Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

manyar garinnan, ina baby Nawal da amarya?. Saida ya sauke numfashi sannan ya ce, "suna lfy. Masha ALLAH, kasanar da amarya zanshigo weekend cin abincin amarci, daganan naga amaryar tamu, tunda ALLAH baisa ansha biki daniba. ALLAH ya kawoka Bobo yafad'a. Daga nana hirarsu suka cigaba dayi, dagani kasan sunyi bala'in shak'uwa da juna. *Waye Ammar?.* Ammar Khaleed Adam, d'ane ga Alh Khaleed Adam, abokin Appa na k'ut da k'ut wanda yayma Rahma k'yautar mota ranar walimar makaran tarsu, su 7 mahaifansu suka haifa, shine na biyar agidansu, yanada yayye maza da mata su hud'u, sai k'anne biyu mata, Ummy matar ya Hamza dakuma autarsu Lubna ita sa'ar su khairiyyace. Tare sukayi karatu da Bobo tundaga primary har secondary, daganan kowa Yakama inda yafi wayau, Bobo yatafi karatun lauya, shikuma yafad'a aikin 'yan sanda, ayanzu haka shine Qumissioner of police na jihar kano, sun shak'u sosai da Bobo, bashida wani aboki sai Ammar da yayyensa. Duk wani aiki da Bobo yarikito Wanda yake buk'atar tsaro to Ammar ne ke taimaka masa, yanzuma yayi wata 'Yar tafiyane ta wata biyu, shiyyasa baisamu damar halartar bikin Bobo ba. Shima matarsa d'aya da yara biyu duk maza. Wannan kenan............. *_luv u oll my fan's_* *_(((S)))...........2017_* [11/12, 2:25 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 3⃣5⃣=3⃣6⃣ Hankali tashe Alh sunusi ya iso gidansa, ko fakin bai bari direbansa yagamaba yafice. Matarsa na zaune afalo itada k'annen Haneef d'in yafad'o ko sallama babu. Arazane suka mik'e suna binsa da kallon mamaki, dukda ba yaune rana tafarko daya fara shigowa gida ahakaba. Ina my son?, yafad'a aburkice. Cikin mamaki haj Falmata ta ce, "Haneef?. "Eh," ya bata amasa afusace. Yanzu babu dad'ewa yafita aii, wani abune yafaru?. Wata uwar harara yasakar mata, waike wace irin shashashar uwace?, wai kina nufin bakisan 'yan sanda sunzo har gidannan sun kamamin yaroba?. Afirgice ta ce, "naga takaina ni Falmi, yaushe hakan tafaru?, yanzufa Haneef d'in yashigo gidannan ya sauya kaya yafita. Bai sauraresuba yafice yabarsu cike da tashin hankali. Abin kamar wasa Alh sunusi har dare yana Neman Station d'in da akakai Haneef amma babu ko Alamarsa, ransa yak'ara 6aci da harzuk'a, aiiko wlhy saiya d'auki mataki akan 'yan iskan police d'in dasukai k'arfin halin shigar masa gida harda kama masa tilon d'ansa namiji. Gida Yakoma danufin zaije ga Qumissioner of police gobe idan ALLAH ya kaimu, saidai zuciyarsa namasa rad'ad'i idan yatuna Haneef zai kwana a Station yau. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. *_9:30pm_* ya isa gidansa duk agajiye, jinsa yake yau fes tunda ankama masa d'an iskan nan, bayan sun gaisa da mai gadi yashige cikin gidan. Babu kowa afalon, har TV akashe yake ga gidan tsit kamar babu kowa, da alama masu gidan har sunyi barci. K'ofar yamaida yarufe sannan yanufi d'akinsa, yazube kayan hannunsa cike da gajiya, babu 6ata lokaci yacire kayansa ya fad'a bayi domin yin wanka. Bayan yafito yagabatar da shafa'i da wutiri, 'yan dube dube yafayi da alama akwai abinda yakeson gani, amma babu, d'an k'aramin tsaki yayi tareda mik'ewa yafice. Cikin barci Rahma taji ana bubbugata, afirgice ta tashi, Dan dama tsorace takwanta, saboda rashin dawowar mai gidan. Ganin shine atsaye yasa ta sauke ajiyar zuciya, ahankali ta ce, "sannu da zuwa. Bai amsaba ya ce, " ina shayina?. Tad'an dafe kanta, wlhy na manta ne. Aii yanzu na tuna miki, yafad'a yana ficewa. Asanyaye Rahma tasakko daga gadon, Dan barcin data fara yasa jikinta yin lakwas, haka ta k'arasa kicin tana jan k'aramin tsaki, idonta cike da barci tadafa masa shayin, tajuye akofi tareda yanka lemon tsami ta matsa aciki, tad'ora akan k'aramin tire tafice. Ganin baya falo gabanta yafad'i, kenanfa d'akinsa zata kai masa?, tai shiru kamar mai nazari, zuciyarta ta ce, "kije kikai karya huce Rahma ki k'ara jama kanji wani laifin", tunda tazo gidan yauce rana tafarko dazata Shiga d'akinsa, Dan haka k'irjinta keta dukan uku uku, haka tadaure ta kwankwasa, saida tayi kusan Monti biyu sannan ya ce, " tashigo. Ahankali ta tura k'ofar tashiga, wani k'amshi yadaki hancinta tashak'a talumshe idanunta, saikuma ta bud'e ta sauke akan Bobo dake zaune abakin gado yana latsa laptop, k'afarsa d'aya ak'asa d'ayar kuma ya tank'washeta a gadon, sanye yake da kayan barci ruwan ganye mai turuwa, tana mamakin yanda yakeson latsa laptop da karatun jarida. Jin shiru bata ajiyeba, bakuma tayi maganaba yasashi d'agowa ya kalleta, shima baiyi maganaba saidai tura mata k'aramin tebir na gilas dayayi. Ganin haka yasa itama tad'ora batareda ta ce, "k'alaba. Bayan ta ajiye saikuma tayi tsaye takasa tafiya. Yana danna laptop d'insa yana shan shayi, tsawon minti 7 ita batayi maganaba shikuma ya shareta yanata aikinsa, yakula bazatace komaiba, kuma akwai magana abakinta, Dan haka shi ya daure ya ajiye NASA shan k'amshin ya ce, " kinada matsalane?. Kad'an ta kalleshi taga har yanzu idonsa nakan laptop d'in. gyara tsayuwarta tayi, muryartan nan mai kasheshi ta daki kunnensa, dama sonake naji yau ko lfy Baka dawo da wuriba?. Cak ya tsaya da abinda yakeyi, yad'ago fararen idanunsa ya sauke akanta, sanye take cikin dogon hijjabinta har k'asa, sa6anin d'azu daya Tatar da ita da kayan barci. Ahankali yasauke ajiyar zuciya, koba komai yaji dad'in kulawarta agareshi, cikin miryarnan tasa ya ce, "babu wata Marsala aikine yamin yawa a office. " okey saida safe." Harta kai k'ofa yana binta da kallo, yadaure ya ce, "incedai babu wata damuwa daga babyn taki?. Bata juyoba amma ta tsaya, Dan furucinsa na k'arshe yaymata dad'i, muryarta araunane ta ce, " a'a babu Marsala, saidai tata jiran dawowarka, harta gaji tayi barci..... Bata jira amsarsaba tafice. Ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe idanunsa, zuwa wani lokaci ya bud'e idon, d'an murmushi naga yayi Wanda bansan da liliba, saikuma yacigaba da aikinsa yana shan shayi. Itakam Rahma tana komawa d'aki tahaye gado ta kwanta abinta sai barci. ::::::::::••••••••••••::::::::: Washe gari Rahma ta tashi kamar yanda tasaba ta had'a break fast da gyaran gida, taima Nawal wanka itama tayi, kwalliya sosai taima yarinyar tai tsaf da ita, Dama ga ruwan k'yau d'an Asali, kan baby Nawal yasha gyara Dan jiya da yamma Rahma tayi mata kalba, kasancewar yau juma'a. Tana cikin saka mata janbaki yaturo k'ofar yashigo da sallama ciki ciki kamar Wanda akaima dole Da sauri Nawal ta hantsilo daga kujerar madubi danta hango daddynta ta madubi, oyoyo papa na tafad'a cike da farinciki tana rungumesa, shima d'aukarta yayi yad'aga sama yana dad'in "I luv u my child," yasumbaci kumatunta. Ta shagwa6e fuska, papa shine jiya kak'i ka dawo ko?, lah nadawo mana, saidai kinyi barci sannan kitanbayi momy kiji?. Nawal takalli Rahma dake kallonsu cike da sha'awa, wai haka momy papa yadawo jiya?, kai Rahma tad'aga mata tana murmushin daya kusan narkar da Bobo atsaye, hakane babyna yadawo kina barci. Nawal tasunbaci kumatun babanta da k'asunba ta kwanta luf tanata shek'in gara. Shikam hankalinsa nakan Rahma yana mata wannan munafikin kallon NASA k'asa k'asa. Talura dashi tsaf dan haka tatsargu, rissinawa tayi ta ce, "INA kwana?." Lfy, yafad'a cike da basarwa shi adole ba ita yake kalloba. Rahma ta d'an ta 6e baki, dukda ta fahimci salon amsa gaisuwarsa kenan...... Muryarsa ta katse mata tunani, kushirya idan mungama break gida zamu wuce, Dan duk juma'a a can kowa yake yini. Ahankali

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});