Chapter 25
Chapter 25
dama mata, dallah malama fitarmin ad'aki, kuma karna sake ganin k'afarki ad'akina. Ran Rahma ya6aci sosai ganin yanda yake cimata mutunci akan hoto, Wanda inyanzu yaso zaikai amaida gilas d'in daya fashe, haka tataka k'afa tabar d'akin tana kuka, tanazuwa tazube akan gado, ga azabar da k'afarta take mata amma bata kulaba, sai kuka maicin rai data saki. Duk abinnan yake faruwa Nawal tana can baya tana wasa, Rahma taturata wajene dantabarta tayi aiki, batason surutu. Bobo kam tana fita yadurkushe agaban hoton, d'agosa yayi yana gogewa tamkar zai fasa kuka, muryarsa na Rawa ya ce, "kiyi hak'uri Ni'imana bada sanina tayiba, ALLAH ya gafarta miki ya yafe miki kinji. Nawal tashiga d'akin Rahma tana kwala mata kira momy! Momy!!, tak'arasa cikin d'akin da murnarta, amma ganin jini ahanyar sai jikinta kuma yay sanyi, tak'arasa har bakin gadon tana kallon k'afar Rahma da gilas ke jiki ga jini yanata zuba ak'asan wajen. Fitowa tayi da gudu tanufi d'akin Papan ta, har yanzu yana gaban Hoton adurk'ushe, papa papa zokaga k'afar momy jini yanata zuba dayawan tsiya. d'agowa yayi yana kallonta, yanda tabirkice shima sai jikinsa yay sanyi, mik'ewa yayi suka nufi d'akin Rahma d'in, gsky shima abin yabashi tsoro ganin jinin dad'an yawa, ga gilas babba kafe ak'afarta, tana kwance rubda ciki tana darzar kuka. Tsugunnawa yayi Kusada k'afar yakama gilas d'in zai cire tasaki wata k'ara wadda tasaka Nawal fashewa da kuka itama, ga gilas d'in yakafe dayawa, ganin karya k'ara jimata ciwo yasa yamik'e dasauri yaje d'akinsa yad'akko key d'in mota. Dawowa yayi ya ce, " tashi muje asibiti acire miki wannan kwalban. Banza tayi masa tacigaba da kukanta, wani haushi yak'ara turnik'eshi, baisan lokacin daya sungumetaba yay waje da itaba, Nawal nabinsa abaya, Nawal tabud'e masa k'ofar motar yasakata aciki, suma suka shiga sai asibiti......... _kuyi hak'uri da wannan yau kaina namin ciwo._ *_luv u oll my fan's_* *_(((S)))..........2017_* [11/12, 2:51 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* 4⃣1⃣ Asibitin ya sulaiman sukaje, ALLAH yasosu sun tarar dashi. Aiko ansha fama wajen cire gilas d'in nanan, Rahma tasha kuka dukta fita hayyacinta, ga k'afar harta d'an kunbura. Shikansa Bobo ya tausaya mata, saiyanzu yake ganin abinda yay mata bai k'yautaba, to amma idan yatuna miyakai hannunta wajen hoton saiyaji ransa ya 6aci. Da hakadai aka kammala, ya Sulaiman yamata allurai tad'an samu nutsuwa. Bayan an kammala bobo ya ce, "ya yarinyar nan kuwa?. Jikinta kam saidai muce alhmdllh, ammafa yakamata asan iyayen yarinyar nan Abdulmaleek, gashi kace zaku fara shiri'a ranar talata, kasanfa Alh sunusi dala mutumne mai had'arin gsk, sarai zai iya bincike akan yarinyar, kuma zai iya aikata kimai Dan ganin d'ansa ya ku6ta. Hakane Yaya, amma inata iya k'ok'arina wajen Neman iyayenta, saidai kutayamu da addu'a kawai. To ALLAH ya taimaka. Amin dai, bari mubiya muganta saimu wuce gida. Okey, kardai kamanta kusiyi maganin. Babu damuwa, k'arasawa yay inda Rahma take fuskarsa babu walwa, yakama hannunta ta sakko. Ya Sulaiman dake kallonsu ya ce, " saidaifa kad'auketa kamar d'azu, Dan babu yanda za'ayi ta iya taka wannan k'afar. K'ara 6ata rai yayi, kamar bazaiyi maganaba, saikuma ya ce, "Yaya ba ancire ba?, eh ancire, amma karfa manta yanda gurin yake a yanzu, idanmma kunje gida ad'an gasa k'afar da ruwan zafi. Baice komaiba ya d'auketa, saiwani kauda kai yake daga saitin fuskarta, itama saita runtse ido Dan bata son ganinsa. d'akin da yarinyar nan take yakaita, yadireta saman kujerar gaban gadon, lahh Muheebat! kece?, Rahma tafad'a tana kallon yarinyar. Itama tashi tayi zaune tana dariya Dan ganin Rahma. Bobo ya ce, " kinsanta ne?. Eh nasanta, K'anwar direban muce idris, dama