Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ina zuwa. Laptop yajawo yafara danne dannensa, bayan wasu 'yan mintuna saiga kamal, hannu yabashi suka gaisa, sannan ya zauna. Wai ina ka mak'alene?. Laptop d'in gabansa ya ture gefe, yadafe tebir yana kallon Kamal, kabari kawai d'an uwa inacan an ritsani za'a kashe. Ban ganeba?, kisa kamar ya?. Ajiyar zuciya bobo ya sauke, ya CE, "wlhy kuwa kamal, wasu k'anan karnukan farauta aka turo waisu kar6i takardu a hannuna, nasandai bai wuce aikin wawayennan ba. Suwa kenan?. Ra'ees da babansa mana, Dan babu wasu takardu ahannuna saina kes d'insa, kuma sakatariyata tace yazo nemana. Kwarai kuwa d'azu Nazo danmuyi magana baka nan, to ayayin shigowata mun had'u, zaifita nikuma zan shigo. Humm, kamal lokaci yayi dazan fito naci uban mutanen nan fa. A'a Abdulmaleek karkayi haka, har yanzu munada sauran bincike kaima kasani. Hakane, amma wlhy natsanesu. Wlhy nima hakantake, yanzudai bara naje, inada wata shari'a anjima kad'an, idan mungama zan dawo. Okey saika dawo to. Tunda kamal yafita yabar office d'in bobo yafad'a duniyar tunani, tunanin Rahma ya kanainaye zuciyarsa gaba d'aya, haka kawai yarinyar tana birgeshi, ko kad'an batada damuwa. Murmushi yayi tareda kauda tunaninta yamaida hankalinsa ga tuno Wanda zai iya turo masa 'yandaba, yamik'e Dan har yanzu ransa a6ace yake, wani wawan huci yafurzar tareda naushin iska, waini za'a turoma 'yan daba yafad'a cikin k'araji, yacije le6ensa yana gyad'a kai humm zanyi maganin koma wane d'an iskane. K'arasawa yayi gaban firij ya tsiyaya lemo akofi yakoma jikin windown office d'in na gilas ya tsaya, hannunsa d'aya a aljihu d'aya rik'eda kofin. Ahankali yakai kofin bakinsa yakur6i lemon, idonsa akan mutanen dake fitowa awasu bak'ak'en jeep, Alhaji Abdurazak yafad'a yana gyad'a kai tareda ta6e baki, yad'anyi shiru alamar tunani, amma miyasa tunanina bai kawomin kai acikin wad'anda zasu iya turamin 'yan daba ba?. Yasaki murmushin nan nasa na mugunta. Sakatariya taturo k'ofar da sallama. Bai juyoba amma ya amsa sallamar. Ta ce, "sir....... Hannu yad'aga mata, ya ce, " kice yashigo. Tad'an zaro ido Dan abin yabata mamaki, bayau Alhaji abdurrazak yafara zuwa office d'innan ba, kuma duk sanda yazo oga baya bashi damar shigowa, Amman yau tunkan tafad'i ko waye yace yashigo, kuma tasan yagansa ta inda yake tsaye, kai lamarin da mamaki. Itadai haka tak'arasa tasanar da Alh Abdurrazak, shima abin yabashi mamaki amma saiyayi tunanin ko bobo yaji tsorone. Bobo yana tsaye baikuma juyoba har Alhaji ya zauna, saida yaja tsawon Minti biyu sannan yajuyo, taku yakeyi cike da isa harya k'araso mazauninsa. Abin ya harzuk'a Alhaji amma saiya dake. Bobo dake lila kujerarsa ahankali, idonsa akan alhajin ya ce, "Alhaji mike tafe dakaine?, yay maganar cikin salonsa na isa. Alhaji yacije le6en jin haushi, saikuma yayi murmushi Barrister nazo maka da Business ne. Bobo-- hummm wane irin business?. Alhaji-- Akan aikine. Bobo--- miyasa saini?. Alhaji-- saboda ka cancanta. Bobo-- kayi kuskuren fahimtar hakan. Alhaji-- miyasa kayi gaggawar yanke hukunci?. Bobo-- saboda hakane yadace, kuma nasanka nasan kaina, bamu dace da had'a business ba. Alhaji-- a'a Barrister ka saurareni. Bobo-- mizaisa na saurareka?. Alhaji-- Saboda nayimaka bayani yanda zaka aminta dani. Bobo yayi murmushin rainin hankali, Alhaji miyasa kakeson takuranine?. Kayi hak'uri maganata mai muhimmancice tasha banban data baya Barrister. d'an kafeshi da ido bobo Yayi, dayin tunani na second 20, yalumshe idonsa ya ce, " INA saurarenka. Murmushi Alhaji yayi, azuciyarsa ya ce, "dole ka saurareni aii, yagyara zama yana fad'in Barrister dama akan maganar yaron aboki nane Alhaji sunusi dala, nawa kakeso mubiyaka ka lalata shari'ar?. Bobo bai amsa masaba, hasalima hankalinsa yana kan bodyguard d'in Alhajin dake k'ok'arin zarar wata takarda da bobo ya ajiye akan Derk's d'insa. Murmushi bobo yayi ya ce, " mai gadi zaka