Chapter 2
Chapter 2
zuwa cikin gida, kansa yagirgiza yana fad'in ALLAH ya shiryeki baby. (nace amin). Bayan yakashe motar yakwashi wayoyinsa shima yay ciki. Ammi dake zaune Nawal nakusada ita ta kwa6e fuska zatayi kuka, ta amsama bobo sallamarsa. Yak'araso cikin falon yana kallon Nawal, kekuma lfy daga dawowarmu?. Ammi tasauke ajiyar zuciya ta ce, " maganar kullumce dai takawo rigimar. Shiru yayi baice komaiba. Ammi takalli Nawal dahar tafara hawaye ta ce, "haba tagidan Appa kiyi hak'uri insha ALLAHU kinkusa ganin momynki kinji. Da sauri bobo yad'ago yana kallon ammi, k'irjinsa sai harbawa yake da k'arfi, yakasa cewa komai. Ammi takauda kai, ranta a6ace ta ce, " nagaji da ganin kukan yarinyarnan wlhy, amma babu komai bari Appanku yadawo, zand'auki mataki. Hannun Nawal takama suka haura sama. Bobo tamkar zai fasa ihu haka yakeji, yarintse idanu zuciyarsa na zafi, afili ya ce, "baby miyasa kikeson sakani a matsalane?. Ganin babu maibashi amsa yamik'e yanufi d'akinsa. *_Wanene Bobo_* Abdulmalik d'ane ga Alh Aliyu Abdulmalik Hamshak'i. d'an siyasa sananne wad'anda suke gwagwar Maya da ilimi dakuma nemawa talakawa 'yancinsu, matarsa d'aya Haj. Zahura (Ammi). Yaransu shidda maza hud'u mata biyu. Is'haq shine babba, yanada mata d'aya da yara hud'u, sai Sulaiman, shima yaransa uku da mata d'aya, sai Hamza matarsa d'aya shima da yara biyu, sai Abdulmalik (matarsa ta rasu) yarinyarsa d'aya, sai 'yan biyu duk mata basuyi aureba. ALLAH ya azurta Alh Aliyu Hamshak'i da yara maza masu kwazo da himma, yaa is'haq ma'aikacine na banki, yaa Sulaiman kuwa likitane, sai yaa hamza lecture, sai Abdulmalik (bobo) cikakken lauya mai zaman kansa. Kansu ahad'e yake, idan kagansu saika d'auka abokaine musamman ma yaa hamza da Abdulmalik, komai zasuyi saida shawarar junansu. *_Abdulmalik_* Mutumne mai zafi da sauk'i, gaba d'aya 'yan uwansa yafisu fad'a, saidai zasuzo daidai da ya is'haq (Dan shima mafad'acine). Abdulmalik mutumne dabayason raini ko kad'an, baya wasa da mutane, baizama dolema kuzauna har kurabu kaga dariyarsaba, kullum cikin d'aurewa yake, amma yanada son jama'a sosai. Abdulmalik bobo, yasamo sunan bobone tun yana k'arami, kasancewarsa mayen shan Bobo sai 'yan uwansa suke kiransa da bobo, ahankali sunan yay tasiri kowa Yakoma cemasa bobo, bayan ya girma saiya zama bobo na gsky saboda gayunsa ga k'yau ga kud'i ga ilimi, komaidai zam zam. Bayan ya kammala karatunsa yafara aiki iyayesu sukace saura aure. Yay tsalle yadire bashida budurwa, wannan yasa Appa yanema masa auren d'iyar k'anwar Ammi mai suna Ni'ima. Da farko baya sonta ko kad'an, amma k'yawawan hali irin na Ni'ima yajanye hankalinsa harya tsunduma a k'aunarta. Shekararsu biyu da aure ta haihu mace, wadda taci sunan Ammi, suna kiranta Nawal, shekarar Nawal d'aya Ni'ima takuma samun ciki, amma wajen haihuwa ALLAH yay mata rasuwa itada abinda ke cikinta. Bobo yashiga rud'ani Dan saida aka had'a da addu'a sannan yadawo daidai. Tundaga nan baisake kallon wata mace da sunan so ba, damashi matan bawani damunsa sukaiba. Bobo yanada k'yau daidai gwargwado, gashi d'an gayu, akwai tsafta da iya d'aukar wanka, dolene mace mai lfy taga bobo ta k'yasa, kullum cikin k'amshi yake. Shiyyasa Madeena ta k'yasa. (To aunty bily dai ta ce, "ki kama kanki Dan bama kulaki zaiyiba, danshi aharkar mata ba gwani baneπ). Shekarar Ni'ima 5 kenan da rasuwa amma bobo yak'i k'ara aure, iyayen sunata fama dashi amma yak'i sunata fama saidai yace zaiyi amma yak'iyi. Kullum zancen Nawal akaita gurin momynta, haka take damunsu Ammi da Appa hardashi dadyn Nata, itadai tanaso taga momynta, kullum zancen kenan. Abin yana damun yayyensa da iyayensa, shikam ko'a kwalar rigarsa, harkar gabansa kawai yakeyi. Wannan kenan. *_Mundawo labari_*......... *_{Aunty bilyn Abdul na gaisheku masoyaππ.}_* [11/12, 2:10 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ» β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£ _{Bobo}_ _Story & editin_ *_Aunty Bilyn Abdul_* βπΏ _Written_ *_Marak'isiyya_* _hak'in mallaka_ *_Aunty Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Bily giro_* 5β£&6β£ ........Safna tadanna hon afusace, da sauri maigadinsu yazo yabud'e mata get, ta danna hancin motarta cikin gidan, tana kashe motar tasuri jakarta da wayoyinta zuwa cikin gida. Wani wawan tsaki tasaki Dan ganin Rahma k'anwarsu kwance akan cinyar ummi. Daga Ummi har Rahma baki suka saki suna kallonta. Ummi ta ce, "kekuma lfy daga shigiwa zakiyi mana tsaki?, wai Safna ban hanaki halinnanba ne?. Baki ta turo gaba tana Harar Rahma, haba Ummi ALLAH wannan abun kunyane, wannan k'atuwar yarinyar shrkara 17 haryanzu bataida halin yaraba, aiiko jafar d'in ya Shaheed baya wannan ta6arar. Rahma ta girgiza kai danjin akanta yayar tata take tada jijiyar wuya, tarasa miyasa basa shan inuwa d'aya da 'Yar uwarta, (ita aganinta abin yafara wuce fad'an sako da sako), afili kuma sai ta ce, " aunty Safna miyayi zafi shiba wutaba, zauna ki huta Dan ALLAH....... Duka takaima Rahma ummi ta kare, Safna kishiga hankalinki danifa, uwarmi tamiki daga shigowa?. Cikin huci ta ce, "ummi kinajinfa maganar datake fad'amin, ALLAH yarinyarnan ta rainani, zan koya miki hankali kwanannan wlhy. Ummi ta tamke fuska tana nunama safna hanya, kinga tashimin anan. Ran safna a6ace tabar wajen tanufi d'akinsu tana mita. Rahma kam ta sauke ajiyar zuciya tana k'ara gyara kwanciyarta. Ummi ma kai ta girgiza ALLAH ya shiryaki Safna tafad'a tana shafa kan Rahma. Safna tacire kayanta tanata masifa harta shiga wanka, (nikam mamaki take bani, Dan banga abin fad'aba anan). Rahma tanason shiga d'akinsu tayi wanka tana tsoron masifar Safna, Dan tasan wlhy bata bartaba, k'ilama yau kwana zatayi bala inta da mitar tsiyarta. d'akin umminsu tanufa dantayi wankanta kawai, yafi sauk'i. +++++++++++++++ Bobo yana kwance ad'akinsa sai juye2 yakeyi, barci yakesonyi amma yak'i d'aukarsa, maganar Ammi ce kemasa yawo akwakwalwa. Yasan Ammi sairai babu sauk'ice, indai Abu ya6ata mata rai saita d'auki mataki, shikam yana tsoron zancennan yaje kunnen Appansu, yad'an cije le6e yana sauke numfashi, tund'azu soyake yafita amma yana shakkar had'uwa da Appa. Yasan fita tazame masa tilas Dan dole zasu had'u wajen cin abinci....... Bai rufe bakiba aka buga k'ofar, batarda ya d'agoba ya ce, "ashigo. Khairiyyace k'anwarsa, cikeda da tsoro ta ce, " yaya kazo wai aci abinci. Hannu yad'aga mata kawai, bata gane nufinsaba Dan haka ta ce, "ka k'oshi kuma yaa Bobo!?. Harara ya watso mata sannan yamik'e, da sauri tayi waje, shikuma yad'auki doguwar riga fara yazura yafito. Kowa ya hallara shikad'ai ake jira, rissinawa yayi yagaida Appa da Ammi sannan yazauna. Khursiyya ta ce, " yaya ina yini, harara ya watsa mata, ya ce, "k d'azu dasafe miya hanaki wankemin bayi?. Kanta ak'asa ta ce, " wlhy yaya ina uzirin makarantane, dakuma nadawo na manta. Tsaki yaja kawai baisake cewa komaiva. Ammi tazubama Appa abinci, tasakama kanta, kairiyya kuma tasakama bobo shima, suma suka zuba. Nawal tana kusada Appa. Suna cikin cin abinci kamar antsikari Nawal ta ce, "aunty khursiyya. Na'am Nawal miya faru?, khursiyya ta fad'a. Cike da murna ta ce, " Ammi tace nima ankusa kawomin momyna. Ayya my dear natayaki murna. Ran bobo yak'ara 6aci, fuska ad'aure ya gallama Nawal harara, Appa da Ammi suna kallonsa, amma basuce komaiba. Itama Nawal saitayi shiru kafin ya bibbigeta, Dan dukda yana wasa da ita hakan bai hana yaci k'aniyartaba idan ta k'uleshi. Harsuka kammala cin abinci babu Wanda yakuma cewa komai, bayan sun kammala kowa yakama gabansa. Bobo yaji dad'i Affa baimasa maganaba har dare. Da daddare yana zaune a babban falo daga can gefe, wasu buks yake dubawa, khairiyya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83