Chapter 8
Chapter 8
fenti da abundan ba'a rasaba tunda andad'e babu kowa agidan, "tun bayan rasuwar Ni'ima daya Shiga rud'ani kamar yayai hauka yasa Appa ya tattaroshi yamaido gida kusadasu. Kayan lefe kam sunyi masha ALLAHU saidai mak'iyi aunty Rashida matar ya is'haq tafad'a tana fesama kanta turare. Dariya suka shek'e da ita suduka, aunty Sameera matar ya Hamza ta ce, "k'yaface haka aunty Rasheeda tunda kina ragema amarya turare....... To aii gara kafesa, k'ila idan amaryar tazo wannan mijin nata maikama da soja ya hanaka fesawa. Dariya suka kuma shek'ewa da ita harda tafawa kamar wasu k'awaye. Adai dai wannan lokacin kuma Bobo yashigo falon shida ya Hamza. Ahankali suka fara tsagaita dariyar tasu, ya Hamza ya ce, " kukuma lfy?, miya sakaku dariya haka?. Aunty Sameera ta maimaita musu abinda yafaru, dariya ya hamza yayi, bobo kam saiyayi murmushi yana kallon aunty rasheda dake dariya, ta ce, "ka kafeni da ido konayi k'aryane?. Kauda Kansa yayi yana murmushi, ya ce, " aunty Rasheeda kenan, kisanifa saikin biyama matana turarenta babu d'aga k'afa. Nanmadai dariya akayi, Aunty ummy ta ce, "lah bobo dama kanason auren nan amma idan anyi magana kaita wani basarwa?. Okey da kin d'auka banasone aunty ummy?, tsaya kiga ikon ALLAH bayan d'aurin aure zakisha mamaki Romeo zan zama. Dariya sosai sukeyi harda ya hamza da Ammi dake sakkowa daga saman Appa. Shikam bobo d'akinsa yashige yana murmushi. Bayan sunyi dariya mai isarsu suka koma tsokanar bobo ya Hamza yana kare masa, danshi tunda yashige d'aki yak'i fitowa. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Alhmdllh yau lefe ya iso gidansu Safna, anyima 'yan kawo lefe tarba ta girmamawa, kowa ya kalli lefen saiya jinjina kai, Dan kayane masu k'yau da birgewa. Sund'an dad'e agidan sannan suka tafi cikeda tukuyci na girma. Cikeda zumud'i Rahma tashiga d'akinsu, Safna tana zaune tana chart da baseera daketa k'ara zugata wai karta yarda da wannan auren, *boy ya ce, " yana gab da samo mata bobonta. Murmushin jin dad'i taketa zabgawa, k'arar rufe k'ofa da Rahma tayi yasa Safna d'agowa, Rahma tak'araso gurinta tana washe baki, aunty Safna kinga kayan lefenki kuwa jar ubancan kai, wlhy kamar basusan ciwon kud'iba. Baki safna ta ta6e sannan tagallama Rahma harara yarinyarnan na kula kemafa kanki da motsi, banace kidaina jingina aurennan danibane Dan uwarki, kakin yakamata kitaya farinciki Dan lefennan nakine baniba kam, saikuma tayi wata 'Yar dariya Rahma lefena yana nan zuwa daga Bobona, k'ilama sannan kinada ciki hhhhhjhhhh ta shek'e da dariya harda rik'e ciki. "Na ce, " hummmmm". Rahma kam girgiza kai kawai tayi, tana mamakin halin kafiya da dagiya irinna Safna, tanayin Abu kamar batada ilimin addini, ALLAH ya k'yauta tafad'a afili tana ficewa ad'akin. Amin safna tafad'a ita tana Raka Rahma da harara. Ran Abba a 6ace yake, sai safa da marwa yake afalonsa, gobe d'aurin aure amma Safna ta tsaya kaida fata bata son aurennan, yau Uncle Abubakar sau biyu yana dukanta shida ya Shaheed amma tace Sam batasan zancenba, daga k'arshema kayanta tahad'a waizata bar musu gidan. Ya Shaheed ne yashigo falon Abba da sallamasa, Abba ya amsa yana mai tsurama Shaheed d'in ido kamar yau yafara ganinsa, ya Shaheed ya rissina ya gaida Abba sannan ya zauna ak'asa kan kafet. Shima Abba saiya nemi waje ya zauna. Ya Shaheed ya sauke numfashi Kansa ak'asa ya ce, "Abba dama wata shawarace nazo da ita. Ina jinka Shaheed Abba yafad'a da hanzari. " Hummm Abba inaga tunda Safna tak'i har yanzu, dataje tamana abin kunya inaganin kawai mubarta, inhar zasu yarda kawai abashi Rahma. Abba yazaro ido waje, Shaheed baka ganin Rahma batayi k'ank'antaba!?. Abba batayi k'ank'antaba, tafa gama secondary, kuma yanda nasan Rahma da hakuri da biyayya bazata bijirema umarninkaba kamar yanda safna tayi, nasan zata yarda ta