saidama mai k'osaine?. Dasauri bodyguard d'in yacire hannunsa Yakuma matsa baya. Bobo ya girgiza kai yana maida kallonsa ga Alhajin, INA saurarenka. Alhaji da haushi yakashe, jiyake tamkar yasa aharbe MASA bobo Dan haushi da tsanarsa dayayi, yazaro sigari yasaka abaki, dasauri d'aya daga cikin bodyguard d'in yakunna leta zaisakama alhajin....hannu bobo yad'aga masa, yatashi tsaye tareda rankwafowa akan tebir d'in yasaka yatsunsa biyu yazare sigarin bakin Alhajin yana girgiza kai, sorry Alhaji ba'a shamin sigari a office, saboda yana lalata lafiyar maisha da mai shak'ar warin. Ya ajiye masa kusadashi akan tebir d'in, gata nan idan katashi tafiya zaka iya d'aukar kayanka, Yakoma ya zauna. Wani Abu ya danna yay k'ara saiga sakatariyarsa da Sauri tashigo, bai kalletaba ya ce, "kawoma Alhaji abin sanyaya mak'oshi Dan yana buk'ata. Okey sir, tafad'a cikeda girmamawa. Alhaji kam ya k'ame azaune, lallai yak'ara tabbatarwa yaron nan d'an iskane, amma zasu gyaramasa zama, a fusace Alhajin yamik'e yakar6i lemon da sakatariya tamik'o masa yay jifa dashi, kofin yadaki bango ya tarwatse. Wata dariyar rainin hankali bobo yayi, yamik'e yana tafa hannayensa wooow! Alhaji ammafa ka burgeni, kaga yanda kayi d'innan haka nayima yaranka Nima d'azu da safe, saidai banbancin d'ayane, kai Kofi kafasa, nikam mutane na jibga. Aburkice Alhaji yake kallon bobo kuma atsorace, amma saiya danne yahad'e fuska tareda Nuna bobo da d'anyatsa, kai k'aramin tantiri kashiga hankalinka, yaro kai k'aramin naman dajine idan yanzu mukaso saimu hallaka ka tamkar yanda muka hallaka.........haba Alhaji mikakeson fad'ane haka?. Bodyguard yay saurin Tatar numfashin Alhajin. Bobo yayatura hannayensa a Aljihu yana murmushi, ya ce, ''no no no mai gadi, Daka barsa yak'asa fad'a kaga ya ragemin nauyin bincike, amma babu laifi hakanma ngd sosai yak'are maganar da d'aga fad'a yana ta6e baki, aii kobai fad'aba nasan yanaciki. Yakuma gyara tsayuwa, yataka daf da Alhaji ya tsaya, ya ce, "Alhaji kakirani k'aramin naman daji. Bakayi k'aryaba, tabbas ni naman dajine mai amsa suna *_ZAKI_*, ni zakine bana 6arnar banza, ammafa duk sanda naji yunwa kowa Shiga hankalinsa yakeyi, Ku saurari fitowata Dan duk sanda naji yunwa saina lak'umeku amatsayin abinci mafi Girman k'an k'anta darashin daraja............ Kai!!!!. Alhaji yakatse bobo atsawace, yanunashi da d'an yatsa Abdulmaleek Aliyu kataka a sannu zakinma yanada nasama dashi ko'a cikin dajin. Dariya bobo yayi ya ce, " hakane Alhaji akwai manya manyan namun daji adokar daji, wad'anda sukafi zaki Girman jiki harda shekaru, amma girmansu baya hana zaki ya kacaccalasu aduk sanda ya harzik'o, barema idan yanakan ganiyar k'uruciyarsa, Dan haka Alhaji abdurrazak bulama Ku saurari matashin zaki yana nan tafe gareku, zaka iya barmin office kuma ka saurari sammaci, Dan zan maka ka akotu kaida karnukan farautarka, inason bin ba'asin bibiyar numfashina da kukeyi....... Fuuuuu Alhaji yafice batareda yaji k'arshen zancen bobo ba, jiyake idan yakara minti d'aya a office d'in zuciyarsa zata bugane kawai. Wani wawan tsaki bobo yaraka Alhaji dashi. _(Na sauke nannauyan numfashi Dan ganin anrabu lafiya bobo baikai dukaba, danni yanzu tsoronsa nakeji)._ *_bayan kwana uku._* Yau tsawon kwanaki uku safna tanata sak'awa da kwancewa, kullum Neman hanyar dazai kaita gidan Rahma takeyi amma tarasa gaba d'aya, tayi wujiga² saboda rashin mafita. Ganin babu yanda zatayi yasa tasaki jikinta tanata harkokinta, agefe kuma kullum saita turama bobo message. Tunbaya kulawa har yaudai yaymata replay, wani uban tsalle tazuba Dan dad'i, tad'ane gado tanata tsalle abinta. Ganin yayi mata replay yau yasa tak'ara masa wani massage d'in na kalamun soyayya masu dad'i, amma har dare babu amsa, data kirama saiya katse kiran yakashe wayar duka. Lamarin ya Sosa ranta amma saita dake, tana fad'in k'ila baya kusada wayarne.

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});