Chapter 4
Chapter 4
yanke aka k'ara kira. Daurewa yayi ya d'auka suka gaisa, AA Hamshak'i wai ya akayine?, kacemin kafito gida amma najika shiru. Sorry Kamal ina nan zuwa, wlhy wani abune ya rik'rni ahanya, amma plz kabani minti talatin zuwa arba'in zan iso. Okey saina ganka. A can kuwa bobo nabarin wajen police suka zo, mutane suka sanar dasu wani ya d'auki yarinyar zuwa asibiti. Wane asibin ne?, wani d'ansanda ya tambaya fuska atamke. Muma bamu saniba wlhy, amma antafi damai shagonnan, suka nuna shagon dake kusadasu. d'ansandan baice komaiba yashiga mota suka juya. Gulma mutanen gurin suka fara da zagin 'yan sandan, wai sai yanzu suka gadamar zuwa, bayan tun d'azu aka kirasu. Wani ya ce, "bar munafukai malam aii k'asarnan munga takanmu, buharine kawai ke k'aunar talaka, (ALLAH dai ya k'ara masa lfy). Amin ya rabbi Garzali. +++++++++++++ Safna tafito sanye cikin atamfa Riga da siket, sunmata d'am kamar zata fashe. Rahma ta kalleta ta girgiza kai, wannan lamari na 6ata mata rai, ita bataga wayewaba ga mace mai saka suturar dake fidda jiki, shiyyasa fad'e yaketa k'ara yawa aduniya, to matan basusan darajar jikinsuba, (suyita fiddo jiki tamkar akuyoyi da sunan wayewa)......... Me wait lfy kike kallona?, karfa ki cinyeni wlhy. Rahma takauda kai saga kallonta, ta ce, " aikinsan Nina mayya bace. Da sauri safna takai mata duka, to ubanwaye mayen?. Rahma ta kauce tana dariya, maida wuk'ar ta hannun damar Abba, Dan ALLAH zanbiki makarantar wlhy zaman gidannan ya isheni. Safna ta harareta tozoki hau kaina uwata. A'a ALLAH yabaki hak'uri, yi tafiyarki zanje gidan yaa Munir nama taya aunty Naja'atu aiki. Yafimiki sauk'i, dama da 'yan aiki kike kama aii, safna tafad'a tana ficewa. Baki Rahma ta ta6e tareda Jan tsaki. Ummi tafito tana fad'in kekuma lfy?. Lfy lay ummi nida aunty Safna ne. Ina Safna d'in?. Tafita makaranta. Shine yau ko sallama babu?, dariya Rahma tayi ta ce, "haryanzu aljanun masifar nasu saukaba. Ummi batace komaiba tashige kicin. +++++++++++++ Asibiti kam lamura saidai addu'a bak'aramar mugunta akaima yarinyarba, amma cikin ikon ALLAH yaa sulaiman yayi nasarar ceto ranta. Bak'aramin lokaci ya6ataba kafin yafito, zuwa yanzu bobo na tsaye jingine da bango ya hard'e hannuwansa biyu ak'irji, k'afarsa d'aya dogare a bango fuskarnan d'aure tamau. Ya sulaima yafito yana shere zufa, da sauri Bobo ya taresa, Yaya ya jikin nata??. Alhmdllh. ya sulaiman yafad'a, yaja hannun Bobo suka shiga office d'insa. Koda ya zaunar dashi saiya bude firij yad'akko fresh milk ya tsiyaya a kofi yamik'ama Bobo. Bobo ya ce, "ya.... Hannu ya d'aga masa, kaga k'ar6a kasha kasamu nutsuwa, nasan ko karyawa bakayiba kafito. Ajiyar zuciya Bobo yayi, yakar6i kofin yasa abaki, ahankali yakesha harya shanye tas. Cikin zolaya ya sulaiman ya ce, " Bobon Ammi damadai yunwa kakeji, ko a k'ara?. Murmushi yayi batareda yace komaiba, ya girgiza kai. Ya Sulaiman ya zauna yana dariya, saida yayi rubuce2 sannan yad'ago ya kalli k'aninnasa, Abdulmalik ina kasamo yarinyarnan?. Ajiyar zuciya Bobo ya sauke shima yayan nasa yake kallo, ya ce, ''Yaya wlhy abakin titi..... Nandai yakwashe komai yasanar dashi. Girgiza kai ya sulaiman yayi, ya ce, ''ALLAH ya saka mata, amma yanzu yakamata musan iyayenta kafin ad'au mataki, sannan ina yaron dakace kunzo tare?. Yana nan awaje. Wani Abu ya sulaiman ya danna, saiga Nos tazo, ya ce, "akwai wani saurayi anan waje shigomin dashi. OK sir............. *_kuyi hak'uri ina muku typing bakamar aunty billy ba, wlhy akwai wahala, writers suna k'ok'ari gsky, ALLAH dai ya biyasu._*🙏🏻 *_" luv u aunty bilyn Abdul"_* [11/12, 2:15 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻 ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _{Bobo}_ _Story & editin_ *_Aunty Bilyn Abdul_* ✍🏿 _Written_ *_Marak'isiyya_* _hak'in mallaka_ *_Aunty Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Bily giro_* 9⃣&🔟 Assalamu alaikum. Wa'alaikassalam yaa sulaima da bobo suka amsama saurayin. Gurin zama yaa sulaiman ya nuna masa, bayan ya zauna yabasa hannu sukayi musabaha. Ya sulaiman ya ce, "d'an uwa ance awajenku aka samu yarinyarnan ko?.. Eh anan akazo aka yardata wajen misalin k'arfe 6:44am, fitowa ta kenan zan bud'e shagona naga wata jar mota ta tsaya agurin, nasan su basu ganniba nida abokina Nura, Dan saida suka wawwaiga sukaga babu mai kallonsu sannan aka turota waje. Bobo ya cije le6ensa zuciyarsa na k'ara zafi. Ya sulaiman ya jinjina kai, Yakuma fad'in to kunsanar da police?. Eh suna barin wajen muka kira 'yan sanda, amma har bawan ALLAH nan yazo ya d'auketa basu zoba. Ya sulaiman ya sauke numfashi, babu damuwa ayanzu nasanar da wani d'an sanda dan kes d'in dolene police sushiga, namata abinda duk yadace, kuma narubuta bayanai akan komai....... Kwankwasa k'ofarne yahana yaa sulaiman cigaba da magana, wata nos tashigo tana sanar dashi wani police nason ganinsa. Shigo dashi mana ya sulaiman yafad'a. Bayan d'an sandan yashigo shida wani suka gaisa dasu bobo sannan sukayi musu bayani akan komai. Har d'akin da yarinyar take aka kaisu, bobo tamkar yay kuka danganin yarinyar, shidama haka yake da tausayi dukda kasancewarsa masifaffe. Bayan sun kammala komai 'yan sandan suka tafi, shima saurayinnan yatafi akan zasu sake nemansa. Ya ce, "insha ALLAHU duk sanda sukazo zai basu had'in kai. Godiya sukai masa yatafi, bobo yay masa alkairi. Ya sulaiman ya kalli bobo, Abdulmalik kaima yakamata katafi gida ka canja kayannan duk sun 6aci da jini. Sai asannan yakula, yad'anyi tsaki wlhy yaya bamma kulaba, bari naje wajen Br kamal Dan yana jirana, idan muka gama saina koma gidan. Dadai kafara zuwa ka canja kayan tukunna. To yaya bari naje, saina dawo. Okey saika dawo. Saida sukad'an rungume juna sannan sukai musabaha yatafi. +++++++++++++++++ Rahma tafito sanye cikin dogon hijjab har k'asa yake ja, hijjabin mai hannune Dan haka hannunta rik'e da fos, sallama tayima ummi sannan tafito. Ta wawwaiga bataga idiris diraiba ba, d'an tsaki taja ta k'arasa wajen mai gadinsu, rissinawa tayi ta gaisheahi. Ya amsa cike da fara'a, yana k'aunar yarinyarnan saboda hankalinta da girmama nagaba da ita, halinta ya banbanta da yayarta sosai..... Rahma tak'atse masa tunani da fad'in baba ina Idris!. aiko d'iyata Idris yaje gida yanzu babu dad'ewa, kinsan suna cikin tashin hankalin 6atan k'anwarsu tun jiya da yamma. K'anwarsu kuma?, 6ata tayi?. Wlhy kuwa haka yake gayamin d'azu, wai tunjiya bata dawoba daga aikenta. Tofa ALLAH yabayyanata, Toni bari naje na hau adaidaita. diyata dakanki?, toki tuk'a kanki mana. Murmushi tayi ta ce, "A'a baba, Abba ya hanani tuk'i." ALLAH sarki 'Yar albarka, aii haka akeson mutum yaringa bin maganar iyayensa, ALLAH yay miki albarka, yabaki miji nagari. Murmushi Rahma tayi, ahankali tace ngd baba saina dawo. To adawo lfy. Rahma tafito daga gida, tad'an wawwaiga anguwar babu mutane sosai, sai jefi jefi, dakuma motoci dake fitowa daga gidaje inaga masu Fita aikine da kasuwa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan tafara tafiya da addu'ar ALLAH yasa tasamu adaidaita da wuri, Dan tsakaninsu da titi da nisa. Tad'anyi tafiya kanta ak'asa, jitai ance a'a Rahma sai Ina?. Ad'an tsorace tad'ago takalli inda aka ambaci sunan nata, tayi murmushi lah ya kamal kaine.?. Nine Rahma ykk?. Lfy lau yaya, lfy naganka anan?. Wlhy lfy k'alau wani abokina nake jira, amma shiru bai zoba shine naked'an shan hantsi anan. Ayya, yasu momy da aunty Ameera. Lfy lay suke, bazaki Shigabane?. A'a yaya gidan ya Muneer zanje wlhy ka gaidaminsu. Zasuji, to amma ina direbanku kika fito ak'afa. Hummm
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83