Chapter 55
Chapter 55
irinnasa. shikam kallonsa yamaida akansu khairiyya ya ce, "ku bakuda hankali Baku iya sallamabane idan zaku shiga waje?. Yaya wlhy bamusan kana nanba munzata ita kad'aice Dan ALLAH kayi hak'uri bazamu sakeba. Le6ensa yacije yama rasa mizaice musu, tsaki kawai yayi dallah kutashimin kai shashashu, haka za a kaiku gidan miji kunama mutane shirme. Da sauri sukayi waje, suna fita khursiyya tarufe bakinta da hannu ta shek'e da dariya, itama khairiyya dariyar tasaka, suka tafa suna cigaba da dariyarsu, saidai sukayi mai isarsu sannan khairiyya ta ce, " kai ya bobo an iya mazuran rashin gsky, nakulafa yama rasa mizaice manane shine ya koromu, dariya suka kama tuntsurewa da ita. Khursiyya ta ce, "yar uwa yau naga ruwan soyayya, dama irinsu ya Abdulmaleek akwai iya soyayya, amma akwai dai mazuran tsiya, badan karyaci ubanaba wlhy saina koma naga mi akeyi yanzu. Idanu khairiyya tazaro ta ce, " tabd'i wlhy badaniba, kingama tafiyata baza'a kaini gidan miji da karyayyar k'afaba, haka kawai su sunacin tasu soyayyar da allura ni akaima mijina jiyya yakasa nunamin. Rahma dake bayansu ta ce, "ALLAH ya shiryaku wlhy. Da sauri suka juyo ganin Rahma yasasu nufowa gareta harsuna 'Yar rigerigen tambayarta ya aikayi tafito?. Hararar wasa tamusu ta ce, saiya fito yaritsaku wlhy. Da sauri suka bar wajen itakuma tabi bayansu tana murmushi. Tundaga wannan lokacin Rahma bata sake bari sun had'a hanya da bobo ba har dare lokacin tafiyarsu yayi. Bansan miya faruba Ammi tace safna tayi zamanta anan danta tayata wasu ayyukan. Ina kallon bobo yayi wani murmushi mugunta, Rahma dai batace komaiba, Safna kam jitayi tamkar tafasa ihu Dan Bak'inciki. Rahma ta ce, "ina Nawal mutafi. Kinga d'iyata kuyi tafiyarku tunda weekend za'a shiga kuma dukan yaran nan za'a barsu. Jiki a sanyaye Rahma ta ce, " to Ammi saida safe. ALLAH yakaimu d'iyata kinji. Tunda suka fita bobo yake wata 'Yar dariyar mugunta k'asa² itadai Rahma batace dashi k'alaba saidai jikinta duk yayi sanyi. Da kansa yabud'e mata motar tashiga, shima yazagaya yashiga, har suka fice daga gidan baikuma cewa k'alaba, bayan yahau babban titi yana tuk'i ahankali yad'an juyo ya kalleta ya ce, "matsoraciya har an hau network d'in tsoronne?. Shiru tamasa kamar batajiba, murmushi yayi yasaka hannunsa d'aya yakamo nata yana murzawa, d'ayan kuma yana tuk'i dashi, batace masa komaiba bakuma ta hanashi abinda yakeyiba. Wai baza'amin maganaba ne my cute?. Idanunta tad'ago ta kalleshi ganin hankalinsa nakan titi yasa takauda kai, miye kuma kike kallona?, bobo yay maganar har yanzu idanunsa atiti. Nifa ban kallekaba, Rahma tafad'ad'a kamar zatayi kuka. Humyim yarinya zaki maganane, ainasan hanyar dazansaki maganar bara mu Isa gida dai kigani. Gaban Rahma ne yafad'i, saikawai hawaye yafarabin kumatunta, aranta ta ce, " wlhy ka k'aramin irinna jiya mutuwa zanyi. Karya kwana yayi yashiga layin gidansu, anguwar shiru babu kowa sai haushin karnuka, yay hon mai gadi yabud'e masa gate bayan sun gaisa yashige ciki damotar. Yana tsayawa ko kashewa bata tsaya yayiba tayi wuf tafice, sauri sauri gudu gudu tashige ciki bayan tabud'e k'ofar falon, kafin yak'araso harta shige d'aki ta kulle kanta. Tabama bobo dariya danhaka yashige d'akinsa yana wata 'Yar dariya. Tana Shiga d'akin tadafe k'irji tanama kanta dariya, wata zuciyarta ta ce, "kai Rahma akwai tsoro?, yo badole naji tsoroba, wlhy nabari mutuminnan idani zaiyi, afili tayi maganar Tanana kanta dariya. Wanka ta shiga bayan tagama ta d'auro alwala tafito, shirin barci tayi sannan tahau abin sallah tayi shafa'i da wutiri, tayi addu'ointa tamik'e, aranta tana fad'in yaudai ba'a nemi shayin k'addaraba. Gado tahaye ta kwanta hankalinta kwance taja bargo ta lullu6a. Shimadai bobo yana Shiga d'akinsa wankan yashiga, yay shirin barci tsaf, duk abinda yakasance al'adarsa yagudamar sannan yajawo laptop akahau aikin k'a ida. Har wajen k'arfe d'aya yana gaban laptop sai biyu saura yad'ago yana kallon agogon dake d'akin, mik'a yayi tareda hamma, yarufe laptop d'in yamik'e, dirowar gefen gado yabud'e ya d'au key da wayoyinsa yakashe fitilar d'akin yafice. d'akin Rahma yanufa yasandai yanzu tayi barci, ahankali yabud'e k'ofar yashiga yamaida yarufe, kallonta yayi kwance akan gado ta k'udindine abargo, aransa ya ce, " yarinyar nan sai abarki, gakida bargo na gsky mai laushi kin 6uge da shiga bargon bogi. Wayoyinsa yazube adurowar gefen gadon yahau yakwanta ahankali, bargon ya janye yashige ciki tareda rungumeta a faffad'an k'irjinsa mai yalwar k'amshin turare. Ahankali yasauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, Alhmdllh yafad'a azuciyarsa. Rahma kam dabatasan yanayiba takuma gyara kwanciyarta sosai a k'irjinsa, ahankali tarink'a sauke numfashi mai d'umi ak'irjinnasa. K'ara lumshe idanu yayi yana mai lashe la66ansa da k'yar ya iya control d'in Kansa yay barci. _washe gari_ Da asuba Rahma tariga bobo farkawa, jinta kamar ajikin wani Abu yasakata saurin bud'e idanu, ganin bobo yasakata zare k'yawawan idanunta, aranta ta ce, "to yaushe yashigone?, mutum tamkar aljani?, k'yak'yk'yawar fuskarsa tazubama idanu, aranta ta ce, " mutumin nan akwai sirrin k'yau, babu Abu mafi d'aukar hankalinta ajikin bobo kamar Sajensa, tanason sajensa sosai danya k'awata sirrin k'yawun fuskarta, ahankali talumshe idanunta tareda kai hannu bisa k'yakykyawar fuskarsa tana shafa sajensa daya kwanta luf luf yanata tashin k'amshi mai dad'i kamar yanzun yasaka masa turaren. Tunda tafara shafa masa fuska yafarka, ta k'asan ido yake kallonta, aransa ya ce, "ALLAH yabani magulmaciyar mata, anasona ana kaiwa kasuwa, Rahma tajanye hannunta tana murmushi Dan duk zatonta bai tashiba, k'ok'arin zare jikinta tafara daga NASA, jin haka yasa bobo k'ara rungumota, acikin kunnenta ya ce, " guduwa zakiyi kibarni?. Shiru tayi wai ita a adole barci takeyi, ya ce, "humm nizakima pretending? Bayan kingama shafemin fuska kina shauk'i?. Rahma ta cusa kanta ak'irjinsa tana dariya k'asa k'asa, shima dariyar yayi ya ce, " oh ni dama matana ta iya gulmar soyayya saikace matar k'auye?. Itadai luf tayi ajikinsa Dan kunya. Jin ana kiran assalatu yasashi yunk'urawa yatashi da ita ajikinsa, to madam pretending tashi muyi sallah. Zame jikinta tayi daga nasa batareda tad'ago ta kalleshiba, shimadai mik'ewa tayi yashiga bayinta ya d'auro alwala, Inda take ya iso yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e saboda alwala, sunkuyowa yayi yasumbaci kumatunta sannan yafice yana fad'in saina dawo. Batace komaiba saidai tasaci kallonsa tagefen ido tana murmushi, yana fita tatashi itama Dan d'auro alwala. Saida yaje d'akinsa ya canja kayan barcinsa zuwa doguwar Riga sannan yafice masallaci. Saida gari yayi haske sannan bobo yadawo, lokacin Rahma ma tana zaune akan sallaya tana addu'a bayan ta k'arasa karatun alkur'ani. Zama yayi suka shafa addu'ar tare. Kan Rahma ak'asa ta ce, ''ina kwana?." Bazan amsaba saikin kalleni. Murmushi tayi tareda rufe idanunta da tafin hannu, kamata yayi yamik'ar tareda zare hijjabin sannan yajata suka zauna a bakin gadon, my cute wai ita wannan kunyar bazata raguba haka?, nafa rage kusan 60% acikinta amma ank'i nunamin hakan. Murmushi tayi kawai batareda tace komaiba, ya ce, "idan kinaso nakaiki gidan Appa yau saikin kalleni, yafad'a yana tsura mata mayun idanunsa. Ahankali tad'ago k'yawawan idanunta masu kasheshi ta sauke akansa, kallon ido cikin ido sukema juna, suduka sunshagala cikin shauk'in so, bobo yad'an lumshe idanunsa yabud'e ahankali, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, " ina k'aunarki dayawa Rahma, tabbas da ubangiji bai sauya al'amuraba danayi asarar rashin kasancewarki matata, ALLAH na gode maka dakamin wannan k'yauta. Rahma talumshe fararen idanunta, ta ce, "nice na cancanci gidema ALLAH ya *_Abdulmaleek_*, kaid'in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83