sunata nemanta tun tuni wlhy. Ajiyar zuciya bobo ya sauke ya ce, "Alhmdllh, yaciro wayarsa yakira Ya Sulaiman, babu dad'ewa kuwa ya iso, shima yaji dad'i sosai dajin labarin. Sun ajiye magana akan anjima zasuje gidansu Muheebat, dukda bata iya magana to tanajin abinda suke fad'a, Dan haka taita murmushi. Bobo Yakuma d'aukar Rahma zuwa Mota, daganan sukayi gida, motar tsit babu mai magana kamar wasu kurame, Bobo sai shan k'amshi yakeyi, itama ganin haka saita d'auke kanta, dama can suka baro Nawal zatabi ya Sulaiman gidansa. Koda suka shiga harabar gidan saiya bud'e motar yay tafiyarsa ciki yabarta. Rahma tayi wata dariya azuciyarta ta ce, " kama dawo wlhy, dan babu inda zan motsa. Aiko tayi zamanta amotar, shikam haryaje k'ofar falon saiyaji babu motsinta abayansa Dan haka ya waiga, can ya hangota cikin mota ko motsawa batayiba, afili ya ce, "wai mi waccan abar take nufi da nine?, koni bawantane dazanta d'aukarta ina ajiyewa mtsooow, yak'arashr maganar dajan tsaki. Komawa yayi wajenta sai wani d'aurewa yakeyi, Rahma ta hangoshi yana tahowa, tayi murmushin mugunta tana fad'in kadaiji dashi. Bemata maganaba yabud'e motar ya d'auketa, itako ta lumshe idonta kamar mai barci, haushine yak'ara turnuk'e zuciyar bobo, gani yake tana k'ara langya6ewa ne kawai. Koda yadireta a gadon bai kalletaba yajuya ya fita. Ita kuma taimasa gwalo😜, wai dole dai ad'auketa. lol. Tana nan zaune har kusan minti talatin, harta fara tunanin yanda zata fita taci abinci Dan yunwa takeji sosai, tayunk'ura zata tashi taji wani azababben zafi, danhaka takoma ta zauna, wai miyasama tabar Nawal tabi ya Sulaiman ne?, yanzu da tananan ai data rage mata wani abun.........bata rufe bakiba taji anturo k'ofar. Kamshinsane ya tababbatar mata dashine, Dan haka tak'i d'agowa danko sallama bataji yayiba. Tire yadire ak'asa na kayan break, Rahma tayi kamar bata ganshiba, shima ko kallo bata isheshiba yad'akko kofin tee ya mik'a mata. Kamar bazata amsaba saikuma ta amsa Dan ganin yayi tamau da fuska kamar bai ta6a dariyaba, yamik'o mata filet d'in soyayyar doya. Saman kujerar dake d'akin Yakoma ya zauna yana danna waya, ganin haka yasa tadake taci abincinta Dan yunwa takeji sosai. k'asa² yake kallonta, aransa ya ce, "k'aryar ciwo kikeyi yarinya, tumda har kika iya share filet guda na doya, Rahma ta kalleshi ta ce, " nagama. Banza yay mata yacigaba da danna wayar, saida ya mula Dan Kansa sannan yataso yazauna saman durowar gefen gadon, maganin yacira yabata. Tofa anan akeyinta, Rahma tayi kwalkwal da ido zatayi kuka, tsak'i yayi yana harararta, idan bazaki amsaba kibarsa kece zakisha wahalarki ke kad'ai wlhy, danni yanzuma zanbar miki gidan. Yanda yake zabga ruwan masifa yasa ta k'ar6a, saidai tana hawaye tana sha, idan tasha d'aya saitayi kamar zatayi amai saikuma ta daure, shidai yana kallonta ta gefen idonsa Dan yacigaba da latsa waya, hakadai tadaure tasha maganin. Tashi yayi ya d'auki kwanukan yafita dashi, babu dad'ewa yadawo da k'aramar roba da ruwan zafi aciki, sai k'aramin tawul. Baiyimata maganaba yajawo d'ank'armin tebir na gilas dake kusada kujera ya zauna, Rahma ta ce, "kasada aranta. K'afarta yad'auka yad'ora saman stool na madubi, itadai ikon ALLAH take kallo kawai. Dukda yaga kallon datake masa bai kulaba yafara aikinsa batareda yabi takantaba, yasaka tawul d'in aruwan zafin yad'an yamatse, daganin yanda yake matsar tawul d'in kasan ruwan da zafi, amma Dan bak'ar mugunta ahaka ya nanama Rahma akan k'afar, wani wahalallen ihu tasaki, yay saurin rik'e k'afar yana harararta, kawai saitaji hawaye nabin kumatunta. Raguwar banza yafad'a afili. Itama ta ce, " ruwanfa da zafi wlhy, yanda tayi maganar ashagwa6e saiya tsaya yana kallon bakinta, ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83