auri Abdulmalik indai Rahma ce...... Dai dainan Rahma tashigo falon, tiren dake hannunta ya su6ce, abinda ke ciki yazube jikinta sai rawa yake saboda jin furucin ya Shaheed na k'arshe. Ya Shaheed ne yamik'e da sauri yakamota ya zaunar, cikin taushin murya ya ce, kiyi hak'uri Rahma kibi umarnin Abba kifiddashi daga kunyar mutanen daya tara, kikalli gidannan cike yake da danginmu, wasuma daga wani gari suka taso, kituna d'unbin mutanene da Abba ya gayyata wad'anda zasu halarci taron d'aurin aure gobe idan ALLAH ya kaimu. Rahma kema kinason Abbanmu yaji kunya?, kamar yanda Safna tayi, jibi kiga yanda hankalin Abba yake atashe akan abinda baifi k'arfiba daga garemu. Rahma tad'ago kai takalli mahaifinsu dashima su yake kallo, gabad'aya fuskarsa ta canja, Abbansu muntum mai sauk'in kai da hak'uri amma yau 6acin rai ya maidashi wani iri, ita saitagama kamar yarame..... Ya Shaheed yad'an ta6ata, da sauri takalleshi, ya ce, "baki aminceba kema ko?. Yanda ya Shaheed yay maganar saiya bata tausayi shima, ahankali ta jinjina kai, cikin kuka ta ce, " nayarda yaya wlhy na amince zan fidda Abba kunya... Shashshekar kuka tahanata k'arasawa." Cikin farin cikin ya Shaheed ya rungumeta, Abba kuma yarungumesu gaba d'aya. Sai albarka suke saka mata da addu'ar fatan alkairi, itakam tana kuka tana sharar hawaye. Abba yakira Appa ya sanar masa komai bai 6oye masaba. Appa ya ce, "babu wani damuwa da Safna da Rahma duk d'ayane tunda daga tsatso d'aya suka fito, shima yayta sakama Rahma albarka. Abba yaji dad'i sosai, sukayi sallama. Ummi ma Abba yakirata tazo d'akin, jin abinda yafaru yasa ta rungume 'yartata cikeda farinciki dakuma saka mata albarka, saidai gefen zuciyarta tana tausayin Rahma, aganinta nawa Rahmar take, amma babu yanda zasuyi, sun tara d'unbin mutane wannan ne kawai mafita agaresu Baki d'aya. Fatanta ALLAH yasa mijin nata yakasance mai kula da tausaya mata, Dan Rahma tanada rauni sosai, dukcikin 'yayansu babu Wanda yakai Rahma hak'uri, daga ita sai ya Muneer, sune suka d'ebo halin mahaifinsu Sak, na Rahma ma yafi nasa, Dan Rahma akwai hak'uri, kuma yaran gidan duk sunfita k'yau sosai. Rahma ba fara bace amma tanada d'an haskenta daidai gwargwado, zamu iya kiran rahma tsaka tsaki batada tsawo bakuma gajera bace, tanada d'an jiki Dan 'Yar lukutar ummi ma da akece mata, idan akafad'a tayita kuka bataso, tanada k'yanta daidai gwargwado (saidai Safna tafita k'yau nesa ba kusaba), Abu mafi d'aukar hankali ajikin Rahma shine idanunta, wasu irin idanu Rahma take dasu masu hasken tsiya da girma kamar suffar kwai, duk yanda ran Rahma ya6aci basa canja kala saidai su k'ank'ance. ALLAH yabama Rahma baiwar juya idanu, gasu masha ALLAHU da girma, sau dayawa idanun Rahma kan fisgi hankalin mutane kanta Dan danan tashiga ransu Dan ita mutumce mai saurin Shiga rai, indai zaka zauna da ita saita shiga ranka. Wannan kenan.π€Έπ»ββππΌ .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Labaridai ya isa kunnene Bobo "wai Amarya bata sonsa", amma abin bai bashi haushiba sosai, tunda dama shima ba auren yakesoba, Dan haka da yarinyar tasoshi da karta soshi duk uwar ubansu d'aya ko akwalar rigarsa, shi dama wadda za'a bashi yanzu d'in ta ce, " itama bataso, da wlhy har k'yauta zai mata. Na ce, "hummmm......... β€β€β€β€β€β€β€ *_masoya kumuje zuwa yanzufa aka fara gashi suya sai ran sallah_*πππΌ [11/12, 2:16 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ» β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£ _{Bobo}_ _Story & editin_ *_Aunty Bilyn Abdul_* βπΏ _Written_ *_Marak'isiyya_* _hak'in mallaka_ *_Aunty Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Bily giro_* 1β£7β£&1β£8β£ Kafin la'asar zazza6i yarufe Rahma, tana d'akin Abba kwance ak'udundune, ya Muneer yashogo da Dr kaleed har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83