abu. Ya ce, " my Nusfulhayat yunwafa nakeji, gashi duk mata agidan nama rasa yanda zanyi. Murmushi mugunta tayi ta ce, "ina Safnar tabaka abinci?, ko sak'one naje nafad'a mata?. Kallonta yayi ido cikin ido, tai saurin kauda kanta Dan bazata juri kallon cikin idonsaba, shima murmusawa yayi ya ce, " idanma kinyi hakan ai babu laifi, yadiro daga saman motar, ki kaimin falon su inna munacan nidasu ya Sulaiman. Baijira amsartaba yawuce............ *_"happy juma'at Mubarak."_*ππΌππΌππΌππΌ *_luv u oll._* *_(((S)))......2017_* [11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ»typing........ β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£ _β’π ±π Ύπ ±π Ύβ’_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* _a *RASHIN SANI* nayi *AUREN K'ADDARA ko BIYAYYA,* mizan d'auketa?, *K'ANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA?.* San zuciya yakawo sa6ani *NI DA AMINIYATA*, salon *NAWAFF* yasani fuskarntar *SABON AL'AMAREE*, *KUKAN KURCIYA JAWABINE* dan haka kugane *BAN SAKETA BA* masoyan *ABDUL-MALEEK BOBO* mukasance tare a *BABU SO, MIYA KAWO KISHI?!!!*._ππΌ _wad'annan sune rukunin jerin books dani bilyn Abdul narubuta a social media._ Zaku iya samunsu a shafina kamar haka.ππ» https://mrsbilkisa.blogspot.com *_sai kunjeππΌ._* *_BAK'IN HAURE!_* zaizone a sabuwar shekarar 2018 insha ALLAHU, karku bari ayi babu kuπ. 6β£4β£ Binsa tayi dakallo tana k'unk'unai, amma baijitaba Dan yayi gaba abinsa. Safna tana dagacan saman kujera tana kallonsu, hawaye suka cika mata ido taisaurin saka handkyn daya bata jiya tagoge, ta Yanke shawara yau zatabi su Ameera sutafi gida, Dan inhar tana ganin bobo bata tunanin sonsa zai ragu azuciyarta barema ayi tunanin fita gaba d'aya, amma idan tayi nesa dashi k'ila taji sauk'in zuciyarta, Dan insha ALLAHU tayi tuba na gsky kenan. Rahma tahad'a musu abincin Wanda dama tun d'azu ta tanada domin su, ihsan da Basma ne suka tayata d'auka zuwa 6angaren inna. Duk sunacan harda Ammar dawasu mutum biyu dabata saniba, bayan sun ajiye suka gaidasu, idanun bobo nakan matarsa, itama tasaci kallonsa ganin idonsa akanta yasa ta kauda idonta tareda Jan hannun su ilham suka fice. ...........................Γ· Bayan sallar isha'i su anty Hafsat sukace zasu wuce, Safna data gama had'a kayanta tamik'e itama, kallonta kawai Rahma takeyi amma batace komaiba, su dama su aunty Ameera tafad'a musu zata bisu Dan gidan yacika damutane kuma Rahma anan zata kwana itama, basu kawo komai aransuba sukace eh gara kawai tatafi gida. Har harabar gidan tarakasu saida suka Shiga mota taga fitarsu sannan takoma ciki. Amota Safna cikin dabara take share hawayenta, wata zuciyarta tana fad'a mata anya zata iya daurewa kuwa?, da sauri ta ce, "insha ALLAHU zan iya. .+.+.+.+.+. Tafiyarsu Safna babu dad'ewa sosai bobo yashigo falon, wasu kallo sukeyi wasukuwama harsun kwanta, yagaidasu sannan ya haura sama, afalo yatarar dasu zaune sunata kulla kayan rabo, zama yayi yana fad'in wai Kodai yau anan zamu kwanane?. Kallonsa ammi tayi, ta ce, " nidama zaku barsu su kwanan Aida yafimin, idan bamu gamk'ullin nan yauba nasan zuwa gobe gidannan zai d'inke da mutane. Kansa yashafa yana d'an murmushi Ammi sudai gama kawai saimu wuce ko zuwa 12 ne. Hararsa Ammi tayi cikin wasa, ta CE, "fin k'arfi za'a nunamin akan 'ya'yana?. A'a Ammi mu mun isane. Hira sukaitayi har su ya ishaq suka shigo suka had'u gabad'aya sukayi k'ullin sannan kowa ya d'auki matarsa sukai gida. Biki yacigaba da kankama cikin farin ciki, komai yana tafiya yanda yadace, washe gari da safe akayi k'unshi, zuwa yamma gida kam ya d'inke da bak'i na nesa Dana kusa, su Rahma kam aii ko ganinsu ba'ayi Duk sun zama busy, to barema su bobo manya manyan yayye. Da daddre k'arfe takwas aka fara d'ibar mutane zuwa wajen brother's night dasu bobo suka shirya, abokansu sosai suka gayyato, taron 'yammata da samarine kawai saikuma irinsu bobo masu mata, amma babu yara bare tsofaffi. Taro yak'ayatar kam masha ALLAH, amare da angwayensu ansha k'yau abin sai Wanda yagani, su bobo suntaka rawar gani irinta manyan yayye, ko INA yashiga yana mak'ale da matarsa abin zak'yk'yau da burgewa, 'yammata kam dayawa sun k'yasa, saidai ganinsa mak'ale da matarsa yakansa sushiga taitayinsu. Alhmdllh dahaka taro yatashi lfy kowa Yakama gabansa. _washe gari_ Aka d'aura auren khairiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Ahmad m sadiq, sai Khursiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Zaharadden usman Aliyu. Masha ALLAH d'aurin aure yatara d'unbin jama'a nanesa Dana kusa 'yan siyasa da masu mulki, 'yan kasuwama ba'a barsu abayaba. To khairiyya da khursiyya saimuce ALLAH yasanya alkairi yabada zaman lfy da zaman hak'uri. Hummmm abun mamaki wai harda alhaji sunusi dala a 'yan d'aurin aure, (araina nace su alhaji sunusi anji yajiπΆπ€£ ahanun bobonmuπππ) aiko bobo sai antaya MASA kallon banza yakeyi. Shidai baimasan yanayiba. Bayan kammala d'aurin aure su bobo sukaima anguna jagora zuwa cikin gidan, shidasu Yaya ishaq duk wankan farar shadda sukayi, masha ALLAH daka gansu kaga 'yan uwa jini d'aya. Har cikin falon suka Shiga anata gaisawa da 'yan uwa da abokan arzik'i, bakin anguna yak'i rufuwa hakama su ya sulaiman suna cikeda farin cikin yau k'annensu sunyi aure. Tunda sukashigo falon bobo yaketa baza ido domin hango Nusfulhayat d'insa, rabonsa da ganinta tun jiya bayan sun dawo daga faty. Ganin duk d'unbin taron Matan falon bai Gantaba har sama dasuka haura aka gaisa dasu ammi nanma bata nan baimaga Matan yayyensaba ko d'aya. Sakkowa yayi yabarosu a can, wayarsa yaciro a aljihu yafara kiran number ta amma bata d'aukaba, yana nan tsaye yanad'an waige waige saiga Nasiba zata shige